Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakai 6 da gwamnatin Tinubu za ta ɗauka don rage raɗaɗi na kwana 90
Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta amince da wani shirin tattalin arziki na gaggawa na tsawon kwana 90, wanda ake sa ran zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa da kuma sauƙaƙa wa ƴan ƙasa wahalhalun tattalin arziki.
An amince da shirin ne a yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta a ranar 22 ga Oktoban 2026.
Shirin, wanda Ministan Kudi Taiwo Oyedele ya gabatar, ya mayar da hankali ne kan rage farashin kayayyaki, musamman abinci, ƙarfafa zuba jari da kuma gaggauta aiwatar da ayyukan raya ƙasa da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al'umma.
Ba dai wannan ba ne karo na farko da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da hanyoyin da ta ce tana ganin za su taimaka wajen rage raɗaɗin da ƴan ƙasar suke ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki.
Waɗanne fannoni ne shirin zai fi mayar da hankali a kai?
Gwamnatin ta ce shirin na kwana 90 zai fi mayar da hankali da muhimmanci ga fannoni guda biyar:
- Samar da abinci mai araha
- Daidaita tsarin haraji
- Kammala muhimman ayyukan raya ƙasa da ke da amfani kai tsaye ga jama'a
- Magance matsalolin da ke hana masu zuba jari shigowa Najeriya
- Bayar da tallafi ga gidaje da iyalai ta hanyoyin da gwamnati za ta sa ido a kansu
- Kafa tsarin sa ido kan ayyukan gwamnati
Majalisar ta kuma amince da kafa wani tsarin sa ido na ƙasa da zai rika bibiyar ayyukan ci gaba a faɗin ƙasar.
Ana sa ran tsarin zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da nuna yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin mai.
Manufar shirin
A cewar Oyedele, gwamnati na fatan rage hauhawar farashin kaya da kuma ribar kuɗaɗen ruwa zuwa matakin da bai wuce kaso ɗaya ba nan da shekarar 2027.
Ya ce shirin zai amfani gidaje da kasuwanci, tare da kawar da wasu ƙalubalen da masu zuba jari ke fuskanta.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya buƙaci gwamnoni da hukumomin gwamnati su tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnati ke aiwatarwa sun haifar da:
- Sufuri mai araha
- Ingantaccen kiwon lafiya
- Ƙarin damar aikin yi
- Ƙarin kwanciyar hankalin kuɗi ga ƴan Najeriya
Ya ce nasarar shirin za ta dogara ne da irin tasirin da zai yi ga rayuwar yau da kullum ta al'umma.
"Amfanin farko na ci gaba shi ne bai wa mutane damar tsara rayuwarsu cikin tabbaci. Aikinmu shi ne mu tabbatar da cewa wannan tabbaci bai dogara da sa'a kawai ba," in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa tattaunawar da NEC ta yi kan sufuri, kiwon lafiya, gyaran aikin 'yan sanda da kuma bunƙasa kiwo na daga cikin matakan da za su inganta rayuwar 'yan Najeriya.
"Kudin zuwa neman abin rayuwa bai kamata ya cinye abin rayuwar kansa ba. Dole ne kwarewar fasinjoji ta kasance ginshiƙin burinmu, domin darajar sufurin jama'a tana cikin irin damar tafiye-tafiyen da yake samarwa," in ji shi.
Matakan za su yiwu?
Masanin tattalin arziki ya ce an fara fahimtar halin da jama'a ke ciki, amma gyaran tattalin arziki na buƙatar lokaci
Masanin tattalin arziki, Shuaibu Mikati, ya bayyana cewa matakin da gwamnati ke shirin ɗauka na tallafa wa jama'a alama ce da ke nuna an fara fahimtar irin wahalar da ƴan Najeriya ke ciki.
Sai dai ya ce matsalolin tattalin arziki da suka shafi rayuwar al'umma ba za su warware cikin kankanin lokaci ba.
Mikati ya ce, "abu ne da za ka iya cewa Alhamdulillah, tura ta fara kai bango. An fara fahimtar cewa jama'a na cikin wani hali, kuma har gwamnati na tunanin yadda za ta taimaka musu."
Ya ce duk da haka, jama'a sun shafe kusan shekara uku suna fama da tsadar rayuwa ba tare da an samu sauƙin da ake buƙata ba.
"Mun yi kusan wata 36 muna cikin wannan wahala. An yi koke-koke da yawa, amma ba a samu wani gagarumin sauyi ba."
"Da tuni ya kamata a dauki wasu matakai"
Mikati ya ce idan aka ga wata manufa tana tafiya ba tare da ta samar da sauyi mai ma'ana ba, ya dace gwamnati ta sake duba salon da take bi.
"Yanayin rayuwar ɗan Adam haka yake. Idan ka ɗauki wani salo, ka ga ana tafiya amma babu wani canji, tun tuni ya kamata a ɗauki wani sabon salo."
Ya ƙara da cewa gyaran tattalin arziki wani tsari ne da ke ɗaukar lokaci kafin a ga sakamakonsa.
"Harkar gyaran rayuwar jama'a, musamman ta tattalin arziki, ba abu ba ne da za ka shuƙa yau ka girba gobe. Abu ne mai buƙatar lokaci."
"Sauyi cikin kwana 90 abu ne mai wahala"
Da yake tsokaci kan hasashen cewa wasu matakan gwamnati za su kawo sauyi cikin kwana 90, Mikati ya nuna shakku kan yiwuwar hakan.
"A ntwa fahimta, a ce za a ɗauki matakai a samu sauyi cikin kwana 90, abu ne mai wahala."
A cewarsa, idan aka dubi ɓangarorin da gwamnati ta ce za ta mayar da hankali a kansu, akwai tambayoyi da dama game da yadda za a aiwatar da su.
"Idan ka dubi batun rage farashin abinci, daidaita hanyoyin karɓar haraji da kuma kammala manyan ayyukan raya ƙasa, za ka tambayi kanka: wanne daga cikin waɗannan gwamnati na da cikakken ikon aiwatarwa cikin gaggawa?"
Mikati ya ce ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke gaban gwamnati shi ne ƙarancin kuɗin da za a zuba a ayyukan raya ƙasa.
"Gwamnati ba ta da abincin da za ta rarraba wa mutane kai tsaye. Maganar manyan ayyuka kuma, ta yaya gwamnatin da mafi yawan kuɗinta ke tafiya wajen biyan bashin ruwa za ta samu kudin aiwatar da waɗannan ayyuka?"
Ya ce hakan na nuna cewa dole ne a samu tsari mai dorewa maimakon jiran sakamako cikin kankanin lokaci.
Mikati ya kuma yaba da ƙoƙarin da gwamnatin baya ta yi wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi.
"Idan ba mu manta ba, gwamnatin Buhari ce ta fara kawo tsarin ƙididdiga da gano masu ƙaramin ƙarfi domin a ba su tallafi. An yi hakan kuma an samu wani sauƙi," in ji shi.
A cewarsa, da an ci gaba da faɗaɗa irin wannan tallafi, da zai taimaka wajen rage raɗaɗin halin da jama'a ke ciki.
Wasu matakan na baya
Fiye da shekara uku bayan cire tallafin mai a Najeriya, tsadar fetur na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar gidaje, masu sana'o'i da masu harkokin sufuri.
Duk lokacin da farashin fetur ya tashi, farashin abinci, sufuri da sauran kayayyaki ma kan yi tashin gwauron zabi.
Kafin waɗannan sababbin matakan guda shida, gwamnatin Najeriya ta fito da wasu matakai a watan jiya da ta ce za su taimaka wajen rage wa jama'a raɗaɗin tsadar mai ba tare da dawo da tallafin fetur da aka soke a watan Mayun 2023 ba.
A cewar Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, a wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, gwamnati na son kare masu ƙaramin karfi daga matsin tattalin arziki, amma ba tare da komawa tsarin tallafin da ta ce ya jawo asarar biliyoyin naira ga kasar ba.
Matakan su ne:
- Rage farashin fetur na wata ɗaya
- Kafa manyan ma'adinan fetur
- Haɓaka aika saƙonni ta Post Office
- Faɗaɗa amfani da CNG