Yaya girman rikicin cikin-gida a APC, kuma ta yaya zai shafi jam'iyyar?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, kowace jam'iyya shirye-shirye take yi kawai domin lalubo hanyoyin da za ta samu nasara da nuna ƙwanji a zaɓen.

Sai dai a daidai lokacin da ake tunanin babbar jam'iyya mai mulki a ƙasar wato APC ta shirya tsaf domin fuskantar babban zaɓen, musamman ganin ita ce ke da mulki, kuma tana masu riƙe da madafun iko, sai alamu ke nuna akwai sauran rina a kaba a jam'iyyar.

Ana dai ganin akwai wasu alamun ɓaraka a babbar jam'iyyar ta APC a cikin-gida, kamar yadda lamarin yake a sauran jam'iyyu a ƙasar, musamman waɗanda suke da ƙarfi a siyasar ƙasar.

Sai dai ba sabon abu ba ne samun ɓaraka da rikice-rikice a jam'iyyun siyasa, musamman jam'iyya mai mulki, wataƙila saboda ƙarfin mulki da kuma yadda ake samun yawaitar masu shiga jam'iyyar.

BBC ta yi nazari irin ƙalubalenda jam'iyyar APC mai mulki ke fuskanta da kuma yadda rikicin gida ke yi wa jam'iyyar dabaibayi.

Na fi fargabar rikicin cikin-gida - Kashim

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju a Abuja, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa abin da ya fi ba shi tsoro ba PDP ba ce ko Peter Obi, illa rikicin cikin gida da ke addabar APC.

"A gaskiya, ba na tsoron PDP. Ba na tsoron Peter Obi. Amma abin da ya fi ba ni tsoro shi ne saɓanin da ke cikin gidanmu. Idan muka haɗa kai a matsayin ƴan gida ɗaya, za mu yi nasara."

Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin rashin jituwar wasu jiga-jigan APC a sassa daban-daban na ƙasar.

Shettima ya kuma yi gargaɗi ga 'yan siyasa musamman a Arewa da su guji siyasar da za ta iya raunana gwamnoni ko wasu shugabannin jam'iyyar domin cimma wata manufa ta daban.

"Babu amfanin a yi fafutukar ganin an ci zaɓen shugaban ƙasa sannan kuma a lokaci guda ana ƙoƙarin raunana gwamna a zaɓen jiha. Wannan ba zai amfani tsarinmu ba," in ji shi.

A cewarsa, APC za ta fi anfani idan dukkan ɓangarorinta sun haɗa kai, tun daga gwamnoni, 'yan majalisu har zuwa shugaban ƙasa.

Masana na ganin wannan magana wata ishara ce cewa akwai wasu ƙarairayi ko rashin jituwa da ke faruwa a cikin jam'iyyar, waɗanda ka iya yin tasiri ga shirinta na kare mulki a 2027.

Kashim ya yi gaskiya - Ndume

Shi ma Sanata Ali Ndume ma ya bayyana irin wannan damuwa, inda ya ce APC na fuskantar ƙalubale daga cikin gida fiye da waɗanda ke zuwa daga jam'iyyun adawa.

A cewarsa, matsalar siyasar Najeriya ita ce mutane sun fi mayar da hankali kan mutane da son zuciya maimakon manufofi da shirye-shiryen da za su amfani al'umma.

Ndume ya ce ya yi daidai da abin da Shettima ya faɗa, yana mai cewa APC tana buƙatar gyara matsalolinta kafin ta mayar da hankali kan adawa.

Ya kuma zargi wasu 'yan jam'iyyar da nuna biyayya a fili amma suna aikata akasin haka a ɓoye.

Da wannan magana, Ndume na nufin cewa akwai mutanen da ke nuna goyon baya ga APC da shugabanninta a idon jama'a, amma a bayan fage ba sa aiki domin cigaban jam'iyyar.

Har ila yau, ya soki yadda ake tallata ayyukan gwamnatin APC, yana mai cewa wasu da aka ba wannan nauyi sun fi mayar da hankali kan muradunsu na siyasa maimakon kare martabar jam'iyyar.

Ndume ya kuma yi gargaɗin cewa siyasar Najeriya na ƙara zama siyasar mutane maimakon siyasar manufofi.

A ra'ayinsa, muddin jam'iyyu ba su mayar da hankali wajen gabatar da mafita ga matsalolin jama'a ba, za su ci gaba da fuskantar matsalolin cikin gida da rashin goyon bayan jama'a.

Barazana ga APC

Masanin siyasa kuma malami a sashen nazarin siyasa na Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya ce duk wata jam'iyya da ta kasa shawo kan rikicin cikin gida na fuskantar barazanar rasa ƙarfi ko ma shan kaye a zaɓe.

A cewarsa, tarihin siyasar Najeriya ya nuna cewa rikice-rikicen cikin gida sun kasance daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa raunana manyan jam'iyyun siyasa.

"Akwai gaskiya a maganar cewa rikicin cikin gida na iya yi wa jam'iyya illa. Duk jam'iyyar da ke fama da irin wannan matsala, ba ya haifar mata da ɗa mai ido," in ji Farfesa Fagge.

Ya bayar da misalin jam'iyyar PDP wadda ke kan mulki a shekarar 2015 amma rikice-rikicen cikin gida suka taimaka wajen raunana ta kafin ta sha kaye a hannun APC.

"PDP tana kan karagar mulki, amma rikicin cikin gida ya dabaibaye ta har ta rasa zaɓe. Wannan darasi ne da sauran jam'iyyu za su iya koya daga gare shi."

Duk da cewa APC na ci gaba da jan hankalin ƴan siyasa daga wasu jam'iyyu, Farfesa Fagge ya ce hakan kaɗai ba ya tabbatar da dawwamar ƙarfinta.

A cewarsa, ba lallai ne duk waɗanda suka shiga jam'iyyar sun yi hakan saboda sun yarda da manufofinta ko akidarta ba.

"Wasu an kwaɗaita musu wani abu ne, wasu kuma tilasta musu aka yi. Idan lokaci ya yi suka ga buƙatunsu ba za su biya ba, wasu za su iya janye goyon baya ko ma su fice daga jam'iyyar."

Ya ce irin wannan yanayi ne ya sanya wasu manyan jam'iyyu a baya suka shiga matsala bayan da suka kasa haɗa kan mambobinsu masu ra'ayoyi daban-daban.

Shin jam'iyyun za su tsinci dami a kala?

Farfesan ya ce rikicin cikin gida na da illa fiye da adawa daga waje saboda yana fitowa daga mutanen da suke cikin tsari ɗaya.

"A gaskiya, rikicin cikin gida ya fi illa. Saboda kowanne bangare yana son ya nuna shi ne ke da rinjaye da iko a cikin jam'iyyar. Wannan ne ke sa rikicin ya fi tsanani."

Ya ƙara da cewa sau da yawa irin waɗannan rikice-rikice kan janyo rabuwar kai, kafa sabbin ƙungiyoyi ko ma ficewar manyan jiga-jigai.

Game da ko jam'iyyun adawa za su amfana daga matsalolin APC, Farfesa Fagge ya ce hakan ba zai faru kai tsaye ba sai idan su ma sun gyara nasu matsalolin.

"Suma za su iya cin gajiyar hakan ne kawai idan sun dinke matsalolinsu. Idan suna fama da rikice-rikice irin na cikin gida, ba za su ci riba ba."

Ya ce wajibi ne ga jam'iyyun hamayya su gabatar da 'yan takarar da jama'a za su amince da su tare da gudanar da yakin neman zaɓe a matakin ƙasa.

"Dole su shiga lungu da saƙo, su yi aiki tuƙuru. Ba wai su zauna suna jiran APC ta samu matsala ba ne kawai."