Fitattun masu neman takarar gwamna da suka janye a APC

Jihohi da dama sun zaɓi bin tsarin maslaha wajen fitar da ƴan takara gabanin babban zaben Najeriya na 2027

Asalin hoton, FB/Multiple

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan jam'iyyar APC da dama ne suka janye daga takarar kujerar gwamna a lokacin zaɓen cikin gida na jam'iyyar da aka gudanar a jihohi da dama.

A ranar Alhamis ne jam'iyyar APC ta tsara gudanar da zaman tantancewa da sulhu domin fitar da ƴan takara a jihohi 28, inda kuma za yi zaɓen fitar da gwanin ta hanyar abin da ake kira "ƙato bayan ƙato".

Gwamnoni da suka samu takarar ta hanyar sulhu sun haɗa da gwamnoni masu ci na jihohin Delta, Kano, Enugu, Jigawa, Katsina, Kebbi da Sokoto da Zamfara da Neja da Akwa Ibom da Ebonyi.

To sai dai wasu fitattun ƴan takarar gwamna a jihohi da dama sun janye daga takarar tun kafin zaɓen bisa dalilan zargin 'rashin adalci'.

Siminalayi Fubara

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sanar da janye takararsa ta neman gwamnan jihar a jam'iyyar ta APC.

A wata sanarwa da ya rattaba wa hannu ranar Laraba, Fubara ya ce ya yanke shawarar janye jikinsa daga takarar ne bayan dogon tunani da kuma tuntuɓar iyali da abokai da mutanensa na siyasa.

"...Na ɗauki matsayin mai wahala ne... da zuciya ɗaya tare da yanke cewa zan goyi bayan duk wanda ya samu takarar gwamna a jam'iyyarmu," in ji Fubara.

Ya kuma ƙara da cewa bai kamata siyasa ta zama a mutu ko a yi rai ba.

"Jihar Ribas tana gaba da kowa, kuma a daidai wannan lokaci, zaman lafiya da haɗin kan jihar ne ya kamata a bai wa muhimmanci fiye da buƙatar kai."

Farfesa Ali Pantami

Shi ma tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Ali Isa Pantami wanda ke takarar gwamna a jihar Gombe ya sanar da janyewa daga takarar bisa zargin 'maguɗi' da 'son rai' da ya ce sun saɓa da dokokin zaɓen Najeriya na 2026.

A wata sanarwa da barista Ibrahim M. Tahir ya fitar a madadin ƙungiyar goyon baya ta Pantami da aka fi sani da Pantamiyya Movement, Farfesan ya ce ya yanke shawarar ne bayan tuntuɓa da kuma duba na tsanaki na yadda tsarin zaɓen fitar da gwanin yake a jihar tasu.

"A mulkin dimokraɗiyya, doka ita ce ya kamata ta jagoranci yadda za a gudanar da komai. Ƙin bin dokar zaɓe ta 2026 tare da dokokin jam'iyya sun mayar da zaɓen fitar da gwanin ba halastacce ba," in ji sanarwar.

Da ma dai Farfesa Pantami ya shaida wa BBC cewa bai aminta da sulhun da aka yi a baya ba, wanda ya fitar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Gombe kuma ya sha alwashin "yaƙar zalunci bisa doka".

Sa'idu Alƙali

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Saidu Alƙali shi ma ya sanar da janye takarar neman gwamnan jihar Gombe bisa zargin "saɓa dokokin zaɓe".

Janyewa daga takarar tasa ta biyo bayan janyewar Farfesa Pantami a ranar Talata.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Alƙali ya ce zai ƙaurace wa zaɓen da aka shirya yi ranar Alhamis sakamakon yanke ƙaunar da ya yi na samun adalci.

Sai dai kuma Alƙali ya ce duk da ya janye daga takarar amma har yanzu shi ɗan jam'iyyar APC ne.

Ya kuma roƙi shugabancin jam'iyyar APC da su soke zaɓen su kuma kafa kwamiti na gaskiya domin gudanar da sahihin zaɓe.

Na daina siyasa - Sadiq

Shi kuwa tsohon hafsan sojin saman Najeriya, Air Vice Marsall Sadiq Baba Abubakar ya ce ya ma daina siyasa gaba ɗaya bayan janyewa daga neman takarar gwamnan jihar Bauchi.

A wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Sadiq ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga harkokin siyasa ne sakamakon matsalolin cikin gida da ke addabar jam'iyyun siyasa a Najeriya.

"Cikin rashin jin daɗi, na yanke hukuncin daina siyasa saboda wasu dalilai na ƙashin kaina," kamar yadda ya faɗa a cikin harshen Hausa.

A shekarar 2021 ne Abubakar ya bar aiki ya kuma tsunduma siyasa.

Tsohon hafsan sojin ya yi takarar neman gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC a 2023.

Yanzu haka tsohon sojan ya ce zai mayar da hankalinsa ne ga ayyukan jin-ƙai ta hanyar gadauniyarsa mai suna 'Marshall Care Foundation'.