Dokar Kare sirrin bayanai ta BBC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 11

An sabunta wannan shafi na ƙarshe a ranar 1 Agusta 2026.

Amincewarku tana da muhimmanci a gare mu, kuma mun himmatu wajen kare sirri da tsaron bayananku. Wannan bayani kan tsare sirri ya nuna yadda Hukumar Yaɗa Labarai ta Birtaniya wato BBC ke tattarawa da amfani da bayanan sirri (wanda kuma ake kira bayanan mutum) lokacin da kuke amfani da shafukan sashen BBC mai watsa shirye-shirye a duniya, wato BBC World Service da sauran ayyukan sassan ayyukan BBC ga al'umma, wato BBC Public Service.

Shafukan harsunan da ke ƙarƙashin sashen BBC mai wasa shirye-shirye a duniya wani ɓangare ne na BBC Public Service da ke hidimtawa jama'a. Suna aiki ne a ƙarƙashin manufar hidimar jama'a ta BBC, kuma suna da cikakken ƴanci a fannin labaran da suke yaɗawa.

Wannan sanarwar tana bayani kan:

  • Irin bayanan da muke tattarawa;
  • yadda muke amfani da su;
  • lokutan da za mu iya bayar da su ga wasu;
  • yadda muke kare su; da kuma
  • haƙƙoƙinku da ƴancinku na zaɓen abubuwan da kuke so.

Ana iya samun wasu ƙarin bayanai na musamman da suka shafi wasu ayyuka ko hidimomi, ciki har da tsarin BBC na sirrantawa da kuma ajiye bayanan shafukan da kuka shiga a intanet (BBC Privacy and Cookies Policy).

1. ABIN DA WANNAN BAYANI YA ƘUNSA

Wannan bayani ya shafi shafukan Intanet na harsunan da sashen BBC mai watsa shirye-shirye a duniya wato BBC World Service ke yi da sauran ayyuka masu alaƙa na BBC Public Service waɗanda BBC ke gudanarwa.

Wannan ya haɗa da:

  • Shafukan intanet na harsunan sashen BBC mai watsa shirye-shirye a duniya, BBC World Service;
  • Ayyukan labarai na BBC a cikin harsuna daban-daban;
  • Manhajojin BBC World Service

Ayyukan da ba su ƙarƙashin wannan bayani

Wannan bayani bai shafi:

• gudummawar edita ga aikin jarida na BBC, waɗanda ke ƙarƙashin Sanarwar Sirri ta Masu Gudummawa (Contributor Privacy Notice), sai dai idan an bayyana akasin haka;

• ayyukan kasuwanci na BBC Studios, ciki har da shafin yanar gizo da manhajar BBC.com na harshen Turanci;

• dandamali da ayyukan kafafen sada zumunta na wasu kamfanoni;

• shafukan yanar gizo na waje da ake haɗawa daga ayyukan BBC;

• dandamalin yaɗawa ko wallafawa na wasu kamfanoni.

Waɗannan ayyukan suna da nasu sanarwar sirri daban.

2. SU WANE NE MU?

BBC ce mai kula da bayanai ga shafukan harsuna na sashen BBC mai watsa shirye-shirye a duniya wato BBC World Service.

Wannan na nufin cewa mu ne ke ƙayyade dalilai da hanyoyin sarrafa bayananku na sirri, kuma dole ne mu tabbatar da cewa muna bin dokokin kariyar bayanai da suka dace.

3. BAYANAN DA MUKE TATTARAWA

Bayanan da muke tattarawa suna dogara ne da yadda kuke amfani da ayyukanmu.

Bayanan da kuke ba mu kai tsaye

Wannan na iya haɗawa da:

  • sunanku;
  • adireshin imel ɗinku;
  • lambar wayarku ko ta salula;
  • adireshin gidanku;
  • bayanan da suka shafi shekarunku;
  • jinsinku;
  • sharhi ko saƙonnin da kuke aiko mana;
  • hotuna, bidiyo ko sautin murya da kuka aiko mana;
  • amsoshin binciken ra'ayi;
  • zaɓuɓɓukan wasiƙun labarai da kuka zaɓa.

Bayanan da ake tattarawa kai tsaye

Lokacin da kuke amfani da shafukanmu na intanet ko manhajojinmu, za mu iya tattara waɗannan bayanai kai tsaye da zarar kun shiga shiga cikinsu:

  • adireshin IP;
  • nau'in burauza;
  • bayanan tantance na'ura, kamar manhaja, kamfani mai ƙera na'ura da/ko lambar talla;
  • bayanan tantance tsarin aiki;
  • shafukan da aka kalla;
  • bayanan yadda ake amfani da sabis ɗin;
  • bayanan kukis da sauran fasahohin bin diddigi;
  • tsarin saita harshe da na yanki.

Bayanan da ke fitowa daga akawunt na BBC

Wasu ayyuka ko hidimomi na iya ba ku damar shiga ta amfani da akawunt na BBC.

A irin waɗannan lokuta, za mu iya amfani da bayanan akawunt domin:

  • gane ku a faɗin ayyuka da hidimomin BBC daban-daban;
  • tuna abubuwan da kuka fi so da zaɓuɓɓukanku;
  • inganta ƙwarewar amfani da hidimominmu;
  • samar muku da abubuwan da aka keɓance muku, idan kun ba da izini.

Ana kuma iya amfani da yawancin shafukan sashen BBC mai watsa shirye-shiryensa a duniya wato BBC World Service ba tare da shiga cikin akawun ba.

Bayanan da ake samu daga wasu ɓangarori

A wasu ƙalilan daga cikin yanayi, muna iya samun bayanai daga:

  • dandamalin kafafen sada zumunta inda kuke hulɗa da abubuwan da muke wallafawa;
  • masu samar da alƙaluma da bayanan da za a nazarta;
  • abokan hulɗar talla;
  • masu samar da binciken ra'ayoyin masu sauraro.

A wasu lokuta kaɗan, muna iya karɓar bayanai daga waɗannan ɓangarori domin taimaka mana fahimtar yadda ake amfani da ayyukanmu da kuma inganta abubuwan da muke samarwa.

Bayanai daga yara

Idan shekarunka ba su kai shekarun balaga da doka ta tanada ba a ƙarƙashin dokar da ta shafe ka, za mu iya buƙatar izinin iyayenka ko mai kula da kai kafin ka shiga shafukan BBC na harsuna daban-daban da/ko manhajojinmu, da kuma kafin ka aiko mana da bayananka na sirri. Wannan na iya nufin cewa ba za a ba ka damar shiga shafukan na BBC ko bayar da bayananka na sirri ba sai an samu wannan izinin. Don ƙarin bayani, da fatan za a duba Sashe na 10, "Yara masu amfani da ayyukanmu."

Lokacin da ba ku bayar da bayanai ba

A wasu lokuta, muna buƙatar bayanan sirri domin samar muku da wata hidima, amsa buƙatarku, gudanar da akawun, ko kuma ba ku damar amfani da wasu sassa na musamman.

Idan kuka zaɓi ka da ku bayar da bayanan da ake buƙata don waɗannan manufofi, ƙila ba za mu iya samar muku da hidimar ko fasalin da ya dace ba, ko kuma amsa buƙatarku yadda ya kamata.

4. YADDA MUKE AMFANI DA BAYANANKU

Muna amfani da bayanan sirri don waɗannan manufofi.

A. Don samar da ayyukan BBC

Wannan ya haɗa da:

  • gudanar da shafukan intanet da manhajoji;
  • samar da abubuwan da kuka nema;
  • sarrafa akawun masu amfani;
  • amsa buƙatu, ƙorafe-ƙorafe da tambayoyi;
  • aika saƙonnin da suka shafi ayyukanmu.

Tushen doka

  • Halattattun muradu;
  • aiwatar da kwantaragi bisa dacewa;
  • aikin jama'a ko muradun jama'a.

B. Don tallafa wa aikin jarida da ayyukan edita

BBC na sarrafa bayanai domin manufofin aikin jarida, ayyukan edita da kuma hidimar muradun jama'a.

Wannan na iya haɗawa da:

  • karɓa da sarrafa bayanan da masu sauraro suka aiko;
  • sa ido da tace tsokaci;
  • tabbatar da sahihancin gudummawar da aka bayar;
  • sadarwa da masu ba da gudummawa;
  • kare mutunci da 'yancin aikin edita.

Inda ya dace, muna iya sarrafa bayanan sirri masu matuƙar muhimmanci idan hakan ya zama dole domin aikin jarida da rahotannin da suka shafi muradun jama'a.

Tushen doka

  • Aikin jama'a ko muradun jama'a;
  • kariyar aikin jarida da 'yancin faɗar albarkacin baki kamar yadda dokokin da suka dace suka tanada.

D. Don fahimtar yadda masu sauraro ke amfani da ayyukanmu

Muna amfani da kayan aikin nazari da bincike domin fahimtar:

  • yadda masu sauraro ke mu'amala da abubuwan da muke wallafawa;
  • waɗanne ayyuka ne ake amfani da su;
  • yadda za a inganta ayyukanmu;
  • yadda za mu ƙirƙiro sababbin hanyoyi da sabbin ayyuka.

A duk lokacin da hakan zai yiwu, muna amfani da bayanan da aka tattara gaba ɗaya ko kuma bayanan da aka cire duk wata alamar gano mutum daga cikinsu.

Tushen doka

  • Aikin jama'a ko muradun jama'a;
  • halattattun muradu ;
  • amincewa idan doka ta buƙaci hakan wajen amfani da kukis ko fasahohin nazari.

E. Don aika wasiƙun labarai da sanarwa

Idan kun yi rajista, muna iya aiko muku da:

  • wasiƙun labarai waɗanda za su iya ƙunsar shawarwarin abubuwan da za ku karanta ko kalla da kuma kamfen ɗin ƙarfafa hulɗa da masu sauraro;
  • sabbin bayanan edita;
  • sanarwa da ankararwa.

Kuna iya soke rajistarku a kowane lokaci.

Tushen doka

  • Amincewa;
  • halattattun muradu dangane da muhimman saƙonnin da suka shafi ayyukanmu.

F. Don tallafa wa tallace-tallace a ayyukanmu na ƙasa da ƙasa

Wasu daga cikin ayyukan sashen BBC mai watsa shirye-shiryensa a duniya, BBC World Service na iya ƙunsar tallace-tallace a wajen Birtaniya. Tallace-tallace na taimakawa wajen ɗaukar nauyin gudanar da ayyukan BBC na ƙasa da ƙasa.

Tallace-tallacen na iya haɗawa da:

  • tallace-tallacen da suka danganci abubuwan da ke cikin shafin da kuke kallo;
  • iyakantattun tallace-tallacen da aka keɓance wa masu amfani inda doka ta ba da izini.

Tallace-tallacen da ke kan shafin intanet na BBC World Service kamfanin kasuwanci na BBC, wato BBC Studios, ne ke gudanar da su. A kan waɗannan manufofi, BBC Studios ita ce mai kula da bayanai masu zaman kansu.

Don ƙarin bayani kan yadda BBC Studios ke sarrafa bayanan sirri don manufofin da suka shafi tallace-tallace, da fatan za a duba Sashe na G na Manufofin Sirri na BBC Studios (BBC Studios Privacy Policy).

Ƙarin bayani game da tushen doka na sarrafa bayanai

Dangane da inda kuke zaune da kuma irin hidimar da kuke amfani da ita, muna iya sarrafa bayanan sirri bisa ga tushe ɗaya ko fiye na doka da dokokin da suka dace suka amince da su.

Waɗannan na iya haɗawa da:

  • amincewarku ;
  • bin doka ko ƙa'idojin da suka shafe mu;
  • aiwatar da kwangila;
  • kare muhimman muradun rayuwa ko lafiya;
  • gabatarwa, aiwatarwa ko kare haƙƙoƙin shari'a;
  • ayyukan da ake gudanarwa domin muradun jama'a da
  • halattattun muradunmu, matuƙar waɗannan muradun ba su rinjayi haƙƙoƙinku da 'yancinku ba.

Za mu yi amfani da tushen doka da ya fi dacewa da yanayin sarrafa bayanan da abin ya shafa, kamar yadda dokokin kariyar bayanai suka tanada.

5. KUKIS (COOKIES) DA SAURAN FASAHOHIN DA SUKA YI KAMA DA SU

Muna amfani da kukis (cookies) da sauran fasahohin bin diddigi masu kama da su (kamar pixels da web beacons) domin:

  • gudanar da ayyukanmu da hidimominmu;
  • tuna abubuwan da kuka fi so da zaɓuɓɓukanku;
  • auna yadda ake amfani da ayyukanmu;
  • inganta aiki da ingancin hidimominmu;
  • tallafa wa talla, inda hakan ya dace.

Kuna iya sarrafa zaɓuɓɓukan kukis ɗinku ta hanyar kayan aikin saitunan kukis da ake samarwa a cikin ayyukanmu.

Don ƙarin bayani, da fatan za a duba Manufar Sirri da Kukis ta BBC

6. LOKUTAN DA MUKE RABA BAYANAI

Muna iya raba bayanai:

  • a tsakanin sassan BBC idan hakan ya zama dole;
  • tare da masu samar da fasaha, ayyukan karɓar bayanai da sabis na ajiyar bayanai a gajimare waɗanda ke taimakawa wajen gudanar da ayyukanmu;
  • tare da masu samar da sabis na tallafin abokan hulɗa, sadarwa da isar da abubuwan da muke wallafawa;
  • tare da masu samar da ayyukan nazari, auna masu sauraro da binciken masu sauraro;
  • tare da abokan hulɗar talla idan ana nuna talla a cikin ayyukan da abin ya shafa;
  • tare da dandamalin kafafen sada zumunta da na rarraba abubuwan wallafawa idan masu amfani sun zaɓi yin hulɗa da abubuwan BBC ta waɗannan ayyuka;
  • tare da hukumomin sa ido, jami'an tsaro masu aiwatar da doka, kotuna ko wasu hukumomin gwamnati idan doka ta buƙata ko ta ba da izini;
  • domin kare haƙƙoƙi, lafiya da tsaron masu amfani, masu ba da gudummawa ko BBC; da kuma
  • tare da masu ba da shawara na ƙwararru, masu binciken kuɗi da wakilan doka idan hakan ya zama dole domin kare ko aiwatar da haƙƙoƙin doka na BBC.

Muna buƙatar duk wasu ɓangarori na uku da ke sarrafa bayanan sirri a madadinmu su kare waɗannan bayanai, kuma su yi amfani da su ne kawai don manufofin da aka ba su izini da kuma bisa ga umarnin da muka bayar.

7. SAUYA WURIN SARRAFA BAYANAI TSAKANIN ƘASASHE

Sashen BBC mai watsa shirye-shiryensa a duniya na gudanar da ayyukansa a ƙasashe daban-daban na duniya.

Ana iya sarrafa bayananku a wajen ƙasar da kuke zaune, ciki har da ƙasashen da dokokinsu na iya bayar da matakan kariyar bayanai da suka bambanta da na ƙasarku.

Inda doka ta buƙata, muna amfani da matakan kariya da aka tsara domin kare bayanan sirri, ciki har da:

  • kariyar da aka tanada ta hanyar yarjejeniyoyi;
  • hanyoyin sauya bayanai da hukumomi suka amince da su;
  • matakan fasaha da na tsaro.

8. TSAWON LOKACIN DA MUKE RIƘE BAYANAI

Muna riƙe bayanan sirri ne kawai na tsawon lokacin da ake buƙata domin:

  • cimma manufofin da aka bayyana a cikin wannan shafi;
  • cika wajibai na doka ko ƙa'idoji;
  • tabbatar da tsaro da gudanar da binciken tantancewa;
  • manufofin edita da adana bayanai a ma'ajiya.

Tsawon lokacin da ake riƙe bayanai yana bambanta gwargwadon nau'in bayanan sirrin da abin ya shafa da kuma irin hidimar da aka yi amfani da ita.

9. YADDA MUKE KARE BAYANAI

Muna kare bayananku ta hanyoyi da dama. Waɗannan sun haɗa da horas da ma'aikata, saka hannun jari a fasahohi, da kuma bin ƙa'idoji masu tsauri wajen sarrafawa da adana bayanai.

Muna amfani da matakan kariya na tsari da na fasaha da suka dace domin taimakawa wajen kare bayanan da muke riƙe da su game da ku daga ɓacewa, amfani da su ba daidai ba, ko samun damar shiga, bayyana su, canja su ko lalata su ba tare da izini ba. Haka kuma, muna ƙoƙarin tabbatar da cewa masu samar mana da ayyuka daga ɓangarori na uku suna ɗaukar irin waɗannan matakan kariya.

Duk da cewa mun ɗauki matakai domin taimakawa wajen kare bayanan da ke ƙarƙashin kulawarmu, ya kamata ku sani cewa babu wani matakin tsaro da zai iya ba da cikakkiyar kariya ɗari bisa ɗari.

Idan kun yi imanin cewa an samu matsala ga bayananku na sirri da ke ƙarƙashin kulawarmu, ciki har da samun damar shiga wani asusu da kuke da shi a cikin ayyukanmu ba tare da izini ba, da fatan za a tuntuɓe mu nan da nan ta wannan adireshin imel:

10. YARA MASU AMFANI DA AYYUKANMU

Wasu daga cikin ayyukan BBC na iya kasancewa an tsara su ne domin yara da iyalai su yi amfani da su.

Inda ya dace, muna ɗaukar ƙarin matakai domin:

  • rage yawan bayanan da ake tattarawa;
  • samar da kariya da ta dace da shekaru;
  • samun izinin iyaye ko masu kula da yara idan doka ta buƙata.

Lokacin da ake sa ran yara za su yi amfani da wasu ayyuka, muna ƙoƙarin yin la'akari da abin da ya fi zama alheri a gare su yayin tsara da gudanar da waɗannan ayyukan. Wannan na iya haɗawa da samar da bayanai ta hanyar da ta dace da rukunin shekaru daban-daban, rage tattarawa da amfani da bayanan sirri inda ya dace, da kuma amfani da ƙarin matakan kariya da aka tsara musamman domin kare yara da matasa.

Idan kun yi imanin cewa wani yaro ya bayar da bayanansa na sirri ta hanyar da ba ta dace ba, da fatan za a tuntube mu ta wannan adireshin imel:

11. HAƘƘOƘINKU DA ZAƁUKANKU

Dangane da inda kuke zaune da kuma dokokin da suka shafe ku, kuna iya kasancewa da wasu haƙƙoƙi dangane da bayananku na sirri. Waɗannan haƙƙoƙin na iya haɗawa da damar:

  • samun damar duba bayanan sirrin da muke riƙe game da ku;
  • neman tabbaci cewa muna sarrafa bayananku na sirri;
  • gyara bayanan da ba daidai ba ko kuma waɗanda ba su cika ba;
  • neman a goge bayanan sirri, a cire duk wata alamar gano mutum daga cikinsu, ko kuma a takaita yadda ake sarrafa su a wasu yanayi;
  • ƙin amincewa da wasu nau'o'in sarrafa bayanai;
  • janye amincewarku idan sarrafa bayanan ya dogara ne da amincewa;
  • neman kwafin bayananku na sirri a tsarin da za a iya ɗauka ko canjawa, inda hakan ya dace;
  • samun bayani game da ƙungiyoyi ko hukumomin da za mu iya raba bayananku na sirri da su;
  • neman a sake duba wasu shawarwari ko matakai da aka yanke ta amfani da sarrafa bayanai ta atomatik, inda hakan ya dace; da kuma
  • kai ƙorafi ga hukumar da ke kula da kariyar bayanai da ta dace.

Ana iya samun ƙarin haƙƙoƙi a wasu ƙasashe da yankuna. Inda dokar da ta dace ta buƙata, za mu samar da ƙarin bayani game da waɗannan haƙƙoƙi da yadda za a yi amfani da su.

Haka kuma, kuna iya samun wasu haƙƙoƙi da suka shafi:

  • kukis;
  • tallace-tallacen da aka keɓance bisa ga masu amfani; da
  • saƙonnin talla ko na kasuwanci.

Yanke Shawara Ta Hanyar Sarrafa Bayanai Ta Atomatik

A al'ada, ba ma yanke shawarwari da ke da tasirin doka ko wani muhimmin tasiri makamancin haka ga mutane bisa sarrafa bayanan sirri ta atomatik kaɗai dangane da shafukan harsunan da BBC World Service ke watsa shirye-shirye a duniya.

Idan wannan ya canza kuma dokar da ta dace ta buƙaci a ba da ƙarin bayani, za mu samar da cikakkun bayanai a lokacin da ya dace.

Amfani da Haƙƙoƙinku

Domin amfani da haƙƙoƙinku dangane da bayananku na sirri, za ku iya tuntuɓar:

Haka kuma, kuna iya samun damar sarrafa wasu saituna ta hanyar Asusun BBC (BBC Account) ɗinku.

12. GUDUMMAWAR EDITA DA ABUBUWAN DA MASU AMFANI KE AIKOWA

Idan kun:

  • yi tsokaci a kan labarai ko maƙaloli;
  • tuntuɓi 'yan jarida;
  • aiko da hotuna, bidiyo ko sautin murya;
  • bayar da gudummawa ga abubuwan da BBC ke wallafawa na edita;

BBC na iya sarrafa bayananku domin manufofin aikin jarida, ayyukan edita da kuma muradun jama'a.

Da fatan za a guji raba bayanan da za su iya jefa ku ko wasu cikin haɗari.

Inda ya dace, BBC na iya:

  • tace da duba abubuwan da aka aiko;
  • cire abubuwan da ba su dace ba;
  • tabbatar da sahihancin bayanan masu aikawa ko tantance ainihin mutum;
  • adana bayanai domin dalilan edita ko na doka.

13. SAUYE-SAUYE GA WANNAN SANARWAR

Muna iya sabunta wannan sanarwar daga lokaci zuwa lokaci.

Inda ya dace, za mu sanar da masu amfani da ayyukanmu game da muhimman canje-canjen da aka yi.

Za a riƙa wallafa sabuwar sigar wannan sanarwar koyaushe dangane da hidimar da BBC ke yi da abin yake da alaƙa da hakan.

14. TUNTUƁE MU

BBC ta naɗa Jami'in Kula da Kariyar Bayanai wanda ke da alhakin kula da tambayoyi da suka shafi wannan Sanarwar Sirri.

Idan kuna da wata tambaya game da wannan Sanarwar Sirri, ciki har da buƙatar amfani da haƙƙoƙinku na doka, ko kuma kuna son gabatar da wata damuwa ko ƙorafi, da fatan za ku tuntuɓi Jami'in Kula da Kariyar Bayanai ta imel:

Jami'in Kula da Kariyar Bayanai (Data Protection Officer)

BBC Broadcasting House

Portland Place

London W1A 1AA

United Kingdom

Haka kuma kuna da haƙƙin kai ƙorafi ga hukumar kariyar bayanai ta ƙasarku ko kuma ga Ofishin Kwamishinan Yaɗa Bayanai na Birtaniya (UK Information Commissioner's Office).