Ɓangarori biyar na hannun jari da matasa za su fi samun riba

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shirin fitar da hannun jarin Matatar Dangote ga jama'a ya sake jawo hankalin ƴan Najeriya zuwa kasuwar hannun jari, musamman a daidai lokacin da matasa da dama ke neman hanyoyin gina dukiya da kuma kare kansu daga asarar kuɗi da ke tattare da wasu hanyoyin zuba jari marasa tabbas.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa matatar man fetur ɗinsa za ta fara sayar da hannayen jari ga jama'a ta hanyar Initial Public Offering (IPO), inda aka tsara bai wa kowa damar mallakar kaso a cikin kamfanin ko da da ƙaramin jari ne.

Wannan ci gaba ne da ya buɗe sabuwar tattaunawa kan muhimmancin kasuwar hannun jari da kuma damar da take samarwa ga matasa masu son gina makoma mai ɗorewa.

Da yake sharhi kan wannan dama, Dr Salihu Lukman, Mataimakin Farfesa a University of Hafr Al Batin da ke ƙasar Saudiyya, ya ce kasuwar hannun jari na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen tara dukiya cikin tsari da kuma dogon lokaci.

A cewarsa, mutane da dama na kallon kasuwar hannun jari a matsayin wani abu mai wahala, alhali kuwa hanya ce da ke ba mutum damar zama mai mallakar kaso a cikin manyan kamfanoni ba tare da ya kafa nasa kamfanin daga farko ba.

Mene ne hannun jari?

Dr. Salihu Lukman ya bayyana cewa hannun jari, wanda ake kira equity a Turance, yana nufin rabon mallaka da mutum yake da shi a cikin wani kamfani.

Ya bayar da misali cewa idan mutane biyu suka kafa kasuwanci da jarin naira dubu 100, kuma kowannensu ya bayar da naira dubu 50, to kowannensu yana da kaso 50 cikin 100 na mallakar kasuwancin.

Idan kasuwancin ya samu riba, za a raba ribar gwargwadon gudunmawar da kowa ya bayar. Haka ma idan darajar kasuwancin ta karu, darajar hannun jarinsu za ta karu.

"Da zarar ka sayi hannun jari a kamfani, ka zama ɗaya daga cikin masu kamfanin, ko da kuwa kaso ne ƙarami," in ji shi.

Hanyoyi biyu da ake samun riba

Masanin ya ce akwai manyan hanyoyi biyu da masu zuba jari ke samun kuɗi daga hannun jari.

Rabon riba (Dividend)

Wannan yana faruwa ne lokacin da kamfani ya samu riba sannan ya ware wani kaso domin rabawa masu hannun jari.

Wasu kamfanoni suna raba riba sau ɗaya a shekara, yayin da wasu ke yin hakan sau biyu ko fiye da haka.

"Kamfanoni irin su MTN kan yi rabon riba sau biyu a shekara, yayin da wasu ke yin sau ɗaya kacal," in ji shi.

Ƙaruwar darajar hannun jari (Capital Gain)

Hanya ta biyu ita ce idan darajar hannun jarin da mutum ya saya ta karu.

Ya bayar da misalin wanda ya sayi hannun jarin MTN lokacin da aka fara fitar da shi ga jama'a sannan daga baya farashinsa ya ninka sau da yawa.

"Idan ka sayi hannun jari a lokacin da farashinsa yake ƙasa sannan kamfanin ya bunƙasa, za ka iya samun riba mai yawa idan ka sayar daga baya," ya bayyana.

Matakan saya da sayar da hannun jari

A cewarsa, akwai matakai biyu da ake saye da sayar da hannun jari.

"Na farko shi ne lokacin da kamfani yake fitowa karon farko domin sayar da hannayen jarinsa ga jama'a. Wannan shi ne abin da ake kira IPO," in ji shi.

A nan ne kamfani ke tara kuɗin da zai yi amfani da su wajen faɗaɗa ayyukansa.

Na biyu kuwa shi ne kasuwar da masu hannun jari ke sayen hannun jari daga junansu bayan an gama IPO.

"Idan mutum ya sayi hannun jari a IPO, daga baya zai iya sayarwa wani a kasuwar hannun jari idan ya ga farashin ya yi masa," in ji shi.

Ɓangarori biyar da suka fi jan hankalin masu zuba jari

A cewar Dr. Salihu Lukman, akwai fannoni biyar da matasa za su iya mayar da hankali a kansu idan suna son shiga kasuwar hannun jari.

Hannayen jari masu bin ƙa'idojin Musulunci

Wannan bangare ya ƙunshi kamfanonin da aka tantance cewa harkokinsu sun dace da ƙa'idodin Shari'ar Musulunci.

Ya ce wannan bangare yana ƙara jawo hankalin masu zuba jari daga Arewacin Najeriya saboda yawaitar fahimtar cewa akwai hanyoyin saka jari ba tare da shiga mu'amalolin da suka saɓa wa addini ba.

"Mutane da yawa a baya suna ganin kasuwar hannun jari haramun ce gaba ɗaya. A yau kuwa ana samun karin fahimta game da kamfanonin da suka cika sharuddan Shari'a," in ji shi.

Ɓangaren mai da iskar gas

Ɓangaren makamashi na ɗaya daga cikin sassan da suka fi samar da riba ga masu zuba jari.

"Na sayi hannun jarin Seplat a shekarar 2024 lokacin da farashinsa yake kusan naira 3,300. A yau kuma yana ciniki sama da naira 16,000. Wannan yana nuna muhimmancin haƙuri da kuma zabar kamfani mai ƙarfi," in ji shi.

Ya ce ci gaban masana'antar mai da gas a Najeriya na kara jawo hankalin masu zuba jari zuwa wannan bangare.

Ɓangaren bankuna

Bankuna na daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin kowace ƙasa.

A Najeriya, bankuna suna cikin kamfanonin da masu zuba jari ke yawan mayar da hankali a kansu.

Masanin ya ce bankuna na da muhimmanci saboda suna taka rawa mai girma wajen tafiyar da tattalin arziki da harkokin kuɗi.

Ɓangaren Kayayyakin Amfani

Wannan ɓangare ya ƙunshi kamfanonin da ke samar da kayayyakin da jama'a ke amfani da su a rayuwar yau da kullum.

"Ko tattalin arziki ya shiga wani hali, mutane ba sa daina cin abinci ko amfani da kayayyakin yau da kullum. Wannan ne ya sa irin wadannan kamfanoni kan tsaya daram," in ji shi.

Ɓangaren sadarwa da fasaha

Yayin da duniya ke ƙara karkata zuwa fasahar zamani, kamfanonin sadarwa suna samun karin muhimmanci.

A cewar masanin, ƙaruwar amfani da intanet, hada-hadar intanet da ayyukan fasaha na daga cikin abubuwan da ke karfafa ci gaban wannan fanni.

"Ga matasa musamman, wannan ɓangare yana da saukin fahimta saboda kusan rayuwarsu gaba daya tana da alaka da fasaha da sadarwa," in ji shi.

Me ya sa Hausawa suka yi baya?

Dr. Salihu Lukman ya yi imanin cewa akwai manyan dalilai guda biyu da suka sa mutanen Arewa suka dade ba su da yawa a kasuwar hannun jari.

A cewarsa, na farko shi ne matsalar ƙarancin ilimi a fannoni irin su tattalin arziki, lissafin kuɗi da harkokin banki a wasu lokuta idan aka kwatanta da sauran yankuna.

Dalili na biyu kuma shi ne yadda mutane da dama suka dauki kasuwar hannun jari a matsayin wata hanya ta mu'amalar ruwa.

"A hankali ana kara fahimtar cewa akwai hanyoyi na halal da mutum zai iya saka jari ba tare da shiga haram ba. Wannan fahimtar ce ta fara canja tunanin mutane," in ji shi.

Abin da ya kamata matashi ya yi

Masanin ya gargaɗi masu son shiga kasuwar hannun jari da kada su fara ba tare da ilimi ba.

"Abu na farko shi ne ilimi. Kada ka saka kuɗinka a inda ba ka fahimta ba. Ka fara koyo, ka fahimci yadda kasuwa ke aiki sannan ka fara zuba jari," ya ce.

Ya kuma shawarci masu zuba jari su tantance manufarsu tun daga farko.

Shin suna son su riƙe hannun jarin na dogon lokaci ko kuwa suna son su rika saya da sayarwa domin cin riba cikin gajeren lokaci?

A cewarsa, amsar wannan tambaya ita ce za ta taimaka wajen zabar irin hannun jarin da ya dace.

Hannun jarin Matatar Dangote?

Da yake magana kan IPO na Matatar Dangote, Dr. Salihu Lukman ya ce dama ce da ya kamata masu sha'awar zuba jari su yi nazari sosai a kanta.

Ya bayyana cewa matatar na daga cikin manyan ayyukan masana'antu da aka taba yi a Afirka, kuma fitar da hannun jarinta ga jama'a zai bai wa talakawa damar shiga cikin mallakar wannan babban kamfani.

"Wannan dama ce ga kowa. Ko kai ba mai kuɗi ba ne, an tsara mafi ƙarancin sayayya yadda mutane da yawa za su iya mallakar kaso a kamfanin. Amma kafin ka saya, ka tabbatar ka fahimci abin da kake yi," in ji shi.

Ya kara da cewa hanya mafi kyau ta gina arziki ba ita ce neman kuɗi cikin gaggawa ba, sai dai zuba jari cikin ilimi, haƙuri da kuma tsari mai kyau.