Barcelona na zawarcin Kane, United ta kammala cinikin Ederson

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta bayar da fifiko kan ɗaukar ɗan wasan gaba a bana domin maye gurbin ɗan wasan gaba na Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37, sannan ta sanya kyaftin ɗin Ingila Harry Kane na Bayern Munich, mai shekara 32, da ɗan wasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, da ɗan wasan gaban Chelsea da Brazil Joao Pedro, mai shekara 24, a cikin jerin waɗanda za ta fi nema. (Mundo Deportivo)
Manchester United ta amince da cinikin £46m (€53m) kan ɗan wasan tsakiyar Brazil Ederson, mai shekara 26, daga Atalanta. (Sport Italia)
Ederson dai yana dab da komawa Atletico Madrid amma kulob ɗin na Sifaniya ya fi sha'awar wani dan ƙasar Brazil ɗin inda ta ke son ɗan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes mai shekara 25, wanda shi ma ya ci gaba da zama abin sha'awa ga Manchester United. (Sky Sports)
Liverpool na ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya da matashin ɗan wasan Atletico Nacional ɗan ƙasar Colombia Samuel Martinez, inda ta doke Barcelona da Borussia Dortmund domin siyan ɗan wasan tsakiyar mai shekara 17. (Liverpool Echo)
Newcastle ta bi sahun Aston Villa wajen neman ɗan wasan Osasuna Victor Munoz, mai shekara 22, inda ake ganin dan ƙasar Sifaniyan zai maye gurbin ɗan wasan gaban Ingila Anthony Gordon mai shekara 25 wanda ke hanyar komawa Bayern Munich. (Mirror)
Everton za ta fuskanci hamayya daga Bayern Munich kan sayen ɗan wasan bayan Ingila John Stones, mai shekara 31, wanda zai iya tafiya a kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a Manchester City a bazara. (Teamtalk)
Bayer Leverkusen ta shirya bai wa kocin Bournemouth Andoni Iraola wani zaɓi bayan Crystal Palace idan kocin ɗan ƙasar Sifaniya ya yanke shawarar makomarsa ba za ta kasance a gasar Premier ba, bayan ya bar ƙungiyar ta Cherries a bazara. (Telegraph)
Roma na sha'awar dan wasan gaban Marseille ɗan kasar Ingila Mason Greenwood da ɗan wasan West Ham ɗan ƙasar Holland Crysencio Summerville, dukkansu masu shekara 24. (Calciomercato)
Bournemouth na shirya miƙa tayi ɗan wasan bayan Sporting da Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 22, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan bayan Argentina Marcos Senesi, mai shekara 29, wanda zai bar Cherries idan kwantiraginsa ya ƙare. (Football Insider)
Newcastle da Aston Villa da Leeds United da Brighton da Crystal Palace duk an sanar da su kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Juventus ɗan ƙasar Canada Jonathan David, mai shekara 26.(Teamtalk)











