Saura ƙiris Arsenal ta lashe gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na dab da zama gwarzuwar gasar Premier Ingila ta 2025/26, bayan nasarar da ta samu a wasan hamayyar Landan.
Arsenal ta samu nasara da ci 0-1 a filin wasa na London Stadium, wanda hakan ya ƙara nutsar da West Ham zuwa ƙungiyoyi ukun ƙarshe na gasar Premier da za su faɗa Championship.
Da wannan nasara Arsenal ta haɗa maki 79, cikin wasanni 36 da ta buga, yayin da ya rage saura wasa biyu a kammala gasar ta bana.
Yanzu dai ta baiwa Manchester City wadda ke matsayi na biyu a teburi tazarar maki tara, yayin da take da wasa uku ita kuma da suka rage a gabanta.
A minti na 83 da wasan ne ɗan gaban Arsenal Trossard ya jefa kwallo ɗaya da ta raba ɓangarorin biyu, abin da ya kai Arsenal da shiga gaba a wasan kenan.
Sai dai a minti na 95 Wilson ya farke kwallon a wani yanayi na hatsaniya, abin da ya kai alƙalin wasa da ba da ci saboda kwallon ta haura layi wani ya fito da ita.
Amma daga baya aka duba na'urar da take taimakawa alƙalin wasa kuma aka gano an yi wa Raya laifi, aka kuma kashe kwallon.

Asalin hoton, Getty Images
Gunners na da wasan Burnely a gabanta, wadda tuni ta faɗa gasar Championship mai matsayi na biyu a Ingila.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tana kuma da wasa da Crystal Palace, kamar yadda City take da kwantan wasanta da Crystal Palace ɗin.
Sauran wasanni biyun da suka ragewa City sun haɗa da na Bournmouth wadda ta yi wasa 16 ba tare da an yi nasara a kanta ba.
Sannan za ta kammala gasar ta bana da Aston Villa da ke matsayi na take da fatan zuwa Champions Lig a kaka mai zuwa.
Ya zuwa yanzu ba za a ce ga wanda zai lashe gasar ta Premier ba, kuma idan aka tafi a haka ba za a iya gane gwarzuwar 2025/26 ba har sai a ranar wasan ƙarshe.
Arsenal wadda rabonta da lashe Premier tun 2003/04, sama da shekaru 20.
Tana da wasan ƙarshe na wasan Gasar Zakarun Turai da za ta yi da PSG a ranar 30 ga watan Mayun nan da muke ciki, a birnin Budapest na Hungray.
West Ham da Tottenham duka ƙungiyoyin birnin Landan ne, kuma suke ke matsayi na 17 da 18 a teburin Premier wanda hakan ke nufin abu ne mawuyaci in ɗaya daga cikinsu ba za ta faɗa Championship ba a bana.
Hakan na nufin za a yi rashin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin Landan a kaka mai zuwa ta 2026/27.









