Yaushe za a gane ƙungiyar da za ta lashe gasar Premier?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Shamoon Hafez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai kawo rahoto kan Manchester City
- Lokacin karatu: Minti 3
Wasu mintuna 13 a wasan Everton da Manchester City na daren ranar Litinin, inda aka sharara ƙwallo 6, zai iya zama babbar zagon ƙasa da masu masaukin baƙin suka yi a gasar Premier ta bana.
City, ƙarƙashin Guardiola ce ta shige gaba da ƙallo ɗaya kafin zuwa hutun rabin lokaci, sai dai daga baya Everton sun haye sama, inda suka zura wa City ƙwallo ɗaɗɗaya har uku.
Duk da cewa Erling Haaland ya sake cin wata ƙwallon, sannan kuma Jeremy Doku ya sake mayar da ta uku, aka tashi 3-3, wannan y asa City ta rasa matayinta ga Arsenal, wadda a yanzu ta yi ɗare-ɗare saman teburi.
Hakan ya sanya yanzu Arsenal ce ke da wuƙa da nama a kann wanda zai lashe kofin Premier na wannan shekara.
Dama an yi hasashen cewa wannan wasa zai iya zama mai wahala ga City, ganin cewa Everton na fafutikar samun gurbin buga gasar Turai.
A ƙarshen wasan, kocin City Pep Guardiola ya ce "gara canjaras da rashin nasara."
''Yanzu kofin ba ya hannunmu, a baya yana hannunmu, amma yanzu ya kuɓuce. Muna da sauran wasanni a gaba, za mu ga yadda za ta kaya," in ji Pep.
A yanzu Arsenal ta san cewa ita ce ke da kofi idan har ta lashe dukkanin wasanninta uku da suka rage, kuma idan ta yi nasarar hakan wannan zai zama karon farko da ta lashe kofin tun daga 2004.
Yadda za ku gane ƙungiyar da za ta lashe gasar Premier
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan yin canjaras da Everton, yanzu mafi yawan jimillar maki da Manchester City za ta iya samu shi ne 83, inda ta lashe dukkanin wasannin gasar da suka rage mata.
Ita kuwa Arsenal a halin yanzu tana da maki 76, saboda haka idan kungiyar ta lashe dukkanin wasanninta na gasar za ta ƙare ne da maki 85, kuma hakan zai tabbatar musu da nasara lashe kofin Premier.
Haka nan yanzu Arsenal ce a gaba idan ana magana kan ƙwallye, inda take gaba da ƙwallo 4 a gaban City.
Amma akwai abin da zai faru a tabbatar wa Arsenal nasarar lashe gasar Premier tun daga ranar Laraba 13 ga watan Mayu.
Idan Arsenal ta yin nasara a kan West Ham a ranar Lahadi, ita kuma Manchester City ta yi rashin nasara a karawarta da Brentford a ranar Asabar, sannan City ta sake yin rashin nasara a hannun Crystal Palace a wasanta na gaba, Arsenal za ta lashe kofin Premier kafin wasanta biyu na ƙarshe.
To amma idan dukkanin ƙungiyoyin biyu suka ci gaba da samun nasara a wasanninsu, ba za a san wanda zai lashe kofin ba har sai a ranar ƙarshe ta gasar.
"Hakin da ake ciki Manchester City na cikin tsaka mai wuya, amma dole ne su natsu, su fuskanci abin da ke gabansu," in ji tsohon ɗan wasan Blackpool Charlie Adam a tattaunawarsa da gidan rediyon BBC 5 Live.
Amma kuma har yanzu akwai abubuwan mamaki da za su iya faruwa.









