Me ɗage shari'ar ADC ke nufi?

..

Asalin hoton, Nasiru ElRufai/X

Lokacin karatu: Minti 2

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage zaman sauraron shari'ar da Nafi'u Bala Gombe ya shigar yana ƙalubalantar sabon shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark, har illa masha Allahu.

Mai Shari'a Emeka Nwite shi ne ya sanar da ɗage zaman bayan da mai ƙarar ya sanar da kotun cewa ya nemi alƙalain alƙalai na babbar kotun tarayya da ya mayar da shari'ar zuwa ga wani alƙalin daban.

Shi dai Nafi'u Gombe yana ƙalubalantar kasancewar Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar ADC, inda ya ce kasancewarsu a jagoranci ya saɓa dokokin jam'iyyar da dokokin zaɓe na Najeriya.

Ɗage shari'ar ba tare da sanya rana ba ya janyo kakkausar suka daga jam'yyar ta ADC, inda mai magana da yawunta, Malam Bolaji Abdullahi ya ce hakan wani shiri ne "na jefa ƴan jam'iyyar cikin halin rashin tabbas".

Abin da ɗage shari'ar ke nufi ga ADC

..

Asalin hoton, ADC/X

Barista Haruna Zakari, lauya mai zaman kansa a birnin Kano ya shaida wa BBC cewa ɗage shari'ar ba lallai ya zamowa jam'iyyar ta ADC alkairi ba a nan gaba kasancewar tana neman a gaggauta yanke hukunci.

"Tunda ita ADC tana son a gaggauta yanke hukunci ne domin kammala dukkan tsare-tsare kafin ƙarewar wa'adin da hukumar zaɓe ta bayar, ko kuma sai bayan zaɓe a ce za a ci gaba da shri'a, kenan ba za ta ji daɗin hukuncin kotun ba," in ji Barista Haruna.

Dangane kuma da zaɓin da ya rage wa jam'iyyar ta ADC, Barista Haruna ya ce zaɓi na ya rage mata na neman alƙalin alƙalai ya saka baki.

"Abin da ya kamata ita ADC ta yi yanzu shi ne ta rubuta wa alƙalain alƙalai ta nemi a ɗauke shari'ar daga hannun ita wannan mai shari'ar da ta ɗage zaman tunda ba za ta iya ba cikin gaggawa," in ji Barista Haruna Zakari.

Martanin ADC

..

Asalin hoton, adc/x

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, malam Bolaji Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a ya bayyana ɗage shari'ar da wani ƙoƙarin "yi wa jam'iyyarmu ƙamshin mutuwa".

"Mun samu bayanan da suka sa muka yi imanin cewa irin wannan hukunci wani yunƙuri ne na tilasta mai shari'a Nwite ya yi watsi da shari'ar, ta yadda zai samar da kafar da babban joji zai samu damar ɗauke shari'ar zuwa ga wasu alƙalan da muke zargin za su fi karkata ga matsin lambar siyasa," in ji Malam Bola Abdullahi.

A ranar 30 ga watan Afrilu ne kotun ƙoli ta Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake da cire sunan shugabancin ADC ɓangaren David Mark daga shafin INEC.

Wannan ya sa shari'ar ta koma babbar kotun tarayya domin sauraron ƙarar farko.