Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 12/06/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Misra ta yi kira ga Iran da Amurka da su cimma yarjejeniya

    Misira ta yi kira ga Iran da Amurka da su yi amfani da “damar da ake da ita a yanzu” don cimma yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen yaƙin da suke yi.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Misira ta bayyana wannan kira a cikin wata sanarwa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya janye barazanar ci gaba da kai hare-hare kan Iran.

    Masu sharhi kan al'amuran da suke da masaniya kan halin da ake ciki sun zayyana wasu abu guda huɗu da suka ce su ne ke tarnaƙi ga cimma sulhu tsakanin Iran da Amurka.

  2. Tawagar ƙwallon ƙafar DRC ta isa Amurka domin buga gasar Kofin Duniya

    A karshe, tawagar 'yan wasan ƙwallon ƙafar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta isa Amurka domin halartar gasar cin kofin duniya, bayan ta shafe kwanaki 21 a keɓe saboda ɓarkewar cutar Ebola a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

    Tawagar ta sauka a birnin Houston a jiya ranar Alhamis, bayan ta shafe lokaci tana shirye-shiryen gasar a ƙasar Belgium.

    Za dai ta buga wasanta na farko da ƙasar Portugal a ranar Laraba.

    Kocin tawagar, Sebastien Desabre, ya ce yana fatan 'yan wasansa za su taka rawar gani domin farantawa ƙasarsu da ke fuskantar ƙalub.

  3. Dimokraɗiyya ba tare da tsaro ba tamkar ba ta zauna ba - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi ƴan najeriya da su ƙaunaci Najeriya duk da irin matsalolin da ƙasar ke fama da su musamman matsalar tsaro.

    A jawabinsa na ranar dimokraɗiyya, Tinubu ya ce a daidai lokacin da ƙasar ke murnar cikarta shekaru 27 da mulkin dimokraɗiyya ba tare da samun tangarɗa ba, abubuwa biyu marasa daɗi sun faru da suka haɗa satar yara ƴan makaranta a Oyo da Borno.

    Tinubu ya ce dimokraɗiyya ba tare da tsaro ba to tamkar ba ta yi ƙwari ba, inda ya ƙara da cewa hakan ne "ya sa gwamnatin ta ayyana ta-ɓaci kan matsalar tsaron sannan kuma ta amince ɗaukar ƴan sanda fiye da 50,000 da kuma dubban sojoji.

    Daga ƙarshe Tinubu ya jinjina wa marigayi Alhaji Mashood Abiola wanda ake bikin ranar saboda shi wanda ya ce ya yi siyasa kuma ya samu goyon bayan jama'a daga ɓangarorin addini da na al'adu daban-daban.

  4. An yankewa Yoon Suk Yeol na Koriya ta Kudu hukuncin shekaru 30 a yari

    An yankewa tsohon shugaban ƙasar Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, hukuncin daurin shekaru talatin a gidan yari bisa tuhume tuhumen bayar da umarnin aika jirage marasa matuƙa zuwa Koriya ta Arewa.

    Wakilin BBC ya ce zaman dar dar tsakanin kasashen biyu ya karu ne a 2024, bayan da wani jirgi marar matuki ya watso da wasu takardu cikin babban birnin Koriya ta Arewa.

    Kotun ta ce hakan yunkuri ne na tunzura Pyongyang ta mayar da martani ta hanyar kai hari domin tabbatar da cewa ta karya dokar kawo karshen mulkin soji da aka ayyana.

    Mista Yoon ya fuskanci shari’o’i da dama tun bayan da aka tsige shi daga kan mukaminsa saboda yunƙurinsa na kafa mulkin soji a watan Disambar 2024.

    A watan Fabrairu, an same shi da laifin tayar da ƙayar baya, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

  5. Har yanzu ba mu fitar da matsaya ba kan yarjejeniya da Amurka - Iran

    Iran ta jaddada cewa har yanzu ba ta kai ga yanke hukunci na ƙarshe ba akan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da Amurka ke yi da ita, duk da cewa Shugaba Trump ya sake nanata cewa akwai yiwuwar nan bada jimawa ba za a sanya hannu akan yarjejeniyar.

    Da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa ta bidiyo a daren ranar Alhamis, Mista Trump ya shaida wa taron cewa: “A yau mun kawo ƙarshen yaƙin da muke da Iran.”

    Da dama daga irin waɗannan iƙirarin a baya na cewa yaƙin na gab da ƙarewa ba su tabbata ba, sai dai sabbin kalaman shugaban sun sake ƙarfafa kasuwannin hannayen jari, tare da jawo farashin mai ya sauka.

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce a halin yanzu tana nazarin ƙunshin yarjejeniyar da aka gabatar mata, amma Tehran ba za ta yi sassauci kan mahimman sharuɗɗanta ba.

  6. Abu huɗu da za su iya hana ɗorewar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka

    Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, wadda aka cimma a farko-farkon watan Afrilu, yanzu za a iya cewa tana kan gargarar watsewa bayan jerin hare-haren da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Shugaban Amurka Donald Trump da wani babban jami'in Iran sun yi musayar barazana a farkon watan Afrilu, sannan kuma sun sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakai kan juna bayan musayar hare-hare.

    A ranar Laraba, Amurka ta ce ta kai hari kan na'urorin tattara bayanai na Iran bayan Iran ta kakkaɓo ɗaya daga cikin helikwaftocinta na soji a yankin Gulf.

    Dakarun juyin juya hali na Iran na mayar da martani ta hanyar kai hari kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Jordan, sai dai Kuwait ta ce ta tare wasu hare-haren.

    Sake farfaɗowar yaƙin ya zo ne kwanaki bayan Iran ta kai hari da makamai mai linzami kan Isra'ila a ranar Lahadi, lamarin da ya sanya Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a yammaci da tsakiyar Iran - wanda shi ne karon farko da aka yi musayar wuta kai-tsaye tsakanin angarorin biyu tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

  7. Me ya faru a ranar 12 ga Yunin 1993?

    Zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, shi ne na farko a Najeriya bayan juyin mulki na 1983.

    Zaɓen ya ƙunshi jam'iyyu biyu; Social Democratic Party (SDP) da National Republican Convention (NRC) sakamakon Najeriya na amfani ne da tsarin jam'iyyun siyasa biyu.

    Moshood Kashimawo Abiola (MKO) ne ɗan takarar shugaban ƙasa na SPD, yayin da Bashir Tofa ya yi wa NRC takara.

    Masu sa ido na ciki da wajen Najeriya na ganin zaɓen 12 ga Yuni a matsayin mafi inganci, amma sai aka yi watsi da shi.

    Abubuwan da suka faru da kuma tasirinsu sun ci gaba da zama a zukatan 'yan Najeriya.

    Yana cikin abubuwan da suka mamaye tarihin Najeriya, sannan ranar ta 12 ga Yuni za ta ci gaba da zama ta musamman.

    Domin karanta cikakken labarin ku latsa nan

  8. Wane ne Mahdi, yaushe zai bayyana kuma a ina?

    Kusan ilahirin al'ummar Musulmin duniya sun yi imani cewa a ƙarshen zamani za a yi wani mutum bawan Allah mai suna Mahdi wanda zai yaƙi zalunci sannan ya tabbatar da adalci.

    Sai dai kuma fahimtar wane ne Mahdi da kuma haihuwarsa sun kasance wasu abubuwa masu taƙaddama a tsakanin mazhabobi da ɗariƙu daban-daban.

    Wannan ya sa a tarihi aka samu wasu mutane a baya da suka ayyana kansu a matsayin Mahdi to amma idan tafiya ta yi tafiya sai jama'a su fahimci al'amarin ba haka yake ba - duk da cewa dai rasuwar mai iƙrarin kasancewa Mahdi ba ta sauya wa wasu ra'ayi.

    Wataƙila hakan ne ma ya sa wasu da suka haɗa da malami da waɗanda suka yi imani da zahiri ke da fahimtar cewa babu wani Mahdi da zai zo a ƙarshen zamani.

    Domin sanin haƙiƙanin yadda al'amarin yake, BBC ta tattauna da malamai daga fahimta daban-daban ta addinin Musulunci domin sanin abin da kowane ɓangare ya yi imani da shi dangane da Mahdi.

    Ku latsa nan domin karanta cikakken labarin

  9. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Juma'a. Muna yi wa abokan hulɗarmu na Najeriya murnar cikas ƙasar shekaru 27 na mulkin dimokraɗiyya ba tare da samun tangarɗa ba. Da fatan za a sha hutun ranar ta dimokraɗiyya lafiya.

    To sai dai ka da a manta wajen ci gaba da kasance wa da shafin kai tsaye na BBC Hausa wanda ke kawo muku sahihan labarai kuma da ɗumi-ɗuminsu dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya. Mun gode!