Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 03/06/2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Gobara ta kashe ƴan Najeriya da wasu ƙasashe a India

    Aƙalla mutum 21 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da gobara ta tashi a wani babban gini mai tsawo a Delhi.

    Marasa lafiya da ƴan uwansu da ke karɓar kulawa a wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa ne ke zama a ginin da gobarar ta tashi.

    Rahotanni sun bayyana cewa da dama daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ƴan ƙasashen waje ne, kamar Najeriya, Mozambique da Bangladesh da Laberiya, waɗanda suka je India domin neman lafiya, ko kuma suka rako ƴan uwansu da ba su da lafiya.

    Shaidu sun bayyana cewa wutar ta yi ta bazuwa cikin sauri, lamarin da ya sa waɗanda ke sama kasa tserewa.

    Wakilin BBC ya ce ƴan sanda sun ce an kashe gobarar, sai dai har yanzu ba a san musababin tashinta ba.

  2. 'Yansandan Najeriya sun gano wurin ƙera bindigogin farauta a Yobe

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta sanar da gano wani haramtaccen wurin ƙera makamai a garin Potiskum tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a aikin.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana nasarar a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da ta samu wajen yaƙi da laifuffuka a jihar.

    Kakakin rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce kamen ya biyo bayan sabbin tsare-tsaren da Kwamishinan ƴansandan jihar ya ƙaddamar domin daƙile ayyukan ta'addanci da sauran laifuffuka a faɗin Yobe.

    A cewarsa, a ranar 2 ga Yunin 2026 da misalin ƙarfe shida na yamma, rundunar ta samu sahihan bayanan sirri cewa wasu maƙera na ƙera bindigogin katako da sauran makamai ba bisa ƙa'ida ba.

    Daga nan ne rundunar yankin Potiskum tare da haɗin gwiwar hedikwatar 'yansanda ta gudanar da samame a wani wajen maƙera da ke Tasha Adua kan titin Danchuwa a Potiskum.

    SP Abdulkarim ya ce a yayin samamen an kama mutane bakwai tare da ƙwace wasu kayayyaki da suka haɗa da bindigogi da aka ƙera da dai sauransu.

    Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan waɗanda ake zargin domin gano abokan hulɗarsu da masu sayen makaman da kuma manufar amfani da su.

  3. Kashe-kashen da ake yi a Najeriya sun yi yawa - Hayab

    Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta ce matsalar rashin tsaro da kashe-kashen da ke faruwa a ƙasar ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin Musulmai da Kiristoci duka suna fuskantar irin wannan barazana.

    Shugaban ƙungiyar ta arewa, Rabaran Joseph Hayab, ya bayyana haka yayin da yake bayani kan matakin da CAN ta ɗauka na ayyana kwanakin jimami na ƙasa tare da kira ga gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro.

    A makon nan ne CAN ta sanar da ayyana ranakun jimami na ƙasa daga ranar 12 ga Yuni, 2026, tare da ayyana ranar Lahadi 14 ga Yuni a matsayin baƙar Lahadi "Black Sunday" a dukkan majami'un Najeriya domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da tashin hankali a sassan ƙasar.

    Matakin ya biyo bayan taron shugabannin mabiya addinin kirista da aka gudanar a Abuja.

    Da yake amsa tambayar dalilin da ya sa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki yanzu duk da cewa an daɗe ana fama da matsalar tsaro a jihohi kamar Borno da Kebbi, Hayab ya ce lamarin ya kai matakin da ba za a iya ci gaba da yin shiru a kansa ba.

    "Kashe-kashen ya yi yawa, dole ne mu fita mu nemi mataki. Ba wai akwai wanda Allah ya halitta da ya fi wani ba. Duk sace-sacen da aka yi a baya da waɗanda ake yi yanzu sun shafi 'yan Najeriya ne, Musulmai da Kiristoci," in ji shi.

    Jami'in na CAN ya kuma yi zargin cewa tun farko shugabanni da 'yan ƙasa sun kasa fuskantar ainihin matsalar yadda ya kamata. A cewarsa, maimakon mayar da hankali kan magance matsalar, mutane sun shafe lokaci suna musayar zargi da musanta abin da ke faruwa.

    Ya ce yanzu lamarin ya kai matsayin da kowa ya fahimci girman barazanar da ke tattare da shi.

    "Wuta ce da za ta cinye mu gaba ɗaya da gidan talaka da na mai kuɗi da gidan Arewa da na Kudu da gidan Kirista da na Musulmi. Wannan abu ne da ya shafi kowa da kowa," in ji shi.

    Ya kuma yi kira ga Musulmai da sauran 'yan Najeriya da su haɗa kai wajen neman mafita ga matsalar tsaro, yana mai cewa ba batun CAN kaɗai ba ne.

  4. Aƙalla mutum 63 sun jikkata a harin Iran kan filin jirgin saman Kuwait

    Ma’aikatar Lafiyar Kuwait ta ce aƙalla mutum 63 ne suka jikkata, ciki har da ma’aikatan filin jirgin sama da fasinjoji, sakamakon harin da Iran ta kai kan Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Kuwait.

    Tun da farko, ma’aikatar harkokin wajen Kuwait ta sanar da cewa mutum ɗaya ya mutu a harin.

    Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin lalacewar ginin Terminal 1 na filin jirgin saman da kuma wasu wuraren jakadanci.

    Iran ta ce Amurka na amfani da ƙasar Kuwait wajen kai hare-hare a kan ƙasarta, kuma tana ɗora alhakin hakan kan shugabannin Kuwait.

    A nata ɓangaren, ƙasashen Kuwait da Qatar sun yi allawadai da hare-haren da Iran ta kai, tare da bayyana su a matsayin abin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

  5. Kotu ta yanke wa mutum huɗu da hannu a harin cocin Owo hukuncin kisa

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Emeka Nwite ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin hannu a harin da aka kai a Cocin Katolika ta Saint Francis da ke Owo a Jihar Ondo ranar 5 ga Yunin 2022.

    Waɗanda aka yanke wa hukuncin na cikin mutum biyar da ake tuhuma a gaban kotun kan laifuka tara da suka shafi ta’addanci, bayan ƙarar da Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar a kansu dangane da harin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 40 tare da jikkata fiye da mutum 100.

    A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya same su da laifuka tara da suka haɗa da kasancewa mambobin ƙungiyar Al-Shabab mai alaƙa da ISWAP da haɗa baki domin aikata ta’addanci da satar mutane da kuma kashe masu ibada sama da 40 a harin cocin.

    Kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen huɗun ba tare da wata shakka ba, lamarin da ya sa aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

    Sai dai kotun ta wanke mutum na biyar daga cikin waɗanda ake tuhuma, bayan da ta ce masu gabatar da ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar da laifinsa.

    Harin da aka kai Cocin Saint Francis da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Owo ya girgiza Najeriya a lokacin, inda ‘yan bindiga suka buɗe wa masu ibada wuta yayin gudanar da bauta.

    Lamarin ya jawo allawadai daga sassa daban-daban na ƙasar tare da kira ga gwamnati da ta tabbatar an kamo masu hannu a harin kuma an hukunta su.

  6. Mojtaba Khamenei na da rawa a tattaunawar Iran da Amurka - Trump

    Donald Trump ya bayyana cewa Iran ta amince ba za ta nemi mallakar makaman nukiliya ba, yayin da ya kuma ya ce ɗan Ayatollah Ali Khamenei, Mojtaba Khamenei, na da hannu a tattaunawar da ke tsakanin Tehran da Amurka.

    A wata hira da aka yi da shi a shirin podcast mai suna “Pod Force One,” Trump ya ce ya yi tattaunawa mai zafi da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kan yadda Isra’ila ke ci gaba da farmaki a yankin Lebanon. Sai dai ya bayyana cewa ba zai ce ya yi fushi ba, illa dai ya ce abin ya dame shi.

    Trump ya ara da cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Netanyahu duk da sabanin ra’ayi da suka samu kan wasu batutuwa na siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Rahoton da kafar labarai ta Axios ta fitar ya ce Trump ya kira Netanyahu da "mara hankali" a wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce “ba dan saboda shi ba da yanzu yana gidan yari" tare da nuna cewa ra’ayoyin duniya na kara juya baya ga Isra’ila.

    Rahoton ya jawo cece-kuce mai yawa a Isra’ila da wasu sassan duniya, musamman saboda yadda kalaman suka fito daga shugaban Amurka a lokacin da ake ci gaba da rikici a yankin. Axios

  7. 'Muna buƙatar a gaggauta ceto ƙananan yaran da aka sace a Borno da Oyo'

    Majalisar Dokokin Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta aikin kuɓutar da ɗalibai da malamansu da aka sace a jihohin Oyo da Borno.

    Kiran na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar satar dalibai a fadin ƙasar.

    Majalisar Wakilai ta ce lamarin na ƙara zama barazana ga ilimi da rayuwar yara, yayin da Majalisar Dattawa ta jaddada buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu domin hana sake faruwar irin wannan abu.

    A halin da ake ciki, Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) ta gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, tana neman gwamnati ta ceto daliban cikin gaggawa.

    Sanata Ali Ndume, a wata hira da BBC, ya tabbatar da cewa halin da ake ciki yana da matuƙar tayar da hankali, musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

    Ya ce ya tattauna da wasu ‘yan majalisa kuma an gabatar da ƙuduri a Majalisar Wakilai kan yaran da aka sace daga Borno tun ranar 15 ga watan Yuni.

    “Har yanzu muna da kusan mutane 416 a hannun ‘yan ta’adda da aka ɗauke daga Gwashe, kuma abin ya kai kusan watanni uku,” in ji Ndume, yana mai ƙara da cewa akwai ƙananan yara masu shekaru biyu zuwa uku a cikin waɗanda aka sace.

    "Abun shine, sai an samu fili ake shanya, wato ƴan ta'adda da masu sace mutane suna cin karensu ba babbaka shiyasa suke ci gaba kuma abin yana faɗaɗawa, yanzu abun ya zama kamar aikin samun kudi ne."

    Ya bayyana cewa rashin tabbas kan rayuwar yaran na ƙara jefa iyalai cikin tashin hankali.

    Ndume ya ce dole gwamnati ta ɗauki mataki mai ƙarfi, yana mai cewa akwai buƙatar ƙara jajircewa domin daƙile matsalar da ta daɗe tana ƙara muni.

    “Idan aka dage da gaske, za a iya shawo kan wannan matsala,” in ji shi, yana mai ɗora alhakin abin kan gwamnati da hukumomin da ke da alhakin aiwatar da tsaro.

    Ya kuma yi gargadin cewa rashin kulawa na ƙara ba wa masu satar mutane damar ci gaba da aikata laifuka kamar wata hanyar samun kuɗi.

  8. Mun kai hari kan hedkwatar rundunar ruwan Amurka - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) sun sanar cewa sun kai hari kan hedkwatar Rundunar Ruwa ta Biyar ta Amurka makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

    Wannan sanarwa ta zo ne sa’a guda bayan rahotanni da dama daga kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa an kai hare-hare da makamai masu linzami a wurare daban-daban a Kuwait da Bahrain.

    A cikin wata sanarwa da aka fitar a safiyar Laraba, IRGC ta ce da daddare sojojin Amurka sun kai hari kan wani jirgin dakon mai na Iran kusa da mashigar Hormuz ta hanyar harba wani makami daga sama, lamarin da ya lalata ɗakin injin jirgin.

    Ta ce a matsayin martani ga wannan abin da ta kira “cin zarafi da keta dokokin mashigar Hormuz,” an kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka da Isra'ila mai suna Panaya da makamai masu linzami na sojojin ruwa.

    Sanarwar ta kuma zargi sojojin Amurka da lalata wata hasumiyar sadarwa ta IRGC a kudancin tsibirin Qeshm.

    A cewarta, a matsayin martani, Iran ta kai hare-hare ta sama da na jirage marasa matuƙa kan wani sansanin jiragen sama Amurka tare da kai hari kan hedkwatar Rundunar Ruwa ta Biyar ta Amurka.

    A ƙarshe, IRGC ta jaddada cewa ta yi gargaɗi tun da farko cewa duk wani hari da aka kai mata zai fuskanci martani mai tsanani da ya bambanta da na baya.

    Ta kuma ce duk wani yunkuri na tauye tsaron mashigar Hormuz zai haifar da sakamako mai tsanani ga sojojin Amurka.

  9. Mojtaba Khamenei na raye kuma yana ƙara tasiri a harkokin mulkin Iran - Amurka

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa sabon jaron addinin Iran, Mojtaba yana raye kuma alamu na nuna cewa yana ƙara taka muhimmiyar rawa a harkokin shugabancin Iran.

    Da yake magana a gaban Kwamitin Hulɗar Ƙasashen Waje na Majalisar Dattawan Amurka, Rubio ya ce akwai alamun da ke nuna cewa Mojtaba Khamenei na ƙara shiga cikin al'amuran ƙasar a wani mataki.

    Tun daga ranar 20 ga Maris, ba a sake ganin Mojtaba Khamenei a bainar jama'a ba bayan da kafafen yaɗa labaran Iran suka ce ya samu raunuka a harin farko da Amurka da Isra'ila suka kai.

    Rahotanni sun ce mahaifinsa, Ali Khamenei, ya rasu a wannan harin.

    Wata guda da ta gabata, mataimakin kula da harkokin ƙasa da ƙasa na ofishin jagoran Iran ya ce Mojtaba Khamenei yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da al'amuran da suka shafi ƙasar.

    Marco Rubio ya kuma shaida wa Majalisar Dokokin Amurka cewa Iran ta amince ta tattauna wasu fannoni na shirinta na makamashin nukiliya waɗanda a baya ta ƙi tattaunawa a kansu.

    Ya ce tattaunawar da ke tsakanin Amurka da Iran na ci gaba, amma babu tabbacin cewa za ta kai ga kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

    Rubio ya sake jaddada cewa buɗe mashigar Hormuz yana daga cikin manyan buƙatun Amurka ga Iran.

    Sai dai ya ce ko da Iran ta buɗe mashigar, hakan kaɗai ba zai sa a ɗage mata takunkuman tattalin arziki ba, domin akwai wasu sharudda da dole ne ta cika.

    A gefe guda kuma, kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito daga wata majiya da ba a bayyana sunanta ba cewa musayar saƙonni tsakanin Iran da Amurka ta tsaya na wasu kwanaki.

  10. Iran da Saudiyya sun tattauna kan matsalolin yankinsu

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ba da rahoton cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araqchi, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, inda suka tattauna kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki da kuma wasu muhimman batutuwan da suka shafi yankin.

    Tattaunawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin, musamman bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran a watan Maris na bara.

    A lokacin fara yaƙin, Saudiyya tare da wasu ƙasashen yankin Gulf irin su Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Kuwait sun fuskanci hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami daga Iran.

    Duk da cewa Tehran ta ce sansanonin sojin Amurka da muradunta da ke cikin waɗannan ƙasashe ne take kai wa hare-hare, lamarin ya haifar da matsala a dangantakar diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya.

    A kwanakin baya, bayan Iran ta sanar da kai hari kan wani sansanin sojin Amurka a Kuwait a matsayin martani ga harin da Amurka ta kai kusa da filin jirgin saman Bandar Abbas, Saudiyya ta fitar da sanarwa tana allawadai da harin tare da bayyana damuwarta kan ƙaruwar rikici a yankin.

    Sai dai duk da waɗannan saɓanin ra'ayoyi, Iran da Saudiyya na ci gaba da nuna fatan samun mafita ta hanyar tattaunawa.

    Ƙasashen biyu sun sake dawo da dangantakar diflomasiyya a baya-bayan nan tare da shiga tsakanin China bayan shekaru da dama na katse hulɗa

  11. Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait

    Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain, a cewar rahotannin kafafen yaɗa labarai masu kusanci da rundunar juyin juya halin Iran (IRGC).

    Wannan sanarwar ta zo ne mintuna kaɗan bayan wasu kafafen labarai masu alaƙa da IRGC sun ba da rahoton cewa an harba makamai masu linzami zuwa sansanonin Amurka da ke Kuwait.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da kusanci da IRGC, ya ce an kai hare-haren ne a lokaci guda da kuma cewa an ji aƙalla ƙarar fashewa uku a ƙasar Kuwait.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa an ji wata fashewa a gaɓar tekun tsibirin Qeshm na Iran.

    A cewar kamfanin dillancin labaran, ana zargin wani makami ya faɗi a yankin da ke tsakanin birnin Souza da ƙauyen Masan da ke tsibirin.

    Rundunar Sojin Amurka (CENTCOM) dai ta ce ta kakaɓo wasu makaman da Iran da kai mata hari da su.

  12. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Laraba - ta-bawa, ranar samu.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.