Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 25/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80 a duniya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasar, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC), Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa.

    Tinubu ya tuna da irin goyon bayan da ya bai wa Atiku a lokacin da yake neman shugabancin ƙasar a shekarar 2007.

    Tinubu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa ranar Laraba, inda ya ce duk da bambance-bambancen siyasa da ke tsakaninsu a yanzu, haɗin kan Najeriya da zaman lafiya su ne abubuwan da ya kamata a bai wa muhimmanci.

    “Ina taya murna ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, bisa cika shekaru 80 a duniya yau, Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026.”

    Ya kuma yaba wa Atiku bisa gudunmawar da ya bayar wajen cigaban ƙasa a tsawon shekaru.

    A cewarsa, goyon bayan da ya bai wa Atiku lokacin takarar shugaban ƙasa a 2007, ya nuna irin imanin da yake da shi na cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan ’yan siyasa suna da ’yancin shiga harkokin siyasa da bayar da gudummawa ga shugabanci da yadda ake tafiyar da mulki.

    Tinubu ya ce ya daɗe yana da'awar ganin tsarin siyasa ta ta’allaka kan buƙatar zurfafa dimokuraɗiyya, ƙarfafa cibiyoyin siyasa, mutunta ra’ayoyi da kuma samar da yanayi mai ɗorewa.

  2. Mutum 19 sun mutu a harin RSF a Sudan

    Aƙalla mutum 19 sun mutu sakamakon hare-haren jiragen marasa matuƙa da dakarun RSF suka kai jihar Blue Nile ta Sudan.

    Wata ƙungiyar lauyoyi ta ce wasu mutane 20 sun jikkata a hare-haren da aka kai Damazin babban birnin jihar da kuma garin Roseires.

    Jirage marasa matuƙan sun kai wa cibiyoyin samar da makamashi da sansanin sojoji da kuma unguwannin fararen hula hare-haren.

    Dakarun RSF waɗanda ke faɗa da sojojin Sudan tun shekara ta 2023, na ci gaba da ƙoƙarin fadaɗa yankunan da ke ƙarƙashin ikon su a jihar wadda ta yi iyaka da Habasha.

  3. El-Rufai ya musanta 'kutse' a wayar Ribadu

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta zargin yin kutse a wayar malam Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro.

    El-Rufai ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin kare kansa a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya kuma ce bai taɓa umartar wani ya yi hakan ba.

    Tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa bai taɓa mallakar wata na’ura da ake amfani da ita wajen sauraron tattaunawar waya ba, kuma ba shi da ilimin fasahar da ake buƙata domin yin hakan.

    El-Rufai ya kuma musanta cewa yana da damar shiga hanyoyin sadarwa ko na’urorin da Ribadu ke amfani da su.

    Ya jaddada cewa kalaman da ya yi a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairu maganganun siyasa ne kawai, ba kuma cewa ya yi kutse ko ya saurari tattaunawar wayar Ribadu ba.

    El-Rufai ya ce: ''Abin da nake nufi shi ne gwamnati na sa ido kan 'yan adawa, kuma muna sane da abin da suke yi.''

  4. Harin Isra'ila ya kashe jami'in Hamas da ƴan uwansa uku a Gaza

    Wani babban jami’in tsaro a ƙungiyar Hamas da ƴan uwansa uku sun rasa rayukansu sakamakon harin da Isra’ila ta kai birnin Gaza da safiya wannan Laraba.

    Hukumar agajin gaggawa ta Gaza ta ce harin da aka kai sansanin ƴan gudun hijira na Shati, ya kashe Mohammed Abuelouf da matarsa da ƴa ƴansa mata biyu.

    Wannan shi ne hari na biyu da Isra’ila ta kai cikin sa’o’i 24 wanda ya yi sanadin mutuwar wani jagoran Hamas.

    A ranar Talata Isra’ila ta kashe Naeem Abu Nahel, shugaban rundunar tsaron cikin gida ta Hamas.

    Isra'ila na ci gaba da kai hari Gaza kusan kowacce rana, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a bara.

  5. Pete Edochie ya taka rawa wajen gina Nollywood - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen jarumin fina-finai ta Nollywood, Pete Edochie, inda ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jaruman Najeriya kuma wadanda suka assasa masana'antar shirya fina-finai ta ƙasar.

    Tinubu ya ce Edochie, wanda aka fi sani da "Ebube Dike", ya taka muhimmiyar rawa wajen gina masana'antar Nollywood da kuma tallata al'adun Najeriya ta hanyar fitattun fina-finai da ya taka a cikinsu.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, bayan samun labarin rasuwar jarumin.

    Ya bayyana Edochie a matsayin jarumi na musamman kuma ɗaya daga cikin wadanda suka fara kafa masana'antar Nollywood, yana mai cewa tasirinsa ya wuce abin da aka gani a fina-finai.

    Shugaban ya kuma tuna rawar da Edochie ya taka a matsayin Okonkwo a cikin shirin talabijin na gidan talabijin na NTA da aka shirya daga shahararren littafin Things Fall Apart na marubuci Chinua Achebe a shekarun 1980.

    Tinubu ya kuma tuno irin rawar da jarumin ya taka a fina-finai irinsu Igodo, Rituals da kuma Lionheart.

  6. Boko Haram ta hallaka sojojin Nijar 11 a Diffa

    Aƙalla sojojin Nijar 11 ne suka mutu bayan wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai musu.

    Harin ya afku ne a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar a ranar Talata 24 ga Nuwamba, kusa da ƙauyen Baroua, inda aka kuma jikkata sojoji biyar.

    Wata sanarwa da hukumomin yankin na Diffa suka fitar, ta nuna cewa an yi wa sojojin ƙwantan-ɓauna ne lokacin da suke raka ayarin wasu mutane zuwa Tafkin Chadi domin gudanar da sana'arsu ta kamun kifi.

    Rahotanni sun ce mayaƙan sun buɗe wa ayarin motocin kusan goma wuta lokacin da suka isa kusa da Tafkin Chadi, inda sojoji suka mayar da martani.

    Yankin na Diffa ya shafe lokaci yana fama da hare-hare da ake alaƙanta mayaƙan Boko Haram da takwarorinsu na ISWAP da kai wa.

  7. An samu Huawei da laifin satar bayanan kasuwanci

    An samu kamfanin fasahar sadarwa na Huawei da laifin haɗa baki wajen satar bayanan kasuwanci da kuma damfarar bankuna.

    A shari’ar da aka kwashe watanni biyu ana yi, masu gabatar da ƙara sun zargi kamfanin da yin ƙarya, yaudara da kuma sata domin samun tagomashi kan abokan kasuwancinsa.

    Tawagar lauyoyin Huawei ta ce masu gabatar da ƙarar sun riga sun ɗauki kamfanin a matsayin ƙungiyar masu aikata laifi, sannan suka gina hujjojinsu a kai, ,amma sun jaddada cewa nasarar kamfanin ta samo asali ne daga ƙirƙire-ƙirƙire da kuma sabbin fasahohin da ya samar.

    Kamfanin ya ce zarge-zargen ba su da tushe, tare da yin barazanar ɗaukar matakin shari'a kan lamarin.

    A ɗaya gefen, an wanke kamfanin daga wani babban zargi na gudanar da wata ƙungiyar masu aikata laifuka.

    Hukuncin ya kawo karshen shari'ar da aka shafe shekaru takwas ana yi tsakanin gwamnatin Amurka da Huawei, wanda shi ne kamfani mafi girma a duniya wajen kera kayayyakin sadarwa.

  8. An kama wani mutum kan zargin tono gawa a makabartar Kebbi

    Rundunar ƴansanda a jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 30 mai suna Tapro Tareza, wanda ake zargi da tono wata gawa a makabartar Machika da ke yankin Ribah.

    An kama mutumin mazaunin ƙauyen Changu ta Gwazawa da ke ƙarƙashin gundumar Kanya ne bayan rahotannin da aka dade ana samu na lalata kaburbura a makabartar.

    Wata sanarwa da kakakin ƴansanda a jihar, SP Bashir Usman ya fitar ranar Talata, ta ce an kama mutumin ne da yammacin ranar 10 ga Nuwamba, jim kaɗan bayan binne wani mamaci.

    Binciken farko da aka gudanar, ya gano cewa ana zargin mutumin da cire wasu sassa daga jikin gawawwaki, inda ya kuma amsa cewa yana da hannu a lalata kaburbura a makabarta, ciki har da cire likkafanin wani mamaci ya tafi da shi.

    Yansandan sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutumin, inda za a gurfanar da shi idan aka same shi da laifi.

    Sun kuma yaba wa al’ummar yankin bisa taka-tsantsan da haɗin gwiwar da suka nuna, tare da gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

  9. Fitaccen tauraron fina-finai Pete Edochie ya rasu

    An tabbatar da mutuwar ɗan wasan fim na Najeriya Pete Edochie.

    Iyalan shahararren ɗan fim ɗin ne suka fitar da sanarwar rasuwarsa yana da shekara 79 a duniya bayan ya yi fama da cutas kansar bakin mafitsara.

    Edochie ya rasu ne da kimanin ƙarfe 12:30 na daren ranar Laraba.

    Edochie tsohon ɗan jarida ne kuma ɗan fim wanda ya yi suna a kan rawar da ya taka a fina-finan Najeriya, kamar labarin 'Things Fall Apart' da aka yi fim a kan shi, wanda Chinua Achebe ya rubuta.

    Ya rasu ya bar ƴaƴa shida, ciki har da taurarin fina-finai Yul da kuma Linc.

    Fina-finansa da suka shahara sun haɗa da Cross fire, Avenge me Iwene my son, Oracle da kuma Lost Kingdom.

  10. Libya ta ce an kashe mata soji biyu a harin da Ukraine ta kai

    Hukumomi a gabashin Libya sun ce sojojinsu biyu sun mutu sakamakon wani hari da jirgi maras matuki da Ukraine ta kai wa wani jirgin ruwan yaki na Rasha da kuma wani jirgin dakon kaya a birnin Benghazi a ranar Lahadi.

    Mahukuntan sun ce akalla mutum goma sun jikkata.

    A Libya akwai gwamnatoci biyu, ɗaya na zaune a Benghazi da ke gabashin kasar, wadda Rasha ke mara wa baya, da kuma gwamnatin da ƙsashen duniya suka amince da ita wadda ke zaune a Tripoli da ke yammacin kasar.

    Dukkan ɓangarorin biyu sun yi Alla-wadai da harin da Ukraine din ta kai.

  11. An kashe sojojin Rasha 500,000 tun fara yaƙin Ukraine

    Wasu bayanan gwamnati da aka fallasa daga Rasha sun nuna cewa kusan sojojin kasar dubu 500 ne suka mutu tun bayan fara yaki da Ukraine.

    Sashen BBC na Rasha, ya yi nazari kan bayanan mutuwar da wasu masu kutse ta intanet daga Belarus da Ukraine suka samu, inda bayanan suka bayyana irin asarar rayukan da Rasha ta yi a wasu yankuna na Ukraine.

    Bayanan sun nuna cewa kimanin sojojin Rasha dubu 20 ne suka mutu a yayin fafatawar kwace iko da wasu kauyuka goma kacal, wadanda yawan mutanensu kafin barkewar yakin bai wuce mutum dubu 12 ba.

    Rasha dai ba ta fitar da alkaluman mutanen da suka mutu ko suka jikkata a yakin ga jama'a ba.

  12. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.