Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 30 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. DSS ta nemi a ɗage shari’ar Sowore zuwa bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027

    Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde (SAN), da ya nemi a ɗage shari’ar da ake yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, kan zargin aikata laifukan intanet har bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027 kamar yadda Gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    A cewar wata majiya mai masaniya kan lamarin, an ɗauki matakin ne domin bai wa Sowore damar gudanar da yaƙin neman zaɓensa ba tare da shari’ar kotu ta hana shi gudanar da harkokinsa na siyasa ba.

    DSS ta shigar da ƙarar ne bayan wasu saƙonnin da Sowore ya wallafa a shafukansa na X da Facebook a watan Agustan 2025, inda ya kira Shugaba Bola Tinubu da suna “mai laifi”.

    Sai dai Sowore ya musanta zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa shari’ar na da alaƙa da siyasa kuma an ƙaddamar da ita ne domin takaita masa ‘yancin faɗar albarkacin baki.

    Rahotanni sun ce shugaban DSS, Tosin Ajayi, ya yi wata ganawa da jami’an sashen shari’a na hukumar inda aka yanke shawarar neman ɗage shari’ar bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ba da damar fara yakin neman zaɓen 2027.

  2. UAE ta fara binciken rassan Bankin Masar bayan matakin Amurka kan Iran

    Babban bankin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya sanar da fara gudanar da bincike na musamman cikin gaggawa kan rassan Bankin Masar da ke ƙasar, bayan matakin Amurka na katse alaƙar bankin da tsarin kuɗin Amurka domin ƙara matsin lamba kan tattalin arziƙin Iran.

    A cikin wata sanarwa, babban bankin na UAE ya ce binciken zai haɗa da zurfafa nazari kan bayanan da suka shafi lokacin da hukumomin Amurka suka ambata a sanarwarsu.

    Bankin Masar, ɗaya daga cikin manyan bankunan gwamnati a ƙasar Masar, ya ce zai tuntuɓi Ma'aikatar Kuɗi ta Amurka domin neman ƙarin bayani tare da ɗaukar matakan da suka dace.

    Bankin ya kuma tabbatar da cewa rassansa da ke UAE na ci gaba da ba abokan hulɗa hidimomin banki bisa ƙa'idojin da suka dace.

    Matakin da Amurka ta ɗauka na daga cikin ƙoƙarin farko a fili na ware tattalin arziƙin Iran, inda Washington ta ce ta gano hanyoyin da gwamnatin Iran da dakarun juyin juya halin Iran ke amfani da su wajen samun kuɗaɗen shiga, tare da gargaɗin cewa ƙasashen da ke taimaka wa Iran za su iya fuskantar irin waɗannan takunkumai.

  3. Ba za mu mutu ba idan ba mu ci gaba da sarrafa uranium ba - Iran

    Yousef Pezeshkian, ɗan shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian, ya ce rayuwar mutanen Iran ba ta dogara ne kan aikin sarrafa da inganta sinadarin uranium ba, yana mai cewa "idan ba mu yi hakan ba, ba za mu mutu ba."

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Yousef ya bayyana cewa ba ya adawa da sarrafa uranium, kuma yana biyayya ga duk wata shawara da Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran da kuma jagorancin ƙasar suka yanke.

    Sai dai ya ce ya kamata a fahimci dukkan fa'ida da illa kafin ɗaukar kowace irin shawara.

    Ya ƙara da cewa makamashin nukiliyar Iran ba ya dogara kacokan da aikin inganta uranium, yana mai nuni da cewa har yanzu man fetur ɗin da tashar samar da wutar lantarki ta Bushehr ke amfani da shi ana shigo da shi ne daga Rasha, ba a cikin gida ake samar da shi ba.

    Yousef Pezeshkian ya kuma ce akwai wasu fasahohi da suka fi muhimmanci ga tsaro da gudanarwar ƙasar, amma ba a ba su kulawar da ta dace ba, yana mai cewa Iran ba ta nuna irin wannan ƙwazo wajen bunƙasa waɗannan fannoni.

  4. Mun samu matsaya da Oman amma ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta cika alƙawurranta - Iran - Iran

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce duk da cewa Tehran da Muscat sun cimma matsaya kan samar da wata hanyar wucin gadi ta zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, Iran ba za ta buɗe mashigar ba har sai Amurka ta cika alkawurran da ta ɗauka.

    Gharibabadi ya jaddada cewa Mashigar Hormuz har yanzu a rufe take, yana mai cewa idan wani jirgin ruwa ya ratsa ta mashigar, sai da izinin Iran.

    A wani labarin da ke da alaƙa da matsin lambar da ake yi wa Tehran, babban bankin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya sanar da binciken rassan Bankin Masar.

    Matakin ya biyo bayan matakin da Washington ta ɗauka na katse alaƙar bankin da tsarin kuɗi na Amurka, a wani yunkuri na ƙara matsin lamba kan Iran.

  5. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta Lahadi.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.