A Najeriya, yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027,
ka-ce-na-ce sun kaure tsakanin magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na
jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ne dai ya shawarci Atiku da ya janye daga neman shugabancin Najeriya, saboda
cewarsa shekaru sun cimma masa.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin ya karɓi baƙuncin magoya bayan jam'iyyar NDC daga Adamawa, jihar Atiku, inda a cikin jawabinsa ya buƙaci ce su biya su fada wa Atiku cewa ya haƙura da takara, ya koma gefe ya cigaba da riƙe sarautarsa ta Wazirin Adamawa.
Waɗannan kalamai sun haifar da muhawara a tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu, lamarin da ya ƙara bayyana takun-saƙar da
ke tsakanin jagororin siyasar guda biyu.
Da suke mayar da martani, ɓangaren Atiku sun zargi Kwankwaso da goyon bayan Tinubu ta bayan fage, inda wani mai magana da yawun Atikun, Abdulrasheed Shehu Uba Sharaɗa ya ce ba su yi mamaki ba, domin a cewarsa kamata ya yi Kwankwaso ya haɗa ba Tinubu wajen bayar da shawarar domin shi ma ya koma gefe ya huta.
Sai dai jigo a NDC, Yusuf Kofar Mata ya yi martani, inda ya ce wannan kalamai na Kwankwaso yabo ne ba suka ba, domin a cewarsa shekaru baiwa ne, kuma mutane suna so Allah ya musu albarka na shekaru.
Ya ƙara da cewa lallai ya kamata mutane masu shekaru irin su Atiku su koma gefe suna bayar da shawara, domin a cewar Yusuf Ƙofar Mata hakan zai fi kyau.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da hanƙoron ganin jam'iyyun hamayya sun dunƙule waje ɗaya domin fuskantar babban zaɓen ƙasar, inda wasu ke tunanin dunkulewar ce za ta taimaka musu domin samun sauƙin fuskantar jam'iyyar APC mai mulki.
Magoya bayan fitattun ƴan siyasar na arewa sun daɗe suna musayar yawu a kan wane ne ya fi girma da ƙarfi da tarin masoya da ma gogewa a siyasar.
A watannin baya magoya bayan ɓangarorin biyu sun shiga murna bayan jagororin siyasar biyu sun dunƙule a jam'iyyar ADC domin fuskantar APC, amma sai auren ya ƙi daɗi, inda suka rabu bayan lokaci kaɗan.
Atiku Abubakar dai shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, shi kuma Rabiu Musa Kwankwanso shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC, inda zai mara wa Peter Obi baya.
Dangantakar siyasa tsakanin Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso ta daɗe, domin sun shafe sama da shekara 30 suna gwagwarmayar siyasa, lamarin da ya sa ake tunanin ya kamata su kasance makusantan juna a siyasa.
Duk da cewa a wasu lokuta sun kasance a jam'iyyu daban-daban ko kuma sun kara da juna a zaɓe, asalinsu na siyasa ya samo asali ne daga tafiya guda, inda dukansu suke da alaƙa da ƙungiyar siyasa ta 'People's Front of Nigeria' ta Marigayi Shehu Musa Yar'adua a Jamhuriya ta uku, wadda ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin siyasa mafi ƙarfi a wancan lokaci, kafin daga baya suka narke a SDP.