Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Lahadi 23 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. DR Congo da M23 sun amince da tsagaita wuta don ci gaba da tattaunawar zaman lafiya

    Tattaunawar zaman lafiya tsakanin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) da ƙungiyar ’yan tawaye ta AFC/M23 ta samu ɗan ci gaba, amma har yanzu akwai wasu batutuwan da ba a cimma matsaya a kansu ba.

    A cewar wata sanarwar haɗin gwiwa, ɓangarorin biyu sun amince da wata sabuwar yarjejeniya ta tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin, yayin da faɗa ke ci gaba a gabashin DR Congo.

    An cimma wannan matsayar ce bayan kwana biyar na tattaunawa a Switzerland, kuma ta ƙunshi matakai da lokutan da za a bi wajen ci gaba da tattaunawar, ƙarƙashin yarjejeniyar tsarin zaman lafiya da aka sanya hannu a Doha, Qatar, a bara.

    An gudanar da sabon zagayen tattaunawar a Switzerland daga 17 zuwa 21 ga Agusta, tare da taimakon Qatar, Amurka, Togo a madadin Tarayyar Afirka, Switzerland da Hukumar Tarayyar Afirka.

    Bangarorin biyu sun amince da fara aiki da tsarin Expanded Joint Verification Mechanism Plus (EJVM+), wani tsarin da aka ƙirƙira domin sa ido kan take dokokin tsagaita wuta.

    An riga an kafa sakatariyar tsarin, kuma ana sa ran gudanar da aikin tabbatarwa na farko ranar Litinin a Minembwe, wani yanki na Kudancin Kivu da ya sha fama da yaƙe-yaƙe.

    Sai dai har yanzu akwai rashin jituwa kan wasu batutuwa, ciki har da takunkuman da aka kakaba wa M23, sakin waɗanda ake tsare da su, da kuma lokacin aiwatar da sauye-sauyen siyasa.

    Haka kuma, faɗa ya ci gaba a Arewa da Kudancin Kivu, duk da alkawuran tsagaita wuta da aka yi sau da dama. Gwamnatin Kongo da M23 suna zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.

  2. Togo ta tsare 'yan jarida 'yan Faransa biyu da dan Togo daya

    Hukumomin Togo sun bayyana a bainar jama’a a karon farko dalilin da ya sa aka tsare ’yan jaridar Faransa biyu da abokin aikinsu ɗan Togo tun watan Yuli, inda suka ce ana tuhumarsu da “bayar da bayanan ƙarya” da zargin karya dokokin nadar bidiyo ba bisa ƙa’ida ba.

    Gwamnatin ta ce an kama mutanen ukun ne a ranar 27 ga Yuli yayin da suke ɗaukar bidiyo a wata kasuwa da ke arewacin Togo, bayan da suka je wasu wuraren da ba su cikin izinin da aka ba su na aikin.

    Sanarwar da ma’aikatun tsaro da shari’a na Togo suka fitar tare ranar Asabar ita ce bayanin farko da gwamnati ta bayar a hukumance kan lamarin.

    ’Yan Faransan biyu, Gaël Mocaër da Sebastian Perez Pezzani, tare da abokin aikinsu ɗan Togo, Fred Vedomey, suna aiki ne kan wani jerin shirye-shiryen talabijin mai suna Les Routes de l’impossible (“Hanyoyin da Ba Su Da Sauƙi”), wanda kamfanin Faransa Tony Comiti Productions ya samar.

    A baya, ƙungiyar Reporters Without Borders (RSF) ta ruwaito tsarewar tasu, inda ta ce ’yan jaridar suna da takardun da suka dace domin yin aiki a Togo, tare da yin kira da a sake su.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ita ma ta tabbatar da tsarewar, sannan ta ce jami’an Faransa sun ziyarce su.

    A cewar gwamnatin Togo, jami’an tsaro sun kama mutanen ukun a kasuwar Matchatom, a yankin Binah, ranar 27 ga Yuli yayin da suke aiki. Daga cikin kayan aikin da suke amfani da su akwai jirgi mara matuki (drone) wanda ba a bayyana cikakkun bayanansa tun farko ba.

    An kai su babban birnin ƙasar, Lomé, ranar 4 ga Agusta, tare da kayan aikinsu, sannan aka miƙa su ga Babban Daraktan ’Yan Sandan Binciken Laifuka.

    Sanarwar ta ce binciken ya gano “rashin bin ƙa’idoji da dama” wajen shirya da kuma aiwatar da aikin shirya wannan shirin talabijin.

    An gabatar da mutanen ukun gaban mai gabatar da ƙara a Lomé ranar 17 ga Agusta, tare da wani lauya.

    Daga nan aka buɗe binciken shari’a, kuma wani alkalin bincike ya tuhumi mutanen ukun da bayar da bayanan ƙarya, sannan ya bayar da umarnin ci gaba da tsare su.

  3. Me ke sa maza neman maganin ƙara girman mazakuta duk da haɗarinsa?

    Jason ba ya son irin tsarin da ake amfani da wasu abubuwa ake kara girman azzakari inda ake masa lakabi da gwangwanin lemon Koka Kola, saboda ya yi kama da gwangwanin.

    "Wasu mutane suna wuce gona da iri," in ji Jason lokacin da muka haɗu a Manchester.

    Yin tiyatar da aka yi masa ta ƙara girman azzakarinsa da kashi 16% - adadin da shi da abokin zamansa suka gamsu da shi sosai. Ya ce hakan ya ba shi "karin kwarin gwiwa".

  4. NDLEA ta kama dattijuwa mai shekara 101 da cocaine

    Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wata dattijuwa mai shekara 101 bisa zargin sayar da wiwi a Ilisan da ke Jihar Ogun.

    An kama matar ne a ranar 15 ga Agusta, 2026, tare da gram 90 na skunk, wani nau’in wiwi. Hukumar ta ce matar ta amsa cewa tana sayar da wiwar.

    A cewar NDLEA, matar mai shekara 101 ta shaida wa masu bincike cewa ta shiga harkar fataucin miyagun ƙwayoyi ne bayan wata gobara ta ƙone shagon kayan masarufin da take da shi.

    An ruwaito cewa ta ce ’yarta da ke zaune a Legas ce ke kawo mata wiwi duk bayan kwana huɗu domin ta sayar wa kwastomomin yankin.

    Bayan kama ta, Shugaban NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya bayar da umarnin a ba ta beli tare da kai ta wajen ba da shawara saboda shekarunta domin a sauya mata tunani, sannan aka mata ’yarta.

    A wani samame daban a Jihar Akwa Ibom, jami’an NDLEA sun tare wani jirgin ruwa na katako da ake zargin yana ɗauke da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙauyukan masunta a Kamaru, inda aka kama mutane uku da ake zargi.

    Aikin ya haifar da kwace kimanin kilogram 42.622 na miyagun ƙwayoyi, ciki har da kilogram 42.06 na skunk, wasu nau’o’in wiwi, da kuma gram 20 na hodar iblis (cocaine) da aka ɓoye a cikin wani babban kunshin fufun rogo.

    Hukumar ta kuma ce ta yi abin da ta bayyana a matsayin karo na farko da ta kwace miyagun ƙwayoyi da aka shigo da su Najeriya daga Thailand ta hanyar teku.

    Baya ga abubuwan da aka kwace ta hanyar ruwa, hukumar ta ce jami’anta sun kuma gano methamphetamine, skunk, opioids da sauran miyagun ƙwayoyi a ayyukan da suka dogara da bayanan sirri a jihohin Legas, Akwa Ibom, Ondo, Oyo, Kwara, Kano, Abia, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

    NDLEA ta bayyana kamen da kwace-kwaicen ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi.

  5. Har yanzu muna shakkar alaka da Isra'ila - Syria

    Ministan Harkokin Wajen Syria ya ce Damascus na sa ran za a sake dawo da tattaunawa da Isra’ila kan yarjejeniyar tsaro nan ba da jimawa ba.

    Kwanaki kaɗan bayan da Isra’ila ta kai harin sama kan wani sansanin sojan Syria, Asad Shaibani ya jaddada a wata hira da Reuters cewa babban abin da Damascus ke son cimmawa a yanzu shi ne dakatar da hare-haren Isra’ila.

    A cewarsa, domin samun ci gaba a wannan fanni, ya zama dole bangarorin biyu su ɗauki matakai na gina amincewa da juna.

    Shaibani ya ce an dakatar da tattaunawar kan yarjejeniyar tsaro tun bayan fara yaƙin Iran, amma yana sa ran za a sake farawa nan ba da jimawa ba. Ya kuma ce an katse hulɗa tsakanin ɓangarorin biyu bayan da Isra’ila ta kai hari kan wani sansanin sojin saman Syria.

    Gwamnatin Syria na fatan cimma yarjejeniyar zai kasance mataki na ƙarshe da zai kai ga janye Isra’ila daga yankunan Syria.

    Shaibani ya yi kira ga Isra’ila da ta yi amfani da wannan “dama ta tarihi”, yana cewa “ƙofofin diflomasiyya” har yanzu a buɗe suke. Sai dai ya kuma nuna damuwa game da rashin amincewa da juna:

    “Mun yi imanin cewa ya kamata a samu hulɗa, musamman da ɓangaren da yake ci gaba da barazana ga tsaron Syria. Amma idan wannan hulɗar ba za ta haifar da wani amfani ba, ba ma buƙatarta. A halin yanzu, ba mu amince da Isra’ila ba.”

    Amurka ta kwashe fiye da shekara guda tana ƙoƙarin sasanta tsakanin Isra’ila da gwamnatin Shugaban Syria Ahmed al-Sharaa, wanda Washington ke ɗauka a matsayin sabon abokinta a Gabas ta Tsakiya, domin cimma yarjejeniyar tsaro. Sai dai har yanzu waɗannan ƙoƙarin ba su yi nasara ba.

    A wannan lokacin, Isra’ila ta tura dakarunta zuwa cikin yankin Syria tare da kai hare-hare kan wuraren gwamnati da kayan aikin soji, tana mai cewa matsalar tsaro ce dalilin hakan.

    Ofishin Firaministan Isra’ila bai mayar da martani ga buƙatar Reuters ta neman bayani kan kalaman ministan na Syria ba.

  6. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ’yan ta’adda sama da 20 a Borno

    Sojojin Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun ce sun kashe sama da ’yan Boko Haram 20 a wurare daban-daban da ke ƙananan hukumomin Monguno da Biu na Jihar Borno.

    Hedikwatar ta ce an gudanar da hare-haren ne ta amfani da jiragen sama, bisa sahihan bayanan sirri, tsakanin daren 21 ga Agusta zuwa farkon safiyar 22 ga Agusta, 2026.

    Ta ce hare-haren sun yi nasarar raunana wuraren da aka gano, tare da dakile ƙoƙarin ’yan ta’addan na taruwa, sake haɗuwa da juna da kuma gudanar da ayyukansu cikin ’yanci a yankin, kamar yadda tashar Channels mai zaman kanta ta ruwaito.

    A ɗaya daga cikin ayyukan, wani jirgin sama mai aikin leƙen asiri da kai hari ya gano tare da bin diddigin wasu mayaka da ake zargi da su a yankin Aduwa na ƙaramar hukumar Monguno, kafin daga bisani ya gano wata babbar taro a cikin wani ƙauye.

    Bisa ga sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Sojoji, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, bayan bin ƙa’idojin aiki da samun izini, an kai wani hari na musamman kan wurin da aka gano.

    Binciken da aka yi bayan harin ya nuna cewa an samu gagarumin tasiri kan taron ’yan ta’addan, inda kimanin ’yan ta’adda 16 aka kashe a hare-hare biyu na musamman.

    A wani aikin daban da aka gudanar a kusa da Buratai, ƙaramar hukumar Biu, Operation HADIN KAI ta ce wani jirgin saman soji ya gano wasu ’yan ta’adda da ake zargi da su sun taru a wani wuri.

    Bayan ci gaba da sa ido da kuma samun izinin da ya dace, jirgin ya kai hari na musamman kan wurin, inda aka ce an kashe wasu ’yan ta’adda 10.

    Sanarwar ta ce waɗannan ayyukan sun nuna ƙara ingancin tsarin leƙen asiri da sa-ido na Operation HADIN KAI wajen gano tare da dakile motsin ’yan ta’adda kafin su zama babbar barazana ga sojoji da al’ummomin da ke cikin haɗari.

  7. Wata hadakar malamai a Arewacin Najeriya ta amince Tinubu ya zarce

    Wata hadakar malaman Musulunci daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da amincewa da ya sake tsayawa takara a zaben 2027.

    Hadakar ta bayyana matsayarta ne yayin taronta na Muslim Intellectuals Forum, wanda aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello, Sabuwar Sakatariya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

    Hadimin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Isah Muhammad Yusuf, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    A cewarsa, taron ya hada malaman Musulunci da masana daga jihohin Arewacin Najeriya 19, inda suka bayyana amincewarsu da jagorancin Shugaba Tinubu da kokarinsa na magance matsalolin da ke addabar yankin, musamman matsalar rashin tsaro.

    Kungiyar ta kuma kada kuri'ar amincewa da Shugaba Tinubu, tare da kira ga 'yan Najeriya, musamman al'ummar Arewa, da su mara wa shugaban baya da jam'iyyar APC a zaben 2027.

    Goyon bayan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyu da kungiyoyin siyasa ke kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

    A nata bangaren, kungiyar ta ce ta yi imanin cewa jagorancin Tinubu da matakan da gwamnatinsa ke dauka za su taimaka wajen magance kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta.

  8. Hukumomin tsaron Iran sun gano “na’urorin Starlink 997”

    Farajah, rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ce a cikin watanni huɗu na farkon wannan shekara, ta gano “na’urorin tauraron dan adam na Starlink 997 da kayan haɗa su.”

    Shugaban sashen tattalin arziki na Farajah ya ce: “Tun bayan yaƙin kwana 12, ’yan sanda sun ƙara mai da hankali wajen ganowa tare da kwace na’urorin tauraron dan adam na Starlink da kayan haɗinsu. Dukkan sassan ’yan sanda, daga iyakokin ƙasar har zuwa cikin birane, sun fara aiki sosai a wannan fanni.”

    Hossein Rahimi ya kuma ce: “Dangane da wannan batu, an kama mutum 163, sannan an kwace motoci 15 da ke ɗauke da kayan aikin Starlink.”

    A cewarsa, mafi yawan waɗannan na’urori sun shigo ƙasar ne ta iyakokin yamma da arewa maso yammacin ƙasar, da kuma daga Azerbaijan da yankin Kurdistan. Haka kuma, wasu sun shigo ta iyakokin ruwa na kudancin ƙasar, ciki har da hanyoyin Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Oman.

    Wannan fasahar tauraron dan adam da ake amfani da ita wajen haɗa mutane da intanet na duniya haramun ce a Iran. Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran sun ruwaito lokuta da dama na kama mutane saboda mallakar tashoshin Starlink ko saye da sayar da su.

    Cibiyar sadarwar Starlink wata tarin tauraron dan adam ce da aka ƙera domin samar da intanet mai sauri, mai ƙarancin jinkiri, a duk faɗin duniya.

  9. Ƙasar da ta taimaki Amurka a yaƙin tattalin arziki maƙiyarmu ce - Iran

    Ƙasashen da suka shiga “yaƙin tattalin arziki” na Amurka ana ɗaukar su a matsayin abokan gaba

    Jami’an Iran sun ce duk wata ƙasa da ta shiga abin da suka kira “yaƙin tattalin arziki na Amurka da Iran” za a ɗauke ta a matsayin abokiyar gaba.

    A baya Iran ta kai hari kan wasu ƙasashe a yankin da ke karɓar sansanonin sojojin Amurka, waɗanda daga cikinsu ne aka kaddamar da hare-haren Amurka da dama.

    A halin yanzu, tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta tsaya cik, amma Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana a ranar Juma’a cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen rikicin da ya kwashe watanni shida yana gudana.

  10. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.