Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar nauyin harin da aka kai a filin jirgin saman birnin Yamai da safiyar Alhamis.
Zargin wanda aka yi a cikin wata sanarwa da ma'aikatar tsaron ƙasar ta Nijar ta fitar, kuma aka karanta a gidan talabijin na RTN da ke Yamai babban birnin ƙasar, ya yi zargin cewa, ''masu ɗauke da makamai da Macron ke biya" sun kai wani mummunan hari da ya kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu.
Sai dai gwamnatin ƙasar ba ta bayar da wata shiada da za ta tabbatar da wannan iƙirarin ba, kuma Faransa ba ta ce uffan kan batun ba ya zuwa yanzu.
A cewar sanarwar, maharan waɗanda ake zargi suna sanye da rigunan bama-bamai, sun kuma yi kuma tafiya ne a cikin motocin haya da wasu motocin faraaren hula, sun yi yunƙurin afkawa wuraren da ke filin jirgin Diori Hamani ne jim kaɗan bayan karfe 6 na safe agogon ƙasar.
Mahukuntan ƙasar sun ce an kashe maharan guda 22, an kuma raunata huɗu, sannan an kama mutane kusan 20.
Rahotanni sun ce an kama wasu tarin makamai da suka hada da bindigogin RPG-7, da bindigogin AK-47 da bama-bamai da gurneti da kayayyakin sadarwa da kuma dubban alburusai. Jami’ai sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin zaƙulo duk wanda ke da hannu a cikin lamarin.