, Daga Jaridu
Paris St-Germain ta gana da wakilin ɗan wasan Portugal da West Ham Mateus Fernandes. (Foot Mercato - in French)
Chelsea na ci gaba da shawarar wanda zai maye gurbin Liam Rosenior, yayin da take duba wanda zai maye gurbin sa ciki har da mai horar da yan wasan Bournemouth Andoni Iraola.(RMC Sport - in French)
Chelsea na kuma duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan tsakiya Cesc Fabregas, wanda yanzu ya ke horar da ƴan wasan Como da ke Italiya.(Football Insider)
Barcelona na sonMarcus Rashford, da ya ci gaba da zama a ƙungiyar a matsayin dan wasan aro a kakar wasanni mai zuwa, maimakon su biya Manchester United fam miliyan 26a matsayin dan wasan su na din-din din. (Mirror)
Liverpool, da Chelsea, da Tottenham, da Newcastle, da Aston Villa da Newcastle sun nuna sha'awarsu na ɗaukar mai tsaron ragar Manchester City da Ingilan James Trafford.(Goal)