Malamai na zanga-zanga a faɗin Najeriya kan sace ɗaliban Borno da Oyo
Dubban malamai a sassan Najeriya sun fantsama tituna a zanga-zangar gama gari inda suke neman a kuɓutar da gomman ɗaliban da aka sace a jihohin Oyo da Borno.
A ranar Litinin aka soma zanga-zangar da ƙungiyar malamai ta Najeriya ta shirya inda sauran jihohi ciki har da Borno da Kano da Legas da Akwa Ibom da Abuja suka bi sahun jihohin Oyo da Ogun da suka fara tun farko.
Ƙungiyar malaman ta ce zanga-zangar nuna goyon baya ce ga takwarorinsu da kuma ɗaliban da aka sace a wasu hare-hare da aka kai kan makarantu a Oyo da Borno wani lamari da ya jefa fargaba game da tsaron makarantu a zukatan mutane musamman iyaye.
A biranen Maiduguri da Uyo da Legas, ɗaruruwan malamai ne suka yi tattaki kan tituna ɗauke da alluna inda suke rera waƙoƙi tare da neman a gaggauta sakin ɗalibai da malaman da aka sace.
Akasarinsu kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su ƙarfafa matakan tsaro domin magance matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a sassan ƙasar.