Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 30 ga watan Yulin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello

  1. Iran ta sake kai sabbin hare-hare a Kuwait da Jordan

    Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan wurare daban-daban a yankin gabas ta tsakiya, bayan sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kai jerin hare-haren sama da suka kai kan Iran cikin daren jiya.

    Kuwait ta ce wani makami mai linzami da Iran ta harba ya faɗa kan wani gini a arewacin ƙasar, inda ya kashe mutum ɗaya.

    Sojojin Jordan kuwa sun ce sun harbo makamai masu linzami guda biyar da Iran ta harba.

    Tun da farko, sojojin Amurka sun ce sun kai hari kan wurare da dama mallakin rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta Iran, a matsayin martani ga harin makamai masu linzami da Iran ta kai ranar Talata kan wani sansanin sojojin Amurka da ke Jordan.

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ce hare-haren na baya-bayan nan da Amurka ta kai sun kashe mutane uku, ciki har da wani yaro.

  2. 'Hana yara shan sukari na inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu'

    Wani sabon bincike da aka gudanar ya gano shaidar da ke nuna cewa rage yawan shan siga ga yara daga shekara biyu na matuƙar taimakawa wajen kare lafiyar ƙwaƙwalwarsu na tsawon gomman shekaru.

    Binciken wanda jami'ar kimiya da fasaha ta Hong Kong ta gudanar ya yi nazari kan tasirin sukarin a Birtaniya bayan yaƙin duniya na biyu.

    Sakamakon ya nuna mutanen da suke yara a lokacin yaƙin da suka taƙaita shan sukari sun samu kariya daga kamuwa da cutar mantuwa da kusan kashi ashirin da uku cikin ɗari.

  3. Amurka za ta fitar da dala miliyan 600 domin tallafin allurar riga-kafi

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka za ta fitar da kudade har dala miliyan dari shida nan ba da jimawa ba domin Ƙungiyar Gavi, wacce ke taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samar da allurar riga-kafi.

    Tunda farko Sakataren lafiyar Amurka Robert Kennedy ne ya riƙe kuɗaden bayan ya yi amannar cewa Gavi na amfani da sinadaran da aka daina amfani da su wadanda ke da haɗari ga lafiyar dan'adam.

    Sai dai Gavi ta ce matakin na shi ya jefa miliyoyin yara cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake iya ɗauka.

  4. Rasha ta kai mana hare-hare - Ukraine

    Rundunar sojin Ukraine ta ce Rasha ta kai mata hare-hare a yankuna uku na ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan gargadin da shugaba Zelensky ya yi na cewa Rashar na shirin kai masu gagarumin hari.

    Wakiliyar BBC ta ce magajin garin birnin Kyiv ya ce Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami, inda ya ce an samu rahoton gobara a gudunma biyu na birnin.

    Ya zuwa yanzu mutum biyar ne ciki har da yara biyu suka rasu sakamakon hare-haren, sai kuma gidaje da suka rushe.

  5. Amurka ta ce ta kai hare-hare masu ƙarfi a Iran

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta fara kai sabbin jerin hare-hare masu ƙarfi da tasiri kan Iran.

    Hakan na zuwa ne bayan da shugaba Trump ya sha alwashi tare da yin alƙawarin yi wa Iran din luguden wuta mafi muni.

    Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa an kai hari kan matatun man fetur biyu na ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce an samu rahotannin fashewar abubuwa a sassa daban-daban na Iran Iran ma ta bada tabbacin kai hare-hare kan kadadarorin Amurka dake Jordan da kuma kan jiragen ruwa a mashigar Hurmuz.

  6. Farawa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa, barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.