Saudiyya ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami na Yemen
Ƙawancen sojin Saudiyya ya ce ya kakkaɓo makamai masu linzami 10 da aka harba daga Yemen
Ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta wajen yaƙi da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran a Yemen ya ce ya kakkabo makamai masu linzami 10 da aka harba zuwa kudancin Saudiyya.
Hukumomin ƙasar sun kuma ce sun kakkabo wani makami mai linzami da aka harba domin kai hari kan babban birnin ƙasar, Riyadh.
A yau Lahadi ne ake sa ran Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Khalid da ke Riyadh zai koma aiki bayan an rufe shi makonni biyu da suka gabata sakamakon munanan hare-haren makamai masu linzami da suka yi sanadiyar asarar rayuka.
Har yanzu ba a bayyana cikakken matsayin yadda zirga-zirgar jiragen sama ke gudana a filin jirgin saman ba, amma mayaƙan Houthi sun yi gargadin cewa filin jirgin saman na ci gaba da kasancewa cikin wuraren da suke iya kai wa hari.
Houthi dai sun sha kai hare-hare kan filin jirgin saman tun bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da Saudiyya da ƙawayenta ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan da ƙungiyar ke iko da su a Yemen.