Me ya sa malaman addini suka fara nuna inda suka karkata a siyasance?
A tsawon shekaru, malaman addini na daga cikin fitattun muryoyin da al'umma ke saurare a Najeriya, musamman a arewacin ƙasar.
Sai dai duk da tasirin da suke da shi a tsakanin mabiyansu, ba kasafai ake ganin ƙungiyoyin malaman addini suna fitowa tare da bayyana goyon bayansu ga wani ɗan siyasa ko jam'iyya ba.
To amma sannu a hankan na hakan na neman sauyawa, domin kuwa a ƙarshen makon da ya gabata ne wata haɗakar ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci ta arewacin Najeriya ta gudanar da wani taro a jihar Jigawa tare da bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.
Haka kuma, a wani lamari da ya ja hankali, fitaccen malamin Musulunci Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce tasiri da martabar Sanata Abdul'aziz Abubakar Yari kaɗai sun isa Tinubu ya samu goyon bayan Arewacin Najeriya tare da tabbatar wa jam'iyyar APC nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Waɗannan batutuwa sun haifar da muhawara a tsakanin 'yan Najeriya, inda wasu ke ganin cewa malaman addini suna da 'yancin bayyana ra'ayinsu a matsayin 'yan ƙasa kamar kowa.