WHO za ta ci gaba da sa ido kan Uganda duk da ayyana ƙarshen cutar Ebola
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce za ta ci gaba da bibiyar halin da ake ciki a Uganda, duk da cewa hukumomin lafiyar ƙasar sun ayyana cewa ba a da mai ɗauke da cutar Ebola.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido na tsawon kwanaki 42, wanda aka fara ƙirga daga ranar 16 ga watan da ya gabata lokacin da aka sallami mara lafiya na ƙarshe daga asibiti, bayan ya kamu da cutar da ya shigo da ita daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
WHO ta ce ana ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje da sauran matakan sa ido domin tabbatar da cewa cutar ba ta yaɗu tsakanin al'umma ba.
A ranar Laraba ne Uganda ta sanar da cewa ba ta da wani mutum da ke ɗauke da cutar Ebola, bayan shafe makonni ba tare da samun sabon wanda ya kamu da cutar ba.
Mutane 20 ne aka tabbatar sun kamu da sabon nau'in cutar Ebola tun bayan barkewarta a watan Maris. Cikin su, mutum biyu sun rasu, yayin da sauran 18 suka warke.