An zaƙulo matattu daga ɓuraguzai a Kyiv
Jami'ai a Kyiv sun ce an zaƙulo gawawwakin mutum uku daga ɓuraguzan ginin da Rasha ta kai wa hari a Kyiv inda ake ci gaba da aikin ceto sakamakon ɓarnar da hare-haren suka yi.
Aƙalla mutum 144 ne suka ji rauni har da yara biyu, in ji magajin garin. 21 cikinsu suna samun kulawa a asibiti, har da yaro guda.
Rana ta uku ne nan da Ukraine ke bayar da rahoton mace-mace yayin da Rasha ke zafafa hare-hare bayan da yarjejenyar tsagaita wuta ta ƙare ranar Litinin.
A hare-haren na cikin dare, an harba fiye da jirage marasa matuƙa 670 sai makamai masu linzami 56 zuwa sassan Ukraine, kamar yadda Shugaba Volodomyr Zelensky ya bayyana.