An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutum uku a gaban babbar kotun Ttarayya bisa zarginsu da hannu a sace ɗalibai da malamai daga wasu makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa, wanda aka fi sani da Yunusa bin Musa, da kuma Shamsu Adamu Sani, wanda ake kira Abu Itisar.
A ranar 15 ga Mayun 2026 ne wasu masu ɗauke da makamai suka kai hari makarantu uku a jihar Oyo, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai, kuma sun kashe ɗaya daga cikin malaman makarantar, Michael Oyedokun.
Bayan shafe kwanaki 56 a cikin daji, jami'an tsaro suka kuɓutar da su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Juma'ar nan ne gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 10 a kan waɗanda ake zargin a gaban kotun da ke Abuja.
Takardar ƙarar ta ce mutanen uku, waɗanda dukkansu ƴan ƙaramar hukumar Suleja ne a jihar Neja, sun haɗa baki da wasu mutane Muhammad Sani da Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab tsakanin watan Janairu da Mayun 2026 domin yin garkuwa da ɗalibai da malamai a jihar Oyo.
Ana kuma zarginsu da ɓoye bayanai kan waɗanda ake zargin su ne suka shirya lamarin, da alaƙa da ƙungiyar Darul Salam, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Ansaru, da gwamnatin ƙasar ta ayyana a matsayin ta ta'addanci.