Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United na harin Gunn, Arsenal na son Rogers
Mai tsaron ragar Scotland Angus Gunn na iya komawa Manchester United, idan har Nottingham Forest suka saki ɗan wasan. (Sun)
Manchester City na son ɗauko ɗan wasan Faransa Malo Gusto, daga Chelsea. (Talksport)
Arsenal za ta ci gaba da neman ɗan wasan Aston Vila Morgan Rogers duk da cewar Villa ba ta son siyar da ɗan wasan Ingilan. (Sun)
Everton ta fara yunƙurin siyen ɗan wasan Ingila da West Ham, Jarrod Bowen. (Football Insider)
Hull City na harin mai tsaron ragar Manchester United Radek Vite, bayan da ɗan wasan Czech Republic ɗin ya yi bajinta a wasannin da ya buga a matsayin ɗan wasan aro na Bristol City a kakar da ta gabata. (Mail)
Sheffield United ta shiga mataki na gaba a tattaunawa da Manchester City kan siyen Kalvin Philips, inda ɗan wasan Ingilar ke taka leda a matsayin ɗan wasan aro, a kakar da ta wuce. (Football Insider)
Chelsea ta ƙara matsa ƙaimi wajen ganin ta siyi ɗan wasan Como Jacobo Ramon,inda ɗan wasan ke ɗaukar hankulan ƙungiyoyi da dama. (Teamtalk)
Arsenal sun rage buri kan farashin da suka sanyawa ɗan wasanBrazil Gabriel Jesus na fam miliyan 20 da 25, inda Everton suka jima suna son siyen ɗan wasan mai shekaru 29. (Caughtoffside)
Ɗan wasan Manchester United Bruno Fernandes zai ci gaba da zama a Old Trafford bayan da ɗan wasan da ya sanar ƴan wasan ƙungiyar cewar ba shi da shirin barin ƙungiyar duk da wasu kungiyoyi Saudiya da suka so ɗaukar sa, a kakar da ta gabata. (Talksport)
Arsenal da Manchester City na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Sporting Morten Hjulmand, wanda ya zura ƙawallo a wasan Denmark da Ingila a gasa Euro ta 2024. (A BOLA - in Portuguese)