Yaya ƙarfin sojin Nijar yake, kuma mene ne rauninta?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A baya-bayan nan, Jamhuriyar Nijar na yawan fuskantar barazanar kifar da gwamnati da kuma bore daga cikin sojojin ƙasar.

A ranar 29 ga watan Agusta ne wasu sojoji suka yi bore tare da kai hari kan wani sansanin soji da ke filin jirgin saman ƙasar, inda aka ji ƙarar harbe-harbe har zuwa kusa da fadar shugaban ƙasa.

Gwamnatin Nijar ta ce ta daƙile wannan bore tare da kama wasu daga cikin waɗanda take zargi, inda ta kuma yi zargin cewa Faransa ce ke ƙulla mata wannan maƙarƙashiya. Faransa ta musanta zargin, tana mai cewa babu gaskiya a cikinsa.

Rundunar Africa Corps ta Rasha ce ta taimaka wa sojojin gwamnati wajen ƙwato sansanin.

A watan Janairun 2026 ma, mayaƙan ƙungiyar Islamic State a Sahel sun kai hari kan sansanin soji da ke filin jirgin, lamarin da ya nuna irin barazanar da dakarun Nijar ke fuskanta daga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Wasu na ganin cewa waɗannan hare-hare da kuma bore daga cikin sojojin na nuna cewa akwai rauni a tsarin tsaron ƙasar, musamman ganin cewa Nijar na ƙarƙashin mulkin soji tun bayan juyin mulkin 2023.

Sai dai duk da waɗannan ƙalubale, akwai masu ganin cewa dakarun Nijar suna da ƙwarewa da gogewa sosai wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Yaya ƙarfin sojin Nijar yake?

Nijar ce ƙasa ta 120 cikin jerin ƙasashe 145 da ke da ƙarfin soji a duniya, kamar yadda da cibiyar Global Firepower mai bincike kan ƙarfin soji a duniya ta tantance a 2026.

Bayanan sun nuna cewa Nijar na da yawan jama'a, amma adadin dakarunta ba shi da yawa idan aka kwatanta da yawan mutanen ƙasar.

Nijar na da kimanin mutane 26,342,784, inda 7.9, wato kashi 30 na ƴan ƙasar suke da niyyar shiga aikin soja, kuma daga cikinsu kusan miliyan 5.2 sun cancanta, amma ba a ɗaukarsu.

A kowace shekara, kimanin mutane 447,827 ne ke kai wa shekarun shiga aikin soja, sai dai an kiyasta cewa Nijar na da jimillar dakarun soja 30,000 kacal, wato ƙasa da kashi ɗaya na al'ummar ƙasar.

Daga cikinsu, 25,000 sojoji da ke aiki ba dare ba rana. Nijar ba ta da dakarun ko ta kwana.

Sauran 5,000 kuma na cikin sauran hukumomin tsaro.

Bisa ƙiyasin Global Firepower, ƙasar za ta iya ɗaukar mutum 223,914 aikin soja cikin watanni shida zuwa 12 na farko, sannan adadin ya kai 345,051 a shekara ta biyu, 543,110 a shekara ta uku, sannan 656,620 daga shekara ta huɗu zuwa gaba.

  • Ƙarfin sojin ƙasa

Tsarin sojin Nijar ya fi karkata ne ga dakarun ƙasa. An kiyasta cewa tana da sojojin ƙasa 10,000, yayin da take da sojojin sama kusan 1,250.

Nijar ba ta da sojojin ruwa, saboda ƙasa ce da ba ta da gaɓar teku daga dukkan sassan iyakokinta.

  • Ƙarfin sojin sama

Ƙarfin sojin saman Nijar ba shi da yawa. Ƙasar na da jiragen sama 26 ne gaba ɗaya, ciki har da jiragen kai hari guda biyu, jiragen jigilar kaya guda bakwai, jiragen ayyuka na musamman guda biyu da kuma jirage masu saukar ungulu 13.

Daga cikin jirage masu saukar ungulun, biyu na cikin waɗanda aka kera domin kai hari.

Makaman sojin Nijar

Ƙasar na da kimanin motocin yaƙi masu sulke 1,550, amma ba ta da tankokin yaƙi, da manyan bindigogin da ke sarrafa kansu da manyan bindigogin da ake ja da motoci, ko kuma na'urorin harba rokoki masu yawa.

Nijar na da filayen jiragen sama 26 da kusan kilomita 18,949 na hanyoyi, amma ba ta da hanyar jirgin ƙasa ko tashar jiragen ruwa. Tana da kuma kusan kilomita 300 na hanyoyin ruwa da za a iya zirga-zirga a kansu.

Nijar ba ta da jiragen yaƙi na musamman na fighter jets, kuma ba ta da jiragen ɗaukar mai ko jiragen horar da matuƙa.

Rashin jiragen yaƙi na daga cikin manyan raunin da alkaluman ke nuna wa a ƙarfin sojin Nijar.

  • Kasafin kuɗin tsaro

Bayanan cibiyar Global Firepower sun nuna cewa kasafin kuɗin tsaron ƙasar bai wuce dala miliyan 488.4, inda ta kasance matsayi na 115 cikin ƙasashe 145 wajen kashe kuɗi kan tsaro.

A ina rauninta yake?

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara wa sojin Nijar ƙarfi shi ne dogon gogewarsu wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, a cewar wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Afirka, Dominic Francis.

Dakarun Nijar dai sun shafe shekaru suna gudanar da ayyukan soji a yankunan da ke fama da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, ciki har da yankunan ƙasashe maƙwabta.

Bayan ficewar sojojin Faransa da Amurka daga Nijar, gwamnatin sojin ƙasar ta ƙara kusantar Rasha domin samun taimakon tsaro. Dakarun Africa Corps na Rasha suna da sansani a Nijar, kuma sun taka rawa wajen taimaka wa gwamnatin ƙasar wajen daƙile hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Haka kuma, rundunar sojin Nijar na da sojojin sama da na ƙasa, tare da jiragen sama da ake amfani da su wajen ayyukan leƙen asiri da kai hare-hare.

Sai dai Dominic ya ce babban raunin sojin Nijar shi ne cewa, duk da gogewarsu a fagen fama, ƙasar har yanzu na fuskantar "hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai."

Ya ce akwai buƙatar ɗaukar ƙarin jami'an tsaro, musamman saboda matasa na da kaso mai yawa na al'ummar ƙasar kuma da dama daga cikinsu na da ra'ayin shiga aikin tsaro.

Sai dai ya ce duk da waɗannan ƙalubale, Nijar na daga cikin ƙasashen da ake jinjina wa a yankin Afirka, idan aka cire Najeriya da Ghana.

Ya ce dakarun Nijar kan je wasu ƙasashe domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

"Wannan yanayin ta'addanci ne ke ƙara musu rauni, amma ya kamata a ƙara ɗaukar sojoji sosai, a ba su horo da kayan aiki," in ji shi.

Dominic ya ce idan Nijar na son samun ƙarin nasara da ƙarfafa rundunar sojinta, akwai buƙatar ta rungumi fasahohin zamani, musamman ganin yadda salon yaƙi ke ci gaba da sauyawa.

Wasu abubuwan da ke haifar wa Nijar tsaiko a ƙarfin soji

Idan ana nazarin ƙarfin sojin Nijar, manyan ƙalubalen da za a iya cewa suna haifar wa ƙasar da tsaiko su ne:

  • Ƙarancin kayan yaƙi na zamani — Nijar ba ta da tankokin yaƙi, manyan bindigogin atilari ko na'urorin harba rokoki masu yawa.
  • Rashin ƙarfin sojin sama — Tana da jirage 26 ne kawai, kuma ba ta da jiragen yaƙi na fighter jets. Wannan na rage mata ƙarfin iya kai hare-hare daga sama da kare sararin samaniyarta.
  • Faɗin ƙasar da wahalar sufuri — Nijar ƙasa ce mai girman sosai, kuma rashin hanyar jirgin ƙasa da tashar jiragen ruwa na iya sa jigilar ta zama mai wahala
  • Ƙarancin dakarun sojojin da ke aiki — duk da yawan jama'a a Nijar, ƙasar na da sojoji 25,000 ne da ke bakin aiki. Wannan adadin a cewar masana irinsu Dominic ya yi kaɗan idan aka kwatanta da girman yankin da rundunar ke da alhakin karewa.
  • Rashin dakarun ko ta kwana — bayanan Global Firepower sun nuna cewa Nijar ba ta da dakarun ko ta kwana. Wannan na iya zama ƙalubale idan aka samu wani babban rikici da ake buƙatar ƙarin dakarun cikin gaggawa.
  • Ƙarancin kasafin kuɗin tsaro — Haka kuma, ƙarancin kuɗin da ake warewa sojoji na daga cikin abubuwan da ke takaita ƙarfin sojin Nijar.

Sauye-sauye a shugabancin sojoji da Nijar ta yi bayan yunƙurin juyin mulki

Shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sauke babban hafsan sojin ƙasar, Manjo Janar Moussa Salaou Barmou, tare da maye gurbinsa da Birgediya Janar Mahaman Sani Kiaou, wanda shi ne babban hafsan rundunar sojojin ƙasa a halin yanzu.

Hakan ya fito ne a wani rahoto da shafin labarai mai zaman kansa na Actu Niger ya wallafa a ranar 11 ga Satumba.

Ma'aikatar Tsaro ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa, tana mai cewa matakin ya zo ne bisa wata dokar shugaban ƙasa.

Rahoton ya ce: "Ba a bayar da wani bayani kan dalilin cire Barmou daga muƙaminsa ba, duk da cewa yana riƙe da wannan matsayi tun bayan karɓar mulki."

Korarsa daga muƙamin na daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi a rundunar sojin Nijar tun bayan juyin mulkin da ya kai Tchiani kan karagar mulki, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Hakan ya kuma biyo bayan yunƙurin juyin mulkin da aka ruwaito ya faru a ranar 29 ga Agusta.