Birnin ƙarƙashin ƙasa da ke ba mutane mafaka daga zafin rana da sanyin hunturu

    • Marubuci, Selin Ugurtash
    • Aiko rahoto daga, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ƙarnukan da suka gabata, mazauna yankin Kapadokiya da ke Turkiyya sun riƙa fakewa a ƙarƙashin ƙasa domin kare kansu daga hare-haren maƙiya. Daga baya, sun gano cewa waɗannan matsugunai na kuma ba su kariya daga matsanancin zafi da sanyi.

A yau, yayin da duniya ke fama da ƙaruwar zafi sakamakon sauyin yanayi, masana na nazarin ko waɗannan tsoffin matsugunai za su iya zama mafita ga wasu ƙalubalen zamani.

Tsawon miliyoyin shekaru, iska da ruwan sama sun sassaka duwatsun Kapadokiya, suka samar da siffofi masu kama da dogayen hasumiyoyin dutse. A da, mutane na danganta samuwar su da ikon aljanu, shi ya sa ake kiransu da (Fairy Chimneys)

Sai dai a ƙarƙashin wannan shimfiɗar ƙasa akwai wani tsohon birni da aka gina a ƙarƙashin ƙasa, mai suna Derinkuyu.

Birnin na da hanyoyi masu duhu da ƙanƙanta, amma abin mamaki shi ne yadda yanayin cikinsa yake. Ko da ana tsananin sanyi ko zafi a saman ƙasa, zafin cikin birnin yana kasancewa tsakanin digiri 15 zuwa 17 na ma'aunin Celsius a duk shekara.

An gina birnin ne tun asali domin kare mazauna yankin daga hare-haren rundunonin sojojin Larabawa, tsakanin tsakiyar ƙarni na bakwai zuwa farkon ƙarni na 11.

Yanzu, bayan ƙarnuka da dama, masana na sake duba muhimmancin gine-ginen ƙarƙashin ƙasan, musamman wajen tunkarar sauyin yanayi.

Masu bincike da masu tsara birane na nazarin yadda za a yi amfani da tsoffin dabarun gine-ginen wajen samar da matsugunan da za su kare mutane daga matsanancin zafi da sauran munanan yanayin damina.

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke gudanar da irin wannan bincike ita ce Obrek Cave Research Group, wadda ta shahara wajen bincike da tsara taswirar tsoffin koguna da ramukan ƙarƙashin ƙasa a Turkiyya. Har ma ta gudanar da bincike a ramukan da ke ƙarƙashin shahararren ginin Hagia Sophia.

Ali Yamac, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar, ya shafe shekaru 15 yana binciken koguna da tsoffin gine-ginen ƙarƙashin ƙasa a Kapadokiya.

A cewarsa, kogwanni, ko na halitta ko waɗanda mutane suka haƙa, suna taimakawa wajen daidaita yanayin zafi a duk shekara.

"Ƙogwanni suna kasancewa cikin sanyi a lokacin zafi, su kuma kasance da ɗumi a lokacin hunturu. Wannan babbar fa'ida ce," in ji shi.

Yamac ya kuma tuna da wata tafiyar bincike mai wahala da shi da tawagarsa suka gudanar a lokacin bazara, lokacin da suke neman gano wani sabon matsuguni na ƙarƙashin ƙasa.

Ya tuna wata tafiyar bincike da ya yi a lokacin bazara, inda ya yi addu'ar Allah ya nuna musu wani kogo da za su iya fakewa a ciki.

A halin yanzu, sauyin yanayi na ƙara tsananta zafi da fari a Turkiyya, tare da ƙara barazanar ambaliya. Wani bincike ya nuna cewa mace-macen da matsanancin zafi ke haddasawa a Istanbul na iya ninkuwa har sau goma kafin ƙarshen wannan ƙarni.

A gefe guda kuma, yankin Kapadokiya na fuskantar tsananin sanyi a lokacin hunturu, lamarin da ke tilasta wa mazauna amfani da na'urorin dumama gidaje masu tsada.

Saboda haka, masana na nazarin yadda tsoffin gine-ginen ƙarƙashin ƙasa za su taimaka wajen kare al'umma daga matsanancin yanayin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Tsawon lokaci, masana ba su san da dama daga cikin tsoffin matsugunan ƙarƙashin ƙasa da aka haƙa a yankin Kapadokiya ba.

Sai a shekarar 1963 aka gano birnin Derinkuyu bisa kuskure, lokacin da wani mutum ke gyaran gidansa. Ya rusa wani bango, sai ga shi ya bankado wata hanya mai zurfi da ta ratsa ƙarƙarshin ƙasa.

Wannan bincike ya kai ga gano wani tsohon birni da ba a san da wanzuwarsa ba. Haka kuma, ya taimaka wajen gano dalilin ɓacewar kajin mutumin da ke gyaran gidan, waɗanda suka riƙa shiga cikin ramukan ba tare da dawowa ba.

Abin da ya fi ba shi mamaki shi ne girman birnin. Ana hasashen yana da matakai tsakanin shida zuwa 18, kuma ya zurfafa kusan mita 85. Ya kuma kai tsawon kusan kilomita 2.5, inda ake kyautata zaton zai iya ɗaukar mutane har 20,000. Birnin na da rijiyoyi kusan 53 da kuma tsarin samar da iska.

Ga mutanen zamanin, waɗannan gine-gine ba mafaka daga maƙiya kaɗai ba ne, har ma suna kare su daga matsanancin zafi da sanyi, domin yanayin cikinsu ba ya sauyawa sosai a duk shekara.

Ko da yake ba a amfani da irin waɗannan matsugunai a yau domin fakewa daga munanan yanayi, masana na ganin cewa irin wannan tsarin gine-gine na iya zama da matuƙar amfani a wasu sassan duniya.

Birane na komawa ƙarƙashin ƙasa.

"Mun saba faɗaɗa birane ta hanyar gina dogayen gine-gine, amma yanzu ya kamata mu fara kallon ƙarƙashin ƙasa a matsayin wata dama ta bunƙasa birane," in ji Francesco La Vigna, wani masani kan ilimin ƙasa a Italiya.

Shi da takwarorinsa na tsara taswirar wuraren ƙarƙashin birnin Rome, domin gano waɗanda za a iya amfani da su wajen adana ruwa da kare al'umma daga illolin sauyin yanayi.

Ya zuwa yanzu, sun gano wurare fiye da 7,000, waɗanda suka haɗa da tsoffin wuraren haƙar duwatsu da hanyoyin ruwa, masu faɗin murabba'in kilomita 350.

La Vigna ya ce ya kamata a saka waɗannan wurare cikin tsarin bunƙasa birnin.

Birnin Helsinki na Finland ya zama misali na yadda za a iya amfani da wuraren ƙarƙashin ƙasa a rayuwar yau da kullum. A ƙarƙashinsa akwai hanyoyin gine-gine masu tsawon kusan kilomita 200, waɗanda ke ɗauke da wuraren wasanni, gidajen baje kolin fasaha, wuraren iyo, gidan tarihi har ma da coci.

Kamar yadda aka yi a Kapadokiya, an gina da dama daga cikin waɗannan wurare tun lokacin Yaƙin Duniya na Biyu domin kare jama'a daga hare-hare, amma daga baya aka mayar da su wuraren gudanar da ayyuka daban-daban.

A garin Coober Pedy na Ostiraliya kuwa, mazauna sun rungumi gina gidaje a cikin duwatsu masu laushi domin kare kansu daga matsanancin yanayi. Hakan kuma ya taimaka musu wajen rage kuɗin makamashin da suke kashewa.

Ƙalubale da haɗurran zama a gidajen ƙarƙashin ƙasa.

La Vigna ya ce mayar da wuraren ƙarƙashin ƙasa zuwa mafakar jama'a na buƙatar taka-tsantsan, domin gine-ginen sun bambanta. Wasu tsoffin ma'adinai ne, wasu kuma matsugunan yaƙi ne na zamani.

Babban ƙalubalen shi ne tabbatar da cewa gine-ginen ba za su ruguje ba, tare da samar da isasshiyar iska ga mutanen da za su zauna a ciki.

A Kapadokiya, haɗarin rugujewar koguna da ramukan ƙarƙashin ƙasa na nan daram, musamman ganin cewa Turkiyya na daga cikin ƙasashen da girgizar ƙasa ke yawan faruwa.

Ali Yamac ya ce ayyukan aman wuta da zaizayar ƙasa ne suka samar da yankin, kuma waɗannan sauye-sauyen yanayi na ci gaba da shafar duwatsun har yanzu.

La Vigna ya jaddada cewa wajibi ne masana su tantance ƙarfin kowanne matsuguni kafin a amince da amfani da shi.

Samar da iska mai kyau ma wani babban ƙalubale ne. Duk da cewa Derinkuyu na da ingantaccen tsarin shigar iska, fasahar zamani kamar fanfo da na'urorin auna ingancin iska na iya ƙara inganta shi.

A Helsinki kuwa, ana amfani da irin waɗannan na'urori wajen samar da iska mai kyau a matsugunan ƙarƙashin ƙasa, waɗanda za su iya ɗaukar mutane har 6,000 ko da an rufe ƙofofinsu a lokacin hari.