Wane ne Olu Jacobs, tauraron finan-finan Nollywood da ya rasu?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Fitaccen jarumin Najeriya kuma tauraron masana'antar fina-finan Nollywood, Olu Jacobs, ya rasu yana da shekaru 84.

Iyalansa ne suka sanar da rasuwarsa a shafukan sada zumunta da safiyar ranar Laraba.

"Cikin godiya ga Allah saboda rayuwar da ya yi mai albarka kuma ta gwagwarmaya, muna sanar da rasuwar mijinmu, mahaifinmu, kakanmu da kawunmu. Zakin Lufodo. Oludotun Baiyewun Jacobs (MFR)."

Marigayin ya fara fitowa a shirye-shiryen talabijin na Birtaniya a shekarun 1970 kafin ya shiga harkar shirya fina-finai a Najeriya a shekarun 1980.

Ya kawo wani sabon salo da gogewa mai zurfi daga wasan kwaikwayo na dandali da kuma ƙwarewar aiki a ƙasashen duniya. Ya taka rawa daban-daban a tsawon aikinsa da ya haɗa masana'antar nishaɗi ta Najeriya da ta Birtaniya.

Iyalansa, waɗanda suka sanar da rasuwarsa a ranar 16 ga Satumba, 2026, sun bayyana shi da lakabin "Zakin Lufodo."

Ya rasu ya bar matarsa, Joke Silva, tare da 'ya'yansu da jikokinsu.

Yadda Olu Jacobs ya yi fama da cutar mantuwa

Fitaccen jarumin Nollywood, Olu Jacobs, ya yi fama da nau'in cutar mantuwa na tsawon shekaru kafin rasuwarsa. Matarsa, Joke Silva, ce ta fara bayyana halin da yake ciki a wata hira da ta bayar a shekarar 2021.

A cewar Joke Silva, cutar tana shafar ƙwaƙwalwa da fahimta, kuma tana da alaƙa da matsalolin rawar jiki irin na Parkinson. Ta bayyana cewa mijinta ba koyaushe yake fahimtar abin da ke faruwa a kusa da shi ba, lamarin da ya kasance mai wahala ga iyalinsa.

Yayin da lafiyarsa ke ta tabarbarewa, Olu Jacobs ya daina yawan fitowa a bainar jama'a da kuma cikin fina-finai. A wasu lokuta da ya bayyana a tarukan fina-finai, masoya sun lura da yadda jikinsa ya yi rauni, abin da ya jawo damuwa da tambayoyi kan lafiyarsa.

Duk da ƙalubalen rashin lafiyar, iyalansa sun ci gaba da kula da shi. Haka kuma, sun sha musanta jita-jitar mutuwarsa da ta ria yawo a shafukan sada zumunta a shekarun 2021, 2022 da 2024, suna tabbatar da cewa yana raye a lokacin.

Rayuwar Olu Jacobs

An haifi Oludotun Baiyewun Jacobs a ranar 11 ga Yulin 1942. Ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman Nollywood kuma daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina masana'antar fina-finai ta Najeriya.

Ya yi karatu a makarantar koyon wasan kwaikwayo ta Royal Academy of Dramatic Art (RADA) da ke Landan, Ingila, kafin ya fara sana'arsa a talabijin na Birtaniya da kuma fina-finan ƙasa da ƙasa. Daga bisani ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman Nollywood.

Olu Jacobs ɗan asalin kabilar Egba Alake ne. Ya taso a Kano, inda ya yi karatu a makarantar Holy Trinity School kuma ya shiga ƙungiyoyin muhawara da wasan kwaikwayo.

Sha'awarsa ta wasan kwaikwayo ta ƙaru ne bayan ya halarci wani wasan kwaikwayo na fitaccen ɗan wasan kwaikwayo Chief Hubert Ogunde a Colonial Hotel da ke Kano. Wannan ne ya zaburar da shi ya tafi Ingila domin koyon harkar wasan kwaikwayo.

Ya fara fitowa a shirye-shiryen talabijin na Birtaniya da wasu fina-finan duniya, sannan ya yi aiki da gidajen wasan kwaikwayo daban-daban a Birtaniya. Bayan dawowarsa Najeriya, ya zama ɗaya daga cikin manyan taurarin Nollywood.

A tsawon rayuwarsa, ya fito a fina-finai sama da 100, inda ya shahara wajen taka rawar sarakuna, dattawa da jagorori masu cikakken iko da hikima.

Daga cikin manyan lambobin yabon da ya samu akwai:

  • Kyautar Africa Movie Academy Award ta jarumin da ya fi kowanne a shekarar 2007.
  • Industry Merit Award a bikin Africa Magic Viewers' Choice Awards na 2013.
  • MAA Lifetime Achievement Award a shekarar 2016.
  • Lambar girmamawa ta ƙasa ta (MFR) a shekarar 2011.

A shekarar 1989 ya auri shahararriyar jarumar Nollywood Silva. Tare suka kafa masana'antar fina-finai na Lufodo Group da kuma Lufodo Academy of Performing Arts, waɗanda suka taimaka wajen horar da sabbin masu fasaha da ci gaban harkar fina-finai a Najeriya.