Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda BBC ta gano gidan Putin na gaɓar teku da ake yi wa gyara na sirri
Shari'o'i da hotunan tauraron ɗan’dam da kuma tallar neman ma'aikata sun ba da alamu kan aikin gina gidaje ga ma'aikatan gine-gine da ke kusa da wurin ninƙaya.
An kuma yi alƙawarin ba su abinci kyauta da kuma kuɗi.
Dukkan waɗannan bayanai sun bayyana yadda aka gudanar da manyan ayyukan sake gina da zamanantar da gidan shugaban Rasha Vladimir Putin da ke gabar Tekun Bahar Aswad, wanda aka fi sani da Bocharov Ruchey.
Wannan wuri ne mai natsuwa da salama da ke birnin Sochi.
A tarihi, manyan shugabannin Tarayyar Soviet da Rasha irin su Nikita Khrushchev da Leonid Brezhnev da kuma Boris Yeltsin, wanda ya jagoranci Rasha bayan rushewar Tarayyar Soviet, sun yi amfani da wurin.
Shugaba Putin ya fara zama a wannan gidan ne a watan Mayun shekara ta 2000, jim kaɗan kafin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a karon farko.
Tun daga lokacin, ya karɓi bakuncin shugabannin ƙasashe daban-daban a wurin a lokuta da dama.
A hukumance, an ayyana wurin a matsayin gidan shugaban ƙasa.
Kamar yadda shugaban Sashen Kula da Kadarorin Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Kozhin, ya bayyana, hakan na nufin shugaban ƙasar na iya zama a wurin da aiki da gudanar da rayuwarsa tare da sauke dukkan nauyin da ke kansa na shugaban ƙasa, ciki har da aikinsa na babban kwamandan rundunar sojin ƙasar.
A cewar jaridar Financial Times, a shekarar 2021 — shekara guda kafin Rasha ta ƙaddamar da cikakken farmakinta kan Ukraine — Putin ya ziyarci Sochi sau 24.
Sai dai a shekarun 2024 da 2025, sau biyu kacal ya je birnin.
Raguwar yawan ziyarar shugaban ƙasar zuwa gabar Tekun Black Sea ta zo ne a daidai lokacin da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Ukraine ke kai wa yankin hari akai-akai.
Sai dai wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa, maimakon gwamnatin Rasha ta yi watsi da Bocharov Ruchey, ta fara gudanar da wani gagarumin aikin sake gina wurin wanda ya fi na baya girma, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro fiye da kowane lokaci.
A shekarar 2024, hukumomi sun fara rushe tsofaffin gine-ginen wurin ba tare da sanarwa ba.
Zuwa watan Satumban 2025, an samu wani babban rami a wurin sakamakon aikin tono ƙasa mai yawa.
A wannan shekarar kuma, hukumar tsaron shugaban ƙasar Rasha, FSO, ta yanke shawarar tsaurara matakan tsaro sosai a Bocharov Ruchey.
Ta kuma kafa wani yanki na musamman na tsaro da ya mamaye fiye da murabba'in kilomita uku a kewayen wurin.
Zuwa kaka na shekarar 2026, hotunan tauraron ɗan’adam da BBC Russia ta nazarta sun nuna wasu manyan sabbin gine-gine a fili.
Ana gina gine-ginen ne a wani fili da ya fi tsohon wurin girma sosai.
Sai dai ba a rushe dukkan tsofaffin gine-ginen wurin ba.
Ginin da aka ginawa wasannin Olympics na lokacin hunturu na Sochi na shekarar 2014, wanda ake kira Bocharov Ruchey-2, har yanzu yana nan.
Putin ya ci gaba da karɓar manyan baƙi a wurin, ciki har da shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, Rafael Grossi, a shekarar 2024.
Har yanzu hukumomi ba su fitar da wani bayani a hukumance game da sabon ginin ba. Sai dai binciken BBC ya gano wasu shaidu da suka samo asali daga takardun hukuma.
A yayin wani rikici tsakanin 'yan kwangila kan hukuncin wata kotu, BBC ta gano wani bayani game da kwangilar da aka yi karkashin shirin sayen kayan aikin tsaro na gwamnati.
An gano kwangilar mai lamba 2327202903572000000000000.
Sau da yawa ana takaita bayanan da suka shafi irin waɗannan kwangiloli. Sai dai wannan lamba guda ta bayyana muhimman bayanai da dama.
Lambobi huɗu na farko suna nuna shekarar da aka sanya hannu kan kwangilar da kuma shekarar da za ta ƙare, wato daga 2023 zuwa 2027.
Lambobi uku da suka biyo baya, wato 202, su ne lambar da ke wakiltar hukumar da ta bayar da kwangilar, wato FSO.
Yayin da take neman wasu hukunce-hukuncen kotu da suka shafi rikice-rikicen da aka samu tsakanin 'yan kwangila ƙanana da ke aikin Bocharov Ruchey, BBC ta gano cewa babban ɗan kwangilar aikin shi ne TSI Group, kamfanin da aka yi wa rajista a yankin Crimea da Rasha ta mamaye.
Ɗaya daga cikin waɗannan rikice-rikicen ya shafi cibiyar tsara gine-gine ta Sevastopol, wadda aka fi sani da Voen Mor Proekt-30.
Bayan 'yan watanni da fara aikin ginin a farkon shekarar 2025, cibiyar ta kasa kammala aikinta cikin lokacin da aka tsara.
BBC ta kuma gano wasu tallan neman ma'aikatan gine-gine da aka wallafa a shafukan sada zumunta da kuma wasu shafukan neman aiki.
Tallan sun nuna cewa ana neman masu aikin shimfiɗa duwatsu da ƙwararrun aikin ƙarfe da masu aikin kankare.
Wasu daga cikin tallan sun ambaci sunan Bocharov Ruchey kai tsaye.
Ɗaya daga cikin tallan ya ce: "Ana gina mafaka. Ana buƙatar izini na musamman kafin shiga wurin. Wurin: Bocharov Ruchey."
Wani tallan kuma ya yi gargadin cewa: "Wannan wurin yana ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro."
Wani tallan da aka wallafa a watan Janairun 2025 ya ce ana neman ma'aikata cikin gaggawa a Sochi domin gina wani bene mai hawa biyu a wani "yanki da aka takaita shiga wanda ke buƙatar izini", inda za a biya ma'aikatan albashinsu da kuɗin hannu.
Daga baya a wannan shekarar, wani tallan ya yi magana kan gina wani bene mai hawa huɗu a wani wuri da ake buƙatar tantance katin shaida da fasfo kafin shiga.
An yi wa ma'aikatan alkawarin samar musu da masauki da abinci sau uku a rana da kayan aiki kyauta da kuma kayan aikin da za su sanya a wurin aiki.
An fi bai wa ƙungiyoyin ma'aikata fifiko waɗanda za su iya "aiki tare da injiniyoyinsu da masu kula da ayyukansu", duk da cewa an kuma amince da ma'aikatan da ke aiki da kansu.
Ɗaya daga cikin tallan ya ce: "Aikin sa ido kan fasaha ba shi da wahala sosai. Hukumomin tsaron Rasha suna sa ido kan harkokin kuɗi, don haka komai yana cikin tsari kuma a bayyane."
Ya zuwa shekarar 2026, har yanzu ana neman ma'aikata a wurin da suka ƙware wajen girka fitilu da aikin famfo da kuma sanya ƙofofi.
Wani mai ɗaukar ma'aikata ya rubuta cewa: "Aikin yana da yawa, don haka muna buƙatar ƙarin mutane, amma dole ne su kasance ƙwararrun ma'aikatan fasaha."
Ya yi gargadin cewa wurin yanki ne da aka takaita shiga kuma za a yi wa dukkan ma'aikatan cikakken binciken tsaro.
A baya, 'yan ƙasar Rasha ne kawai waɗanda ba su taɓa aikata laifi ba za su iya neman aikin. Ɗaya daga cikin tallan ya ce: "Za a gudanar da binciken tarihin mutum."
Sai dai daga baya an sassauta waɗannan sharudda. An kuma gayyaci 'yan ƙasar Belarus da Kazakhstan da Kyrgyzstan su nemi aikin, tare da alkawarin samar musu da masauki.
TSI da kamfanin da ke da alaƙa da shi, Trans Stroi Invest, sun taɓa gudanar da ayyukan gine-gine ga gwamnati da hukumomin tsaro.
Kafin aikin Bocharov Ruchey, kamfanin Trans Stroi Invest ya riga ya gina wani gidan zama na Putin.
A shekarar 2019, hukumar binciken Rasha Proekt ta ruwaito cewa kamfanin na da hannu wajen gina wani katafaren wurin zama mallakin gwamnati a yankin Oliva da ke kudancin gabar tekun Crimea da Rasha ta mamaye.
An gina aikin ne a wuraren hutawa na gwamnati da shugabannin Tarayyar Soviet suka taɓa amfani da su, sannan daga baya manyan jami'an Ukraine suka riƙa amfani da su.
Yanzu BBC ta samu wasu hukunce-hukuncen kotu da suka tabbatar da hakan. A cikin takardun kotun, an bayyana wurin a fili da cewa "gidan shugaban ƙasa".
Har yanzu Trans Stroi Invest na gudanar da ayyuka a yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.
Misali, kamfanin na da hannu wajen aikin gyaran tsohon gidan sinima mafi tsufa a Mariupol, mai suna Pobeda, wanda Rasha ta ƙwace a shekarar 2022.
Bisa ga bayanan kwangilolin gwamnati, tsakanin shekarun 2022 da 2025, TSI ta samu kwangiloli 54 na sake gina Cibiyar Yara ta Ƙasa da Ƙasa ta Artek da ke Crimea da Rasha ta mamaye.
Jimillar kuɗin kwangilolin ta kai kusan dala miliyan 330.
BBC ta aika da tambayoyi game da aikin ginin Bocharov Ruchey ga wakilan Trans Stroi Invest, ciki har da ɗan kasuwa mai shekaru 47, Alexey Fomenko, wanda ake ganin shi ne ainihin mamallakin TSI.
An kuma aika da irin waɗannan tambayoyi ga babban aminin Putin, Arkady Rotenberg da kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov.
Sai dai ya zuwa yanzu, babu ɗaya daga cikinsu da ya mayar da martani.