Waɗanne ƴanƙwallo ƙungiyoyinku ke buƙata kafin rufe kasuwar ƴanwasa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

An kammala wasannin makon farko na Premier League, amma har yanzu ƙungiyoyi na da mako guda kafin rufe kasuwar saye da sayar da ƴanwasa domin ƙulla yarjejeniyoyin ƙarshe don ƙarfafa ƙungiyoyinsu.

Sakamakon wasanni ba komai ba ne, amma ga kociyoyi da daraktocin wasanni da dama, wasan tamkar zakaran gwajin dafi ne da zai ba su damar gyara ɓarakarsu, ƴanwasan da ba sa buƙata, da kuma giɓin da har yanzu suke buƙatar a cike.

Yayin da kasuwar hada-hadar ƴanwasa za ta rufe ranar Talata, 1 ga Satumba da ƙarfe 11:00 na dare agogon BST, BBC Sport ta yi nazari kan abubuwan da wasu ƙungiyoyin Premier har yanzu ke buƙata, yayin da magoya baya su ma suke bayyana ra'ayoyinsu.

Arsenal

Mai riƙe da kambun Premier League, Arsenal ta riga ta ƙarfafa tsakiyarta da Bruno Guimaraes, gefen gaba da Christos Tzolis, sannan kuma ta ƙarfafa tsaron bayansu da Ezri Konsa.

Amma Arsenal har yanzu tana kasuwa tana neman ɗan gaba, kuma ta daɗe tana nuna sha'awar Julian Alvarez.

Ko da yake wannan ciniki na iya zama mai wahala saboda dalilai da dama, Gunners za su kasance a shirye su ɗauki mataki idan aka samu damar kammala shi.

Watson, magoyin bayan Arsenal

"Idan kana son ɗan wasan da ya riga ya tabbatar da kansa a Premier League, wanda ya lashe komai daga Kofin Duniya zuwa Champions League, Julian Alvarez shi ne mutumin da zai iya kai Arsenal zuwa matakin da take fata, wato samun nasara a Turai. Musamman ganin cewa babu yawan fitattun ƴan gaba masu inganci a duniya a yanzu."

Aston Villa

Mene ne ma Aston Villa ba ta buƙata a yanzu, bayan ficewar wasu fitattun ƴanwasanta a wannan bazarar?

Batun yiwuwar tafiyar Ollie Watkins, wanda ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ke zawarci, ya sa Villa ke neman wanda zai maye gurbinsa, inda Nicolas Jackson yake cikin waɗanda take hari.

Tana kuma neman ɗanwasan gefe, yayin da ƙungiyar ke buƙatar mai tsaron baya bayan Ezri Konsa ya koma Arsenal.

Villa ta kuma fara tattaunawa kan ɗaukar mai tsaron bayan na Club Brugge, Joel Ordonez, bayan da Southampton ta yi watsi da tayin da suka yi kan Taylor Harwood-Bellis.

Amy Finley, magoyiyar bayan Aston Villa

"A bayyane yake cewa Aston Villa na matuƙar buƙatar ɗanwasan gaba fiye da komai a halin yanzu.

"Ko da yake ina matuƙar yaba wa Victor Lindelof da Pau Torres, abin da suka yi a wasan Brighton ya ɗan tayar min da hankali.

"Don haka, zan yi maraba da ƙarin mai tsaron bayan tsakiya.

"Da alama za mu kasance da ƙarfi a tsakiya idan Johan Manzambi ya dawo daga rauni, tare da zuwan Leon Goretzka."

Chelsea

Magoya bayan Chelsea za su so a sayo wani fitaccen ɗanwasan gaba ko kuma sabon mai tsaron gida da zai maye gurbin Robert Sanchez, wanda bai gamsar da kowa ba a wasa.

Sai dai koci Xabi Alonso yana ganin tawagarsa ta kusan cika kuma ba ta da wata babbar buƙata a wannan bazarar.

Duk da haka, har yanzu akwai babban aiki a gaban ƙungiyar na rage yawan ƴanwasa daga 39 zuwa kusan 25 cikin kwana takwas masu zuwa. Wannan ne babban abin da ya fi ɗaukar hankali, domin Chelsea ba za ta so ta shiga kakar wasa da ƴanwasan da ba sa farin ciki ba saboda rashin samun damar buga wasa.

Savage Dan, magoyin bayan Chelsea:

"Chelsea ya kamata ta fi mayar da hankali kan ƴanwasan da za su bar ƙungiyar fiye da waɗanda za ta saya.

"Da yake ba ma cikin gasar Turai a wannan kakar, yana da muhimmanci ka da mu riƙe ƴanwasa da yawa sosai, domin ba za mu samu damar yin sauye-sauye da yawa a wasanni ba.

"Idan har za mu ɗauko wani ɗanwasa, ina ganin fifiko ya kamata ya kasance kan mai tsaron gida mai matukar inganci."

Fulham

Kocin Fulham, Alvaro Arbeloa, ya bayyana a fili cewa yana farin ciki da kasuwancin da ƙungiyar ta yi zuwa yanzu, amma har yanzu akwai damar ƙara inganta tawagar domin ta samu daidaito sosai.

An yi ƙoƙarin sayen wani ƙarin mai tsaron baya na tsakiya, inda aka tattauna yiwuwar ɗaukar Abdelhamid Ait Boudlal na Rennes makonni biyu da suka gabata. Wannan na iya kasancewa ɗaya daga cikin manyan wuraren da Fulham za ta ƙara ƙarfafawa.

Fulham ba ta daga cikin ƙungiyoyin da ke kashe kuɗi masu yawa a kasuwar musayar 'yan wasa, kuma ta shahara wajen kammala ciniki a ranar ƙarshe ta kasuwa.

John Charles, masoyin Fulham

"Har yanzu ina ganin Fulham na buƙatar ɗan wasan gefe na dama. Ko dai a ci gaba da dogaro da Oscar Bobb ko kuma a kawo wanda zai yi gasa da shi sosai, ina ganin dole ne mu nemo mafita bayan rasa yawan ƙwallayen da Harry Wilson ya sa ba bayarwa a baya.

"Haka kuma muna buƙatar mai tsaron baya na tsakiya daga gefen dama, saboda akwai damuwa sosai kan yadda Joachim Andersen zai dace da sabon tsarin wasan Arbeloa."

Liverpool

Kamar yadda ya kasance a mafi yawan lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta wannan bazarar, abin da Liverpool ta fi mayar da hankali a kai shi ne karfafa bangarorin gefe da gefe da ke taimakawa a kai hari, kuma ana sa ran a kalla za ta sayo dan wasan gefe guda, ko ma biyu, cikin mako mai zuwa.

Kocin Liverpool Andoni Iraola ya ce matsalar ba ta ta'allaka ne kan 'yan wasan tsakiya masu aikin kare baya ba, amma yadda kungiyarsa ta bari aka ci ta kwallaye biyu a wasanta da Newcastle ya nuna cewa zai dace a magance raunin da Liverpool ke da shi a wannan bangare.

Nahyan Chowdhury, magoyin bayan Liverpool:

"Ba boyayyen sirri ba ne cewa Liverpool tana ta neman 'yan wasan gefe a kasuwa, ciki har da Bradley Barcola, Ibrahim Mbaye da Yankuba Minteh. Wasan da suka yi da Newcastle ranar Lahadi ya kara tabbatar da hakan, musamman ganin yadda Rio Ngumoha ya yi fama a bangaren dama.

"Duk da haka, wasan ya kuma nuna cewa Liverpool na iya bukatar dan wasan tsakiya mai aikin kare baya domin cike babban gibin da ke tsakanin masu tsaron baya da 'yan tsakiya, musamman idan ana kai hare-haren gaggawa.

"Magoya bayan Liverpool sun dade suna neman wanda zai maye gurbin Fabinho tun bayan tafiyarsa, amma watakila lokaci ya kure saboda saura mako guda kacal kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa."

Manchester City

Manchester City na iya kasancewa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da za su fi yin kasuwanci a kwanakin da suka rage kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

Bayan tafiyar Savinho da ta Omar Marmoush da Nico Gonzalez, za a samu gurabe a cikin tawagar da dole ne a cike su.

An riga an kammala ciniki da Lille kan ɗaukar Ayyoub Bouaddi, haka kuma da Palmeiras kan dan wasan gefe Allan. BBC Sport ta kuma samu bayanin cewa har yanzu City na sha'awar ɗan wasan gefe Pedro Neto, yayin da raɗe-raɗin ɗaukar abokin wasansa na Chelsea, Enzo Fernandez, ke ci gaba.

Daraktan ƙwallon kafa Hugo Viana na iya samun aiki mai yawa a gabansa cikin kwanaki masu zuwa.

Steven McInerney, magoyin bayan Manchester City:

"City na buƙatar ƙarin 'yan wasa. Mun bar 'yan wasa da dama su tafi, kuma Omar Marmoush da Nico Gonzalez sun bi sahun Rodri da Savinho tare da wasu da dama wajen barin ƙungiyar a wannan bazarar.

"Yana da matuƙar muhimmanci City ta ɗauko sabbin 'yan wasa uku ko huɗu kafin wa'adin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, kuma biyu daga cikinsu ya kamata su kasance 'yan wasan tsakiya."

Manchester United

Bayan kammala ɗaukar Carlos Baleba a Manchester United, ƙungiyar ta gama gyara tsakiyarta, kuma yanzu hankula sun karkata ne kan ɗan wasa mai tsaron baya na ɓangaren hagu da kuma ko za a kawo wani dan wasa da zai yi gogayya da Luke Shaw.

Kungiyar ta daɗe tana sha'awar ɗan wasan Newcastle, Lewis Hall, amma kuma tana nazarin yiwuwar ɗaukar Alejandro Balde na Barcelona. Haka kuma ana alaƙanta ta sosai da Jorge Salinas na Racing Santander.

Haka kuma akwai yiwuwar a sayo wani ɗan wasan gaba, amma hakan na iya dogara da ko wani daga cikin 'yan wasan gaba na yanzu zai bar ƙungiyar, inda Joshua Zirkzee ya fi zama wanda za a iya sayarwa.

Jay Motty, magoyin bayan Manchester United:

"Dan baya na hagu yana da matuƙar muhimmanci. Wannan ba wai martani ne kawai ga rashin nasarar da aka yi a hannun Hull City ba, domin a bayyane yake cewa United na da ƙaranci a wannan wannu.

"Ba zai yiwu mu sa ran Luke Shaw zai buga kowane wasa a wannan kakar ba, kuma har yanzu akwai shakku kan ko Michael Carrick yana da cikakken yaƙini da Patrick Dorgu a bangaren tsaro."