Me ya faru da makusantan Buhari shekara ɗaya bayan rasuwarsa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shekara ɗaya bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, abokan tafiyarsa a lokacin da yake raye sun shirya wani gagarumin taron tunawa da shi a Abuja babban birnin ƙasar.

Buhari na daga cikin ƴan siyasa ƙalilan waɗanda suke da tarin mabiya da masoya a lokacin rayuwarsa, lamarin da ya sanya ya riƙa samun ɗimbin ƙuri'u a duk lokacin da ya yi takara, tun yana faɗuwa, har zuwa lokacin da ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

A ranar 13 ga watan Yulin 2025 ne tsohon shugaban ƙasar ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan, shekara biyu bayan sauka daga mulki.

Bayan rasuwarsa, ya bar babban giɓi, inda aka riƙa tababar ko za a samu wani da zai gaji farin jininsa da aƙidar siyasar irin tasa a nan kusa.

Masana siyasa kamar Kabir Sufi sun ce halin da muƙarraban Muhammadu Buhari suka samu kansu a ciki ya samo asali ne tun kafin saukar gwamnatin marigayin.

"Tun gabanin rasuwar tsohon shugaban ƙasar, a siyasance an samu rarrabuwar kai tsakanin wasu daga cikin manyan na hannun damansa," in ji Sufi.

Yayin da wasu suka ci gaba da biyayya ga gwamnatin magajinsa Bola Tinubu, wasu sun yi hannun riga da ita, har ma suka riƙa jayayya da kuma adawa da ita. Sai dai a lokacin Buhari bai taɓa fitowa fili ya nuna ɓangaren da ya fi rinjaya ba.

Yaya muƙarraban Muhammadu Buhari suka rarrabe?

Waɗanda suka ja daga da gwamnatin Tinubu

Mutane irin su tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon ministan shari'a Abubakar Malami da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi duk sun barrance wa gwamnatin Tinubu har ma suka sha alwashi ƙalubalantar ta, tun lokacin Muhammadu Buhari na da rai.

Haka lamarin ya ci gaba ko bayan rasuwar tasa.

Waɗannan na daga cikin waɗanda suka tsinci kansu cikin komar hukumomin bincike kan zargin aikata badaƙala.

Gabanin haka Abubakar Malami ya kasance cikin jagororin yin haɗakar ƴan hamayya ƙarƙashin jam'iyyar ADC, waɗanda suka sha alwashin ƙalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu a zaɓen ƙasar na 2027.

-Nasir El-Rufai: A watan Fabarairun 2026 ne hukumomin bincike irin su EFCC da ICPC har da da hukumar tsaro ta farin kaya suka ƙaddamar da bincike da tuhume-tuhume a kotu kan tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Shi ma yana ɗaya daga cikin ginshiƙan jam'iyyar haɗakar ƴan hamayya ta ADC, kuma ya kasance ɗaya daga cikin wadanda suka fi sukar gwamnatin Bola Tinubu.

Daga cikin tuhume-tuhumen da aka masa a kotu akwai karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa'ida, da mallakar kadarorin jama'a ba bisa ƙa'ida ba, da halasta kuɗaɗen haram sai kuma wata tuhumar kan zargin shi da satar sauraron wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.

Akwai kuma wasu daga cikin na kusa da marigayi Muhammadu Buhari waɗanda suka raba gari da gwamnatin shugaba Tinubu mai ci, amma ba su shiga hannun hukumomin bincike ba. Irin wadannan sun haɗa da:

  • Rauf Aregbesola
  • Rotimi Amaechi

Waɗanda aka zarga da almundahana

Wannan sun ƙunshi mutanen da suka faɗa komar hukumomin bincike na Najeriya, mafi yawansu bisa laifin almundahana.

Hukumar ta zarge shi da yin amfani da ofishinsa wajen yi wa 'yarsa Fatima da mijinta Jalal Hamma alfarmomi ta hanyar ba su aikin bayar da shawarwari a Nigeria Air, da kuma ba su kwangilar gina wani ɓangare na filin jirgi a Katsina.

Kotu ta ce ta samu Saleh da aikata laifuka 12 da hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa - EFCC - ta tuhume shi da su masu alaƙa da haɗa baki da almundahana.

-Sadiya Faruk: A cikin watan Mayun 2026 ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohuwar ministar jinƙai ta Najeriya, lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar ne bisa zarge-zarge masu alaƙa da almundahanar kuɗaɗe.

Waɗanda suka koma gefe

Akwai kuma wasu na hannun Muhammadu Buhari waɗanda suka koma gefe ba tare da ana jin ɗuriyarsu ba, irin waɗannan sun haɗa da:

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo
  • Tsohon ministan ayyuka, makamashi da gidaje Babatunde Fashola
  • Tsohon gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura
  • Tsohon ministan yaɗa labarai Lai Mohammed
  • Sule Yahaya Hamma

Ko akwai masu ɗasawa da gwamnatin Tinubu?

Kusan za a iya cewa da wuya ka ga manyan muƙarraban marigayi Muhammadu Buhari a cikin gwamnatin Bola Tinubu.

Hakan kuwa ya samo asali tun lokacin da tsohon shugaban ƙasan ke da rai.

Sai dai akwai waɗanda sun ɗasa a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari kuma suna damawa a wannan gwamnati ta Bola Tinubu, kamar:

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, kuma sanata mai ci a yanzu
  • Festus Keyamo, ya yi ƙaramin ministan ƙwadago a gwamnatin Buhari, yanzu kuma shi ne ministan sufurin jiragen sama

Me ya sa aƙidar Buhari ta gushe bayan rasuwarsa?

Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa a Najeriya ya ce: "Duk da Muhammadu Buhari na da ɗimbin mabiya da magoya baya, siyasarsa ba ta kafa wasu gungu ba ne ko kuma wata tafiya wadda za ta ci gaba ko da ba ya nan ba".

Ya ƙara da cewa rarrabuwar mabiyansa ta samo asali ne tun yana raye: "an yi ta zargin ko da a jam'iyyarsa ta APC ya bar kowa ne ya ya yi abin da ya ga dama.

"Shi bai yadda a kan cewa akwai wata siyasa ta gidan Buhari ko sai an yi wata tafiya ta Buhari ba," in ji Kari.

"Babu wani abu da za a ce ita ce aƙida ta zaihiri ta Buhari wadda za a ce za a ci gaba da bin ta.

"Ba kamar irin aƙidar su Malam Aminu Kano ko Awolowo ba, waɗanda za a iya cewa ga ƴan gani-kashe-ninsu.

Dama abin aka san shi a kai shi ne, shi mai gaskiya ne, mai son a yi abu daidai ne, to amma ko a lokacin rayuwarsa bai kafa wannan aƙidar ba, bai dage a kan cewa sai ta ci gaba bayan rayuwarsa ba".

Kari ya ce shi ya sa bayan shuɗewar Buhari sai aƙidarsa ta kau.