Nawa ne dukiyar Elon Musk kuma me zai iya saya da ita?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mai kamfanin SpeaceX da Tesla Elon Musk ya kama hanyar ajiye babban tarihi na zama mutum na farko da zai mallaka dukiyar da ta kai dala tiriliyan ɗaya.

A yanzu haka, Musk yana da hannun jarin da ya kai dala biliyan 273 a kamfanin Tesla kaɗai.

Idan kuma darajar kamfaninsa na SpaceX ya ci gaba da ƙaruwa kamar yadda masu zuba jari suka yi hasashe, arzikinsa zai iya ƙaruwa zuwa ɗaruruwan biliyoyin dala.

Kamar yadda wasu masana suka yi ƙiyasi, darajar Tesla da SpaceX zai iya zarta dala tiriliyan 1.1

Wannan tarin dukiyar babu mutum guda wanda ya taɓa mallakarta a tarihin duniya. To amma yaya tarin dukiyar da ta kai tiriliyan ɗaya take?

Idan muna san gane yawan adadin dukiyar, sai mun daina kallon alƙaluman mu ɗora ta a kan yadda masu ƙaramin ƙarfi za su amfana, ko kuma kasafin kuɗin gwamnati da kuma tattalin arzikin wasu ƙasashe.

Me dala tiriliyan ɗaya za ta iya yi?

Adadin na da tarin yawa ta yadda mutane da dama ba za su iya ƙimanta yawan kuɗin ba sai dai a yi ta hasashe.

Dala tiriliyan ɗaya ita ce dala biliyan dubu. Idan mutum zai riƙa kashe dala miliyan ɗaya a kowace rana, zai kai shekara 2,700 kafin ya kashe dala tiriliyan ɗaya.

Wani misalin kuma shi ne idan aka ce za a raba kuɗin ga duk mutanen da ke duniya.

Yawan al'ummar duniya a yanzu kamar yadda aka yi ƙiyasi ya kai biliyan 8.3.

Idan Elon Musk zai raba tiriliyan 1.1 ga kowane mutum - maza, mata da yara - a duniya, kowa zai iya samun aƙalla dala 133 ko kuma Naira 181,000.

Idan akwai mutum biya a gida ɗaya, za su samu aƙalla Naira 905,000 jimilla. Ko da yake idan aka ce kowane mutum zai iya kashe aƙala Naira 200,000 a kullum, kuɗin ba zai kai ba.

Amma duk da haka, wannan tulin dukiyar ta dala tiriliyan 1.1 ba ƙaramin arziki ba ne idan aka kwatanta da kasafin kuɗin ƙasashe da kuma tattalin arzikinsu.

Kasafin ƙudin Ivory Coast, Senegal, Burkina Faso da Mali na kusan shekaru 20

Kasafin kuɗin Ivory Coast mai ƙarfin tattalin arziki a yankin yammacin Afrika, ya kai Sefa biliyan 17,320.2 a 2026, kimanin dalar Amurka biliyan 30.6.

Wannan na nuna cewa dukiyar Elon Musk ta tiriliyan 1.1 za ta iya biyan kasafin kuɗin Ivory Coast na kusan shekaru 35 a yanayin da ake ciki.

Senegal kuwa wadda ita ce ƙasa ta biyu mafi tattalin arziki a yammacin Afrika, kasafin kuɗinta na 2026 ya kai dala biyan 13.1.

Kasafin kuɗin Burkina Faso da Mali na shekarar 2026 ya kai kusan dala biliyan 6 da dala biliyan 5.4 kowannesu.

Idan aka haɗa kasafin kuɗin ƙasashen huɗu (Ivory Coast, Senegal, Mali da Burkina Faso) zai kai kimanin dala biliyan 55.1

Idan za a yi amfani da dukiyar Elon Musk ta dala tiriliyan 1.1, zai iya biyan kasafin kuɗinsu sama da tsawon shekaru 19.

Wannan dukiyar za ta iya biyan kasafin kuɗin fannin ilimi, lafiya, tsaro da albashin ma'aikatan ƙasashen huɗu na kusan shekaru 20, waɗanda mutanensu ba su wuce miliyan 100 ba a 2025.

Ƙasashe 20 kaɗai ke da tattalin arzikin da ya kai dukiyar Musk

Wasu alƙaluma da Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF ya fitar, ya ce ƙasashe kaɗan ne a duniya suka mallaki dukiyar da ta kai dala tiriliyan 1.1.

Daga cikin ƙasashe 195 a duniya, 20 ne kawai tattalin arzikinsu ya zarta dala tiriliyan 1.1, inda yawancinsu ba su da duniyar da ta kai ta Musk.

Alal misali, ƙasashe irinsu Taiwan na da $977bn, Ireland ($779bn) Sweden ($760bn) da Singapore ($660bn).

Dukiyar ta Musk ya tara ta fi tattalin arzikin shekara guda na ƙasashe da dama a duniya.

Duk ƙasashen Afrika, babu wadda ke da tattalin arzikin da ya kai dala tiriliyan ɗaya.

Har ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a nahiyar irinsu Afrika ta Kudu, Masar, Aljeriya, Najeriya, Kenya da Ethiopia ba su mallaki wannan adadin ba.

Afrika ta Kudu na da ƙarfin tattalin arziki da ya kai dala biliyan 480, abin da Musk ke da ninkinsa.

Mutum ɗaya kenan da ya mallaki arzikin da ya zarta abin da yawancin ƙasashen Afrika ke samu a shekera guda.

Sau nawa zai iya sayen Abidjan da Dakar?

Babu wasu alƙaluma game da darajar gine-ginen da ke cikin birnin Dakar da Abidjan. Sai dai idan aka yi ƙiyasin, darajar gine-ginen ƙasashen Afrika zai kai dubban biliyoyin dala ba ma ɗaruruwa ba.

Amma idan aka lissafa ma, ba lallai darajar gine-gine da ke biranen Abidjan da Dakar da Ouagadougou da Bamako su kai dala tiriliyan ɗaya ba.

Amma wannan dukiyar a takarda ce kawai

Duk da maganar wannan tarin dukiyar da ake magana, babu wanda ya taɓa rike tsabar kuɗin a zahiri ko ganinsu a banki ko kuma a wani wuri a Amurka.

Yawancin dukiyar Elon Musk ana auna darajarsu ne daga hannun jarin da ya mallaka a kamfanoni daban-daban.

Idan da a ce darajar waɗannan hannayen jari na kamfanonin za su karye a kasuwar hannun jari, shi ma zai samu raguwar tattalin arziki.