Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na 16/04/2026.

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Amurka ta fitar da bayanan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon

    Wani bayani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya bayyana cikakkun bayanai kan yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki goma tsakanin Isra’ila da Lebanon da za a fara da karfe 5 na yamma agogon ƙasar a yau.

    Amurka ta ce, bayan da ɓangarorin biyu suka gana a zahiri don tattaunawa a birnin Washington a wannan makon, "sun tabbatar da cewa ƙasashen biyu ba su yaƙi da juna, kuma suna da ƙudurin shiga tattaunawa ta gaskiya ta gaskiya, da Amurka ke jagoranta".

    Ga wasu muhimman bayanai guda 6 daga ciki:

    • Gwamnatin Isra'ila ta bayyana matakin tsagaita wutan a matsayin "abin fatan alheri"
    • Za kuma a iya "faɗaɗa yarjejeniyar idan an fahimci juna" a yayin tattaunawar
    • Duk da tsagaita wutar, Amurka ta sake nanata ƴancin Isra’ila na “ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare kai, a kowane lokaci, kan hare-haren da ake shirin kai mata ko ake kaiwa"
    • Da zarar an fara tsagaita buɗe wuta, gwamnatin Lebanon "za ta ɗauki matakan da suka dace don taka wa Hezbollah burki, da sauran masu tada ƙayar baya masu ɗauke da makamai" a cikin ƙasarta.
    • Ƙasashen sun amince da " alhakin Lebanon da ƴancinta na tabbatar da tsaron ƙasar"
    • Isra'ila da Lebanon sun buƙaci Amurka da ta ci gaba da shiga tsakanin kasashen biyu a tattaunawar da ake yi, da nufin warware duk wasu batutuwan da suka rage
  2. Ana samun nasara wajen yaƙi da matsalar tsaro a Sokoto - Ahmed

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ce ana samun nasara a yaƙin da ake yi da rashin tsaro a jihar sanadiyyar sabon ƙoƙarin da ake yi wajen kawar da matsalar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Alhamis sa'ilin buɗe taron majalisar zartarwar jihar.

    Aliyu ya ce "ina sanar da ku cewa sabon ƙoƙarin da muka fara yi na haifar da ci gaba, a yunƙurin da muke yi na kawar da ayyukan ƴan fashin daji da ke addabar ƙananan hukumomi 13".

    Gwaman ya ce ana kuma samun ci gaba a yaƙin da ake yi da sauran masu aikata laifuka a jihar.

    Sokoto na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji.

    Duk da iƙirarin da gwamnatoci ke yi, har yanzu abin ya ci tura, inda ƴan bindigar suka tarwatsa ƙauyuka da dama a jihar da ma wasu jihohin masu maƙwaftaka.

    A cikin bayanin nasa, Ahmed Aliyu ya ce gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta "mayar da duk ƴan gudun hijira zuwa ƙauyukansu na asali".

  3. Trump ya yi watsi da kalaman Fafaroma Leo

    Yayin da taƙaddama ke ci gaba tsami tsakaninsa da fadar Vatican kan yakin Gabas ta Tsakiya, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da kalaman Fafaroma Leo, wanda ya ce duniya na fuskantar barazana daga azzalumai.

    Trump ya ce yana da ƴancin saɓanin ra'ayi da Fafaroman, tare da zargin cewa Iran na iya mallakar makaman nukiliya, zargin da ake akallo a matsayin mai cike da shakku.

    Da yake jawabi ga mabiya addinin Katolika a wani yanki na Kamaru da rikici ya ɗaiɗaita, Fafaroman ya sake kira da a samar da zaman lafiya, yana mai cewa wasu shugabanni na amfani da sunan Allah, domin biyan buƙatunsu na ƙashin kai.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne, Shugaba Trump ya zargi Fafaroman da cewa, ba shi da kwarewa kan manufofin ƙasashen waje.

  4. Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya nan da fiye da shekaru 20.

    Da yake magana da manema labarai a wajen fadar White House, Trump ya ce Amurka da Iran na daf da ƙulla yarjejeniya, inda Tehran ta amince da kusan dukkanin buƙatun Amurka.

    Ya kara da cewa Iran a shirye take ta yi abubuwan ba su yi yiwu a baya ba.

    "Komai na tafiya yadda ya kamata, za mu kulla yarjejeniya da Iran kuma za ta kasance mai ma'ana, yarjejeniya ce da babu maganar makaman nukiliya ba..."

    "Mun samu bayani mai gamsarwar cewa, ko nan da shekaru 20, ba za su mallaki makaman nukiliya ba," in ji shi.

    Sai dai babu wani bayani daga ɓangaren Iran.

  5. Isra'ila ba ta da niyyar janye dakarunta a Lebanon - Majiyoyi

    Majalisar ministocin tsaron Isra'ila na wani taron gaggawa da Firaminista Benjamin Netanyahu ya kira.

    Wasu rahotanni sun ce cikin minti biyar aka kira taron kuma har yanzu ba samu wani tabbaci daga ɓangaren Isra'ila dangane da sanarwar tsagaita wutar ba.

    A halin da ake ciki kuma, majiyoyin sojan Isra'ila sun ce ba su da niyyar kwashe dubban sojojinsu daga kudancin Lebanon a lokacin tsagaita bude wuta na kwanaki 10.

  6. Hezbollah ta buƙaci a hana dakarun Isra'ila mamayar Lebanon idan ana son tsagaita wuta

    Hezbollah ta ce dole ne a "dakatar da kai hare-hare a duk faɗin Lebanon" da "haramta wa dakarun Isra'ila mamaya" a ƙasar.

    Ta kuma ta bukaci "dawo da komai yadda yake kafin ranar 2 ga Maris", a ranar da Hezbollah ta harba rokoki da jirage marasa matuƙa cikin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa jagoran juyin juya halin Iran, wanda ya sa Isra'ila ta mayar da martani da hare-hare a duk faɗin ƙasar.

    Ta kara da cewa: Ci gaba da mamayar da Isra'ila ke yi a ƙasar Lebanon ya ba Lebanon da al'ummarta 'yancin yin turjiya.

  7. Firaministan Lebanon ya yi maraba da sanarwar tsagaita wuta

    Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya ce yana maraba da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta na wucin gadi da Isra'ila, wadda ya ce dama abin da Lebanon ke buƙata tun bayan ɓarkewar yaƙin.

    Ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta baiwa waɗanda rikicin ya shafa damar komawa gidajensu.

    Salam ya kuma yaba da ƙoƙarin ƙasashen duniya na cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta.

  8. Trump ya gayyaci Netanyahu da shugaban Lebanon Fadar White House

    Shugaban Amurka Trump ya ce ya gayyaci firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Lebanon Joseph Aoun zuwa fadar White House domin ci gaba da tattaunawa.

    Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta na kwanaki 10 tsakanin kasashen biyu, inda ya ce za ta fara aiki da karfe 5 na yamma agogon ƙasar.

    "Dukan ɓangarorin biyu suna son ganin an samu zaman lafiya, kuma na yi imanin hakan zai faru, da sauri!" Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social

    Sai dai ba a bayyana ko sun amsa gayyatar ba.

  9. Shugaban Lebanon ya gode wa Trump bisa 'ƙoƙarin' ganin an tsagaita wuta

    Ofishin shugaban ƙasar Lebanon Joseph Aoun ya tabbatar da cewa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Amurka Donald Trump a yau Alhamis.

    A cikin wani saƙo da aka wallafa a shafin X, ofishin ya ce Aoun ya gode wa Trump saboda ƙoƙarin da ya yi na cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Lebanon da kuma "wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali".

    Aoun ya jaddada cewa yana son ganin an tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah "nan kusa".

    Bayanin ya ƙara da cewa Trump zai ba shugaba Aoun da Lebanon goyon bayan da ya dace

  10. Firaministan Pakistan ya isa Doha domin ci gaba da ziyarar diflomasiyya kan yaƙin Iran

    Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, wanda ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, ya isa Doha a ranar Alhamis bayan ziyararsa Saudiyya, inda ya gana da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.

    Fadar Firaministan Pakistan ta ce Sarkin Qatar ya yaba da rawar da Pakistan ke takawa, inda suka nuna goyon baya ga ƙoƙarin rage tashin hankali da ƙarfafa haɗin kai na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin, musamman wajen tabbatar da hanyoyin samar da makamashi ba tare da tangarda ba.

    Ziyarar Sharif zuwa Saudiyya da Qatar ta zo ne kwanaki huɗu bayan tattaunawa tsakanin manyan jami’an Amurka da Iran a Islamabad.

    Ana sa ran Sharif zai wuce Turkiyya a gaba.

    Tattaunawar da aka yi a Pakistan ba ta kai ga cimma yarjejeniya ta dindindin ba don kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa an samu tsagaita wuta na kusan kwanaki goma tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila.

  11. Trump ya ce Isra'ila da Lebanon sun amince da tsagaita buɗe wuta na kwanaki 10

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Lebanon da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta na kwanaki 10 da zai fara aiki da karfe 5:00 agogon ƙasar.

    A cikin wani sakon da ya wallafa na bayyana yarjejeniyar tsagaita bude wuta, Trump ya ce ya tattauna da shugaban Lebanon Joseph Aoun da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    Sai dai babu dai wani ƙarin bayani a cikin bayanin nasa game da ƙungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran a Labanon, wadda Isra'ila ke ta musayar wuta da ita.

    Trump ya ce: “Na tattauna da Shugaban Kasar Lebanon Joseph Aoun cikin girmamawa, da Firaminista Bibi Netanyahu na Isra’ila.

    “Shugabannin biyu sun amince cewa domin a samu zaman lafiya a tsakanin kasashensu, za su fara tsagaita wuta na kwanaki 10 a hukumance da karfe 5 na yamma," in ji Trump.

  12. Kotu ta ba EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Faruoq

    Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta'annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq.

    EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma'aikatar da ake zargin an wawure.

    A wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari'a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma'aikatar Bashir Nura Alkali.

    Ta ce matakin ya biyo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.

    Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya da hana Sadiya halartar kotun, amma kuma ba a amince da buƙatar tasu ba.

    EFCC ta ce ta shigar da ƙarar ce tun a ranar 15 ga watan Disambar 2025, amma ba a samu damar yin ido biyu da waɗanda ake zargin domin miƙa musu takaradar kotun ba.

    Sadiya ta riƙe muƙamin ministar ne a mulkin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda daga baya ta auri tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya AVM Sadiq Abubakar.

  13. Isra'ila ta kai munanan hare-hare a kudancin Lebanon

    An saki wasu sabbin hotuna da ke nuna yadda Isra'ila ta kai munanan hare-hare a kudancin Lebanon.

    Hotunan farko guda biyu da aka ɗauka sun nuna bayan wani hari da aka kai a birnin Nabatieh, wani birni mai mutane kusan 40,000 a arewacin kogin Litani, kuma ya nuna hayaki na tashi sama.

    Hoto na uku ya nuna yadda mutane a Qasimieh da ke kusa da gaɓar tekun Mediterrenean na duba irin ɓarnar da harin ya haifar, wanda wani babban jami'in tsaron kasar ya ce ya lalata gadar ƙarshe da ta haɗa kudancin Lebanon da sauran sassan ƙasar.

  14. Tsagaita wuta a Lebanon na da muhimmanci kamar na ƙasarmu - Iran

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya jaddada cewa a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Lebanon, Nabih Berri tsagaita wuta a Lebanon na da muhimmanci iri ɗaya da na Iran.

    Qalibaf, wanda ya jagoranci tawagar Iran a tattaunawar kai tsaye da Amurka a Islamabad, ya ce Iran na ƙoƙarin ganin an tilasta wa ɓangarorin da ke rikici su amince da tsagaita wuta na dindindin.

    Ya kuma ce Iran ba ta manta da ‘yan uwanta na Lebanon ba, kuma tana sa ido a kai a kai kan halin da ake ciki a ƙasar da kuma ƙoƙarin samar da tsagaita wuta, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci a gare su.

    Nabih Berri, wanda ake ganin na kusa da ƙungiyar Hezbollah ne, ya yaba da ƙoƙarin Iran, yana mai cewa bai ga wata hulɗa kai tsaye da Isra’ila a matsayin abin da ya dace da muradun al’ummar Lebanon ba.

  15. Isra'ila ta yi barazanar kai wa Iran hare-hare masu zafi

    Ministan tsaron Isra'ila, Isra'ila Katz, ya yi gargaɗin cewa kasarsa za ta ƙaddamar da hare-hare masu zafi a kan Iran matuƙar ba ta amince da yarjejeniya da Amurka ba.

    "Iran na tsaka mai wuya. Wannan ne lokacin da ya kamata su ɗauki matsaya - tsakanin makomarsu ko kuma keɓewa cikin halaka," in ji shi.

    Ya ce idan Iran ba ta yi abin da ya kamata ba, Isra'ila za ta ƙaddamar da munanan hare-hare a inda ta yi niyya tun da farko fiye da waɗanda suka gani a baya.

    Ya ƙara da cewa: "Zaɓi ya rage nasu, kuma su za su ji a jikinsu."

  16. Abubuwan da taron manema labaran sojojin Amurka kan yaƙin Iran ya ƙunsa

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, tare da shugaban hafsoshin soji Janar Dan Keene da kwamandan CENTCOM, Admiral Brad Cooper, sun yi taron manema labarai a Pentagon kan yaƙin Iran.

    Ba a bayyana sabbin muhimman bayanai ba, amma sun mayar da hankali kan gargadi da nuna shirye-shiryen soja. amma ga wasu abubuwa da suka tattauna a taron

    • Hegseth ya ce Iran na da “ƙwarin gwiwa mai yawa” na amincewa da tsagaita wuta
    • Rundunar CENTCOM ta ce sojojin Amurka na sabunta dabarunsu da hanyoyin aikinsu
    • Hegseth ya sake kira ga gwamnatin Iran da ta zaɓi hanya ta gaba cikin hikima
    • Janar Keene ya ce duk wani jirgi da ya yi ƙoƙarin kauce wa toshewar mashigar Hormuz da aka yi, za a ɗauki mataki a kansa yadda ya dace
    • Janar Keene ya kuma ce Amurka a shirye take ta koma yaƙi a kowane lokaci
    • Hegseth ya kara da cewa kasa da kashi 10 cikin 100 na ƙarfin rundunar ruwan Amurka aka yi amfani da shi wajen toshe mashigar Hormuz
    • Hegseth ya ce Iran ba za ta iya maye gurbin ƙarfin sojinta da ta rasa ba
  17. Fafaroma Leo ya soki "azzaluman" da ke kashe biliyoyin kuɗi a yaƙe-yaƙe

    Fafaroma Leo ya soki shugabannin da suke kashe biliyoyin kuɗi a yaƙe-yaƙe a wani kalami na rashin tsoro a Kamaru. Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi masa kakkausan suka a karo na biyu a shafinsa na soshiyal midiya.

    Da yake magana a Bamenda Kamaru, Fafaroman na farko ɗan Amurka ya yi alawadai da "masu amfani da addinin da sunan ubangiji a harkokin soji da tattalin arziƙi da kuma neman cin nasara a siyasa," inda ya yi gargaɗin amfani da addini wajen samun hujjar haifar da rikici.

    "...duniya na fama da wasu tsirarun azzalumai,"

    Fafaroma Leo ya kuma bayyana irin kuɗaɗen da ake kashewa a fannin yaƙi inda ya soki abin da ya bayyana da rashin daidaito a duniya a fannin abin da ya dace.

  18. Ƴan daba sun addabi jihar Diffa a jamhuriyar Nijar

    A jihar Diffa a jamhuriyar Nijar, al'ummomi na kokawa kan yawaitar ayyukan faɗan daba da ƙwacen waya ta hanyar amfani da miyagun makamai.

    Hukumomi sun ɗora laifukan a kan mutanen da suka bayyana da baƙi duk da dai wasu ƴan ƙasar su ma na da hannu a cikin miyagun lafiukan.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da suka haɗa da Boko Haram da sauransu ke zafafa hare-hare da ke haddasa salwantar rayukan jami’an tsaro da na fararen hula.

  19. China ta ce tattalin arziƙinta ya samu bunƙasa a 2026

    Alkaluman hukuma daga China na nun acewa tattalin arzikin ƙasar ya karu a shekara da kashi biyar cikin ɗari a rubu'in farko na wannan shekara.

    Fitar da kaya waje da ƙirar kayayyaki na fasaha da kuma tallafin gwamnati ne suka janyo hakan.

    To amma kuma burunƙasar cinikin ɗaiɗaikuwa na jama, ba ta kasance ba yadda aka yi tsammani.

    Ana sa ran tattalin arziƙin na China zai gamu da dan tazgaro a sakamakon tsadar farashin makamashi da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haddasa

  20. Burkina Faso ta haramta wa kungiyoyi fararen hula fiye da 100 aiki a ƙasar

    Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta rushe kungiyoyin sa-kai fiye da guda 100 waɗanda da dama daga cikin su ke da alaƙa da fafutukar neman ƴancin dan adam.

    Ana dai yi wa al'amarin kallon wani yunƙuri na daƙile ƴancin al'umma a ƙasar.

    Ma'aikatar kula da iyakokin ƙasar wadda ta sanar da matakin ta ce an rufe ƙungiyoyin ne sakamakon gazawarsu wajen bin dokokin ƙungiya da ƙasar ta tsara, inda aiwatar da hanin nan take ga duk wata ƙungiya a ko'ina afaɗin ƙasar.

    Gwamnatin ta kuma ta ce hakan zai ba wa kasar damar daƙile safarar haramtattun kuɗi da tallafawa ƴan ta'adda da kuɗade.