Isra'ila ta ce ta lalata rumbunan ajiyar makaman Hamas uku a Gaza
Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-hare tare da lalata rumbunan ajiyar makaman Hamas a tsakiyar Gaza cikin sa'a 24.
A cewar Isra'ilar, waɗannan rumbunan na ɗauke da tankokin harba makaman linzami da makamai masu cin dogon zango da RPG da sauran makamai.
Cikin wata sanarwa da sojojin Isra'ila suka fitar sun ce za su ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da za su ci gaba da kawar da duk wani abu da suka kira barazana.