Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 23 Agusta

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni ne daga sassan duniya, kasuwar musayar 'yan wasa da kuma manyan sauye-sauyen da ke faruwa a fagen

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. An ci tarar Messi bayan marin danwasa

    An ci tarar danwasa Lionel Mesai na kungiyar Inter Miami bayan ya mari danwasan kungiyar Philadelphia Union, Quinn Sullivan yayin karawa tsakanin kungiyoyin biyu a gasar Major League Soccer ta Amurka, inda kungiyoyin suka tashi canjaras 2-2 a ranar Laraba.

    Messi mai shekara 39 ya mari Sullivan ne a keya lokacin da aka kusa tashi daga wasa bayan ya koka kan cewa danwasan na Philadelphia Union ya tokare shi da gwiwar hannu a lokacin da ya buga wata kwallo.

    Sullivan ya fusata a lokacin da Messi ya mare shi a keya sai dai nan da nan lafari ya shiga tsakani.

    Hukumar kula da babbar gasar kungiyoyin Amurka ta MLS ta tabbatar da labarin cin tarar Messi sai dai ba ta fadi ko nawa ne aka ci shi tarar ba.

    A wasan, Messi ne ya ci kwallo ta biyu wa kungiyarsa, wanda hakan ke nufin ita ce kwallo ta farko da ya zura tun bayan rasuwar mahaifinsa.

    Ba Messi ne kadai danwasan da ya yi fada da Sullivan a karawar ba, kasancewar dan wasan Miami, Ian Fray shi ma an ci shi tara.

    Fray ya cacumi wuyan Sullivan bayan da suka yi wata arangama a lokacin wasan.

    Wasan wanda aka tashi shi dutse a hannun riga, ba a tashi ba sai da aka bai wa ‘yanwasa biyu katin kora.

    ‘Yan wasan da aka kora su ne Yannick Bright na kungiyar Inter Miami da kuma Cavan, dan’uwan Sullivan.

    Messi ya koma wasa ne bayan binne mahaifinsa, wanda kuma shi ne mai tafiyar da harkokin danwasan.

  2. United ta sha kashi a wasanta na farko a wannan kaka, Hull City 2 - 0 Manchester United

    An fara shan mamaki a gasar Premier 2026-27 a rana ta biyu, bayan da Hull City ta doke Manchester United da ci 2-0.

    Hull ta nuna ƙwarewa da ƙarfin gwiwa a wasan na ranar Asabar, wanda shi ne na farko bayan fitowa daga ralageshon, inda za a iya cewa ta samu nasara "cikin sauƙi".

    Yanzu ya rage wa kocin United Michael Carrick ya koma ya yi tunani, domin kuwa a wasan na farko masharhanta na ganin cewa ƴan wasan ƙungiyar ba su nuna cewa da gaske suke yi ba, tamkar waɗanda "basira ta ƙare musu".

    An jefa wa United ƙwallayen biyu ne tun kafin zuwa hutun lokaci, ta farko a minti na 17, ta biyu kuma a minti na 38.

    Sai dai har aka kammala wasan ƙungiyar ba ta iya farkewa ba.

    A ranar Juma'a ne aka yi wasan farko a sabuwar kakar, inda mai riƙe da kofi Arsenal ta samu nasara cikin sauƙi kan Coventy City da ci 3-0.

  3. 'Har yanzu ba mu gama sayen 'yan wasa ba'

    Kocin Manchester City, Roberto de Zerbi, ya ƙi yin magana kai tsaye kan rahotannin da ke alaƙanta Savinho da Omar Marmoush da komawa Tottenham Hotspur, yana mai cewa ba daidai ba ne a tattauna batun 'yan wasa kafin a kammala yarjejeniya a hukumance.

    "Ba daidai ba ne a yi magana game da 'yan wasa kafin a sanar da komai a hukumance. Abin da zan iya cewa kawai shi ne ina farin ciki sosai. Har yanzu ba mu gama kasuwar musayar 'yan wasa ba. Wannan wani muhimmin ɓangare ne."

    De Zerbi ya yabawa irin 'yan wasan da ƙungiyar ta ɗauka zuwa yanzu, yana mai cewa: "Zuwa yanzu, mun yi sayayya masu kyau, mun samu manyan 'yan wasa, kuma sun nuna halaye masu kyau, ƙwazo mai kyau da kuma ƙarfi na hali."

    Kocin ya kuma jaddada cewa samun fitattun sunaye kaɗai ba ya tabbatar da nasara a Premier League.

    "Kun fi ni sanin cewa a Premier League ba a lashe wasanni da sunaye ko manyan 'yan wasa kaɗai. Akwai misalai da yawa a shekarun baya."

    Ya ƙara da cewa: "Dole ne ku cancanci cin nasarar wasa. Domin mu cancanci lashe wasa, dole ne mu kai matakin da ya dace ta fuskar hali, niyya, ƙima da kuma salon wasanmu."

    Kalaman De Zerbi na nuna cewa, duk da muhimmancin sayen sababbin 'yan wasa, babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne gina ƙungiya mai haɗin kai, ƙwazo da kuma ingantaccen salon wasa da zai ba ta damar yin nasara a filin wasa.

  4. Watkins ka iya zama dan wasan Aston Villa na gaba da zai bar ƙungiyar

    Koci Unai Emery ya kasa bayar da tabbacin kan ko ɗan wasan gaban Ingila Oliie Watkins zai ci gaba da zama a ƙungiyar bayan rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

    Ya tabbatar da cewa ƙungiyar Al-Hilal ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan mai shekaru 30, amma ya amince cewa Watkins, wanda ya ci wa Aston Villa kwallaye 108, na iya bin sahun Morgan Rogers, Ezri Konsa, Youri Tielemans da Lucas Digne wajen barin ƙungiyar.

    Emery ya ce:"Muna da wani batu da ya shafi shi, kuma hakan a bayyane yake. Har yanzu ɗan wasanmu ne. Mun samu tayin sayensa."

    "Ba na so mu sayar da shi, amma hakan na iya canzawa idan yarjejeniyar za ta kasance alheri gare shi da kuma ƙungiyar, kuma idan zan iya samun wanda zai maye gurbinsa a cikin tawagar. Wannan shi ne tsarin da muke bi, kuma mun yi hakan a baya da ‘yan wasan da suka bar ƙungiyar."

    "Game da Ollie, yana nan tare da mu. A gare ni, shi ƙwararren ɗan wasan gaba ne, kuma a koyaushe mun yi imani da ƙwarewarsa."

    "A yanzu shi ɗan wasanmu ne. Akwai kusan kwanaki 10 kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa. Za mu ga abin da zai faru. Ina farin ciki da shi, kuma idan ya ci gaba da zama tare da mu, zai ci gaba da taka leda a matsayinsa na ƙwararren ɗan wasa."

  5. Me Maresca yake shirya wa Man City ne?

    Enzo Maresca na fuskantar manema labarai a karon farko kafin jagorantar Manchester City a wasan Premier League, kuma akwai batutuwa da dama da ke gabansa.

    Kocin ɗan asalin Italiya ya fara rayuwarsa a City cikin yanayi mai wahala bayan da ƙungiyarsa ta sha kashi da ci 3-0 a hannun gwarzuwar Premier League, Arsenal, a wasan Community Shield makon da ya gabata.

    Maresca bai samu isasshen lokaci ba wajen aiki tare da 'yan wasan da suka dawo a makare bayan kammala gasar Kofin Duniya, kuma ana sa ran kwanakin da suka rage kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa za su kasance masu cike da aiki a Etihad.

    Ana ganin Savinho da Omar Marmoush na dab da komawa Tottenham Hotspur, yayin da kuma ake ci gaba da tambayoyi kan makomar ɗan wasan tsakiya Nico Gonzalez.

    Hakan na nufin cewa akwai yiwuwar sabbin 'yan wasa su shigo ƙungiyar. A halin yanzu, City na dab da kammala cinikin ɗan wasan tsakiya na Morocco daga Lille, Ayyoub Bouaddi, sannan kuma tana nuna sha'awar Alex Scott na Bournemouth da Alexis Mac Allister na Liverpool.

    Tambayar ita ce: 'Yan wasa nawa ne za su bar ƙungiyar, kuma nawa za su zo?

    Za a jira a gani ko Maresca zai bayyana wani abu game da shirye-shiryen ƙungiyar a kasuwar musayar 'yan wasa yayin ganawarsa da manema labarai.

  6. Isak zai shiga Newcastle a karon farko bayan komawa Liverpool

    Kocin Liverpool, Andoni Iraola, ya kuma fuskanci tambayoyi game da tsohon ɗan wasan Newcastle United, Alexander Isak.

    Wasan da Liverpool za ta yi da Newcastle United ranar Lahadi zai kasance karo na farko da Isak zai koma filin St James' Park tun bayan barinsa Newcastle cikin yanayi mai cike da ce-ce-ku-ce a bazarar bara.

    Ɗan wasan mai shekaru 26 ya fuskanci matsaloli na rashin ƙwazo da kuma raunuka tun bayan komawarsa Liverpool kan kuɗi kimanin fam miliyan 125, wanda ya zama ciniki mafi tsada a tarihin ƙungiyar a wancan lokaci.

    Sai dai Isak na fatan amfani da wasan na wannan ƙarshen mako wajen farfado da rayuwarsa a Liverpool, musamman kasancewar zai koma filin da ya taɓa kira gida a lokacin da yake taka leda a Newcastle.

    Idan ya buga wasa, za a mayar da hankali sosai a kansa daga magoya bayan Newcastle, yayin da zai yi ƙoƙarin nuna wa tsohuwar ƙungiyarsa cewa har yanzu yana da abin da zai bayar a matakin koli.

  7. Babu abota tsakaninmu cikin mintina 90

    Kocin Fulham, Álvaro Arbeloa, ya yi magana kan dangantakarsa da kocin Chelsea Xabi Alonso gabanin wasan hamayya na Landan da za su fafata a ranar Litinin.

    "Mun yi nazarin Chelsea kamar yadda muke yi wa kowace ƙungiya. Na san Xabi sosai saboda na kalli wasanninsa da yawa, amma mun san cewa ba zai kasance wasa mai sauƙi ba. Suna da ƙungiya mai ƙarfi sosai tare da fitattun 'yan wasa. Sun yi siyayya masu kyau a kasuwar musayar 'yan wasa. Dole ne mu kasance cikin shiri."

    Game da ko sun yi magana da Alonso kafin wasan, Arbeloa ya ce: "Mun yi magana kwanaki kaɗan da suka wuce, amma ba batun ƙwallon ƙafa muka tattauna ba. Iyalanmu suna zuwa Landan. Mu abokai ne na ƙwarai. Amma na mintuna 90 na wasan, za mu ba da duk abin da muke da shi domin ƙungiyoyinmu. A cikin waɗannan mintuna 90 mu ba abokai ba ne. Kowannenmu yana son lashe wasan."

    Arbeloa da Alonso sun kasance abokai tun lokacin da suke taka leda tare a Spain, amma kocin Fulham ya jaddada cewa abota za ta koma gefe yayin da kowannensu ke neman samun nasara a wasan na farko na kakar Premier League.

  8. Foden da Cherki 'za su iya wasa tare su ba da abin da ake so'

    Kocin Manchester City, Enzo Maresca, ya ce Phil Foden da Rayan Cherki za su iya taka leda tare a cikin ƙungiya, duk da cewa suna taka irin rawa mai kama da juna a bayan ɗan wasan gaba Erling Haaland.

    Da aka tambaye shi ko yana kallon Foden da Cherki a matsayin masu fafatawa kan wuri ɗaya a cikin tawaga, Maresca ya ce: "Za su iya taka leda tare, a matsayi daban-daban. Amma tabbas suna da kamanceceniya sosai."

    Ya ƙara da cewa: "A ƙarshe, idan kana son gina babbar ƙungiya mai ƙarfi, dole ne a samu gasa tsakanin 'yan wasa a cikin tawagar. Don haka abu ne mai kyau cewa Phil da Rayan suna ƙara wa juna ƙalubale. Amma kuma suna iya taka leda tare a wasu wasanni."

    Kalaman Maresca na nuna cewa bai ɗauki zuwan Cherki a matsayin barazana ga Foden ba, sai dai a matsayin wata dama ta ƙara inganci da zaɓuɓɓuka a cikin tawagar Manchester City. Haka kuma, ya yi nuni da cewa duka 'yan wasan na iya kasancewa cikin tsarin wasa guda, gwargwadon yadda ƙungiyar za ta buga wasan.

  9. Man City na son Elias, sai dai Wharton kan iya fin karfinta

    Yayin da Savinho ke dab da komawa Tottenham Hotspur, kocin Manchester City Enzo Maresca na neman karin karfi a bangaren hagu na gaban kungiyar.

    Dan wasan gefe na Brazil, Allan Elias, ya zama daya daga cikin manyan wadanda kungiyar ke son saya.

    A cewar rahoton ESPN, Manchester City na tattaunawa da Palmeiras domin daukar dan wasan mai shekaru 22.

    Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa City ta nemi bayani kan yiwuwar daukar Adam Wharton, amma a cewar jaridar The Sun, kungiyar Crystal Palace na son ci gaba da rike dan wasan tsakiya na Ingila mai shekaru 22 kuma ba ta da niyyar sayar da shi a halin yanzu.

  10. 'Ba zan iya komai ba kan jita-jitan Baleba'

    Kocin Brighton & Hove Albion, Fabian Hurzeler, ya yi magana kan jita-jitar da ke alaƙanta ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar, Carlos Baleba, da komawa Manchester United.

    "Shi ɗan wasanmu ne, kuma ba na son yin tsokaci kan jita-jitar da ke yawo a kafafen yaɗa labarai. Haka kuma, wannan wani abu ne da ba ni da iko d shi."

    Hurzeler ya guji yin magana kai tsaye kan yiwuwar cinikin, yana mai jaddada cewa Baleba har yanzu ɗan wasan Brighton ne.

    Kocin ya kuma bayyana cewa Baleba ba zai buga wasan ranar Lahadi ba saboda ba shi da cikakken ƙoshin lafiya."Ba shi da cikakken lafiya."

    An rahoto cewa ɗan wasan tsakiya na Kamaru ya samu raunin ƙafa a lokacin shirye-shiryen tunkarar sabuwar kakar wasa, kuma har yanzu bai murmure gaba ɗaya ba.

    Rashin Baleba zai zama babban gibi ga Brighton, ganin yadda ya taka muhimmiyar rawa a tsakiyar fili tun bayan komawarsa ƙungiyar. Duk da haka, Hurzeler ya nuna cewa fifikon ƙungiyar a yanzu shi ne tabbatar da cikakken lafiyarsa kafin komawarsa filin wasa.

  11. Tottenham na son Mateta

    Bayan amincewa da yarjejeniyar daukar tauraron gefen Manchester City, Savinho, Tottenham na ci gaba da duba wasu 'yan wasan gaban da za su kara mata karfin gab.

    Mun riga mun ba ku labarin tattaunawar da Spurs ke yi da Manchester City kan dan wasan gaba na Masar, Omar Marmoush. Amma rahoton Football Insider ya bayyana cewa Tottenham na kuma nazarin yiwuwar daukar dan wasan gaba na Faransa, Jean-Philippe Mateta, mai shekaru 29, daga Crystal Palace.

    Tottenham na neman kara zabin 'yan wasan gaba a kungiyar yayin da take shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa, kuma Mateta na daga cikin sunayen da ake la'akari da su a halin yanzu.

  12. Ko shakka babu Liverpool za ta karo sabbin 'yan wasa - Araola

    Sabon kocin Liverpool, Andoni Iraola, ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ƙara sayen sababbin 'yan wasa kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa a ranar 1 ga Satumba.

    Da yake magana da Sky Sports kafin wasan farko na Liverpool a gasar Premier League ta bana da Newcastle United ranar Lahadi, Iraola ya ce: "Tabbas za mu sayi wasu 'yan wasa. Akwai wasu yarjejeniyoyi da sai an jira zuwa ƙarshen kasuwar musayar 'yan wasa."

    Ya ƙara da cewa:"Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ƙungiyar za ta kasance a ranar 1 ga Satumba. Domin gaskiya ne cewa har yanzu ba mu da isassun 'yan wasa a wasu wurare."

    Kalaman na Iraola na nuna cewa Liverpool na ci gaba da bincike a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa domin ƙarfafa tawagar kafin rufe kasuwar bana.

    Kocin ya amince cewa har yanzu ƙungiyar tana buƙatar ƙarin 'yan wasa a wurare da dama, duk da cewa kakar wasa ta riga ta fara.

  13. Coventry Cuty ta dauki Bentley daga Wolves

    Coventry City ta sanar da daukar mai tsaron ragar Ingila Dan Bentley daga Wolverhampton Wanderers kan kwantiragin shekaru biyu.

    Dan wasan mai shekaru 33, wanda ya taba taka leda a Southend United da Brentford, ya buga wasanni 14 kacal a Wolves cikin shekaru uku da suka gabata bayan komawarsa daga Bristol City.

    Bentley ya ce yana da burin kawo kwarewa da jagoranci ga kungiyar ta Coventry yayin da kulob din ya koma gasar Premier League.

    Da yake magana da shafin yanar gizon Sky Blues, mai tsaron raga ya ce:"Ni dan wasa ne mai kwarewa, mai halayen jagoranci masu kyau, kuma mutum ne da ke da manyan ka'idoji da buri."

    Ya kara da cewa: "Hakika, ina son in nuna abin da zan iya a filin wasa ma. Akwai kyakkyawar tawagar masu tsaron gida a nan, don haka ina son in kara mata karfi. Idan kuma na samu dama ta buga wasa, alhakin nawa ne in yi amfani da damar yadda ya kamata."

    Bentley na fatan amfani da gogewarsa domin taimakawa Coventry a kakar wasannin da ke gaba, tare da fafatawa domin samun gurbin buga wasa a kungiyar.

  14. Wan-Bissaka zai koma Aston Villa a matsayin aro

    Aston Villa ta kammala daukar dan bayan West Ham, Aaron Wan-Bissaka, a yarjejeniyar aro ta tsawon kakar wasa guda.

    Yarjejeniyar Villa ta daukar dan wasan gefen dama na DR Congo tana dauke da “sharadin wajabcin saye” idan wasu sharudda suka cika.

    Ba a bayyana cikakkun sharuddan yarjejeniyar ba, amma a baya West Ham ta nemi kungiyoyin da ke sha'awar dan wasan su biya kudin fam miliyan 25.

    A kakar wasan da ta gabata, Villa ta dauki dan wasan tsakiya na Liverpool, Harvey Elliott, a matsayin aro na kakar wasa guda tare da sharadin saye kan fam miliyan 35.

    Sai dai yarjejeniyar ta tanadi cewa za a sayi Elliott din ne kawai idan ya buga wasannin lig guda 10. Bayan ya buga wasanni hudu kacal, ya koma Liverpool a wannan bazarar.

    Wan-Bissaka ya rasa wasanni biyu na farko na West Ham a gasar Championship ta wannan kakar yayin da ake tattaunawar komawarsa gasar Premier League.

    Dan wasan mai shekaru 28 ya koma West Ham daga Manchester United a shekarar 2024, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru bakwai.

    Ya buga wasanni 65 a cikin kakanni biyu da ya yi a kungiyar, ciki har da wasanni 25 a kakar da ta gabata lokacin da West Ham ta sauka zuwa Championship.

    Kafin haka, ya buga wasanni 190 a Manchester United, inda ya lashe League Cup a shekarar 2023 da kuma FA Cup a shekarar 2024.

  15. Disasi na Chelsea na gwajin lafiya a Crystal Palace

    Axel Disasi, ɗan wasan bayan Chelsea, ya samu izinin zuwa Crystal Palace domin yin gwajin lafiya yayin da tattaunawa ke ci gaba kan batun komawarsa ƙungiyar a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda.

    Crystal Palace, wadda ke kudancin Landan, ita ce ta fi nuna sha'awar ɗan wasan bayan na tsakiya ɗan ƙasar Faransa mai shekaru 28, kuma dukkan ɓangarorin da abin ya shafa suna son a kammala yarjejeniyar.

    Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan adadin kuɗin aron ɗan wasan, amma ana sa ran Chelsea da Crystal Palace za su kai ga cikakkiyar yarjejeniya nan gaba kaɗan.

    Ga Crystal Palace, idan aka kammala cinikin, Disasi zai zama ɗan wasa na bakwai da sabon koci Pierre Sage ya ɗauka a wannan bazarar, yayin da yake sake gina da ƙarfafa tawagar ƙungiyar.

  16. Labarin tawagar Fulham gabanin wasan Chelsea

    Kocin Fulham, Alvaro Arbeloa, ya tabbatar da cewa Tom Cairney ne kaɗai ɗan wasan da ba zai kasance cikin jerin ‘yan wasan da za su fafata da Chelsea ba saboda rauni a wasan farko na Premier League da za a buga ranar Litinin a gida da abokan hamayyarsu na yammacin Landan.

    Ɗan wasan tsakiya Cairney ya yi wani ƙaramin aikin tiyata a gwiwar hagu a lokacin hutun bazara.

    Haka kuma, ɗan wasan baya Joachim Andersen ba zai buga wasan ba saboda dakatarwa.

  17. Joao Pedro zai tsawaita kwantaraginsa da Chelsea zuwa 2034

    Joao Pedro, ɗan wasan gaba na Chelsea, na shirin sanya hannu kan sabon kwantiragi da ƙungiyar wanda zai ci gaba har zuwa shekarar 2032, tare da zaɓin ƙarin shekaru biyu.

    Ɗan wasan ƙasar Brazil mai shekaru 24 ya koma Chelsea daga Brighton a bazarar bara kan kuɗi fam miliyan 55, tare da yiwuwar ƙarin fam miliyan 5.

    Lokacin da ya rattaba hannu da Chelsea, an bayyana cewa kwantiraginsa zai kare ne a shekarar 2033.

    Sai dai a zahiri, yarjejeniyar ta kasance har zuwa shekarar 2032, tare da zaɓin ƙarin shekara guda a hannun ƙungiyar.

    Chelsea kan saba haɗa irin waɗannan zaɓuɓɓukan tsawaita kwantiragi a cikin sanarwar da take fitarwa a hukumance, kuma tana ƙididdige su a matsayin wani ɓangare na tsawon kwantiragin ɗan wasa.

    Saboda haka, idan aka tabbatar da sabon kwantiragin Joao Pedro, akwai yiwuwar Chelsea ta sanar da cewa zai kasance a ƙungiyar har zuwa 2034, duk da cewa ainihin yarjejeniyar za ta kasance har zuwa 2032 tare da zaɓin ƙarin shekaru biyu.

    A hakikanin gaskiya, Chelsea ba ta rage masa tsawon kwantiragi ba ne, sai dai ta tsawaita masa yarjejeniyarsa tare da ingantattun sharuɗɗa da albashi mafi kyau.

  18. Tottenham ta amince za ta biya £75m kan Savinho na Man City

    Tottenham sun amince da yarjejeniya da Manchester City domin sayen ɗan wasanta na gefe Savinho kan kuɗi fam miliyan 75, tare da yiwuwar ƙarin fam miliyan 10 idan wasu sharuɗɗa suka cika.

    Savinho mai shekaru 22 a duniya yanzu zai yi gwajin lafiya kafin ya sanya hannu kan kwantiragin dogon lokaci da Tottenham.

    Yunkurin kawo ɗan wasan na Brazil zuwa arewacin Landan ya shafe fiye da watanni 12 ana tattaunawa a kai, domin Tottenham ta kasa samun nasarar sayensa a bazarar shekarar da ta gabata.

    Savinho ya zaɓi ci gaba da zama a filin wasa na Etihad Stadium, amma bai samu isasshen lokacin buga wasa a ƙarƙashin koci Pep Guardiola ba a kakar da ta gabata, inda ya fara wasa sau bakwai kacal a gasar Premier.

    Bayan kashe jimillar fam miliyan 185 wajen sayen ‘yan wasan tsakiya Mateus Fernandes daga West Ham da Sandro Tonali daga Newcastle, kocin Tottenham Roberto de Zerbi na neman ƙara wa gaban ƙungiyarsa ƙarfi.

  19. Me ya faru da cinikin Barcola da Liverpool

    Babban abin da Liverpool ta fi mayar da hankali a kai a kasuwar musayar 'yan wasa har yanzu shi ne yan wasan gaba masu kai hari, musamman neman ɗan wasan gefe na PSG, Bradley Barcola.

    Kokarin ɗauko Barcola yana ɗaukar lokaci saboda tattaunawar da ake yi tsakanin ƙungiyoyin biyu, amma akwai yiwuwar cewa Liverpool da Paris Saint-Germain za su cimma yarjejeniya a wannan bazarar domin ɗaukar ɗan wasan na Faransa.

    A halin yanzu, da alama Liverpool ba ta da niyyar gaggawar neman wani sabon ɗan wasan tsakiya duk da tafiyar Jones. Sai dai, kamar yadda aka saba a kasuwar musayar 'yan wasa, idan wata dama mai kyau ta bayyana, ƙungiyar na iya ɗaukar mataki.

    A bana, Liverpool ta riga ta tsawaita kwantiragin Dominik Szoboszlai da Ryan Gravenberch na dogon lokaci. Haka kuma, matashin ɗan wasa mai shekara 19, Trey Nyoni, zai samu damar nuna bajintarsa ga kocin ƙungiyar Andoni Iraola.

    Alexis Mac Allister, wanda ya rage masa shekaru biyu a kwantiraginsa na yanzu a Anfield, shi ma ba shi da shirin barin ƙungiyar a wannan lokacin.

    Sai dai kasancewar har yanzu ba a fara wata tattaunawa a hukumance kan sabon kwantiragi da Mac Allister ba, akwai yiwuwar Liverpool ta mai da hankalinta sosai wajen ƙarfafa tsakiya a cikin watanni 12 masu zuwa.

  20. Ko Arsenal za ta ɗauki Yildiz?

    Lallai Arsenal na da son ɗan wasanJuventus Yildiz, kuma yana cikin jerin 'yan wasan da ƙungiyar ta dade tana sa ido a kansu.

    Magoya baya ba sa son kalmar “sa ido” , amma gaskiyar ita ce Arsenal ta kasance tana bibiyar ci gabansa da wasanninsa.

    Arsenal na neman ɗan wasan da zai ƙara wa gabanta karfi da kuma ɗaga martabarta wajen cin kwallaye.

    Yildiz na da babbar baiwa da kuma kyakkyawar makoma a gaba.

    Sai dai har yanzu ba a san ko kuɗin da za a kashe domin sayensa zai dace da darajar da ake nema ba, idan Arsenal ta yanke shawarar yin tayi.

    Haka kuma, akwai tambaya kan ko zai iya kawo sauyi nan take a a gaban Arsenal da kuma samar da ƙarin ƙarfi da ƙungiyar ke nema a wannan lokaci?