’Yan Najeriya 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu
Hukumomin Najeriya sun ce ’yan ƙasar 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu a ƙarƙashin wani shirin mayar da ’yan ƙasa da wasu ’yan kasuwar Najeriya ke ɗaukar nauyin sa.
Mutanen sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a yammacin Laraba, a cikin jirgin kamfanin South African Airways, inda ta ce jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da hukumar kula da ’yan gudun hijira, ’yan ci-rani da masu gudun Hijira a cikin gida (NCFRMI) ne suka tarbe su.
A cewar NCFRMI, waɗanda suka dawo sun ƙunshi manyan mutum 30, yara 36 da jariri guda ɗaya. Mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar, Alex Oturu, ya shaida wa BBC cewa wasu ’yan kasuwar Najeriya ne suka ɗauki nauyin aikin, ƙarƙashin jagorancin Ikem Ume-Ezeoke.
Ya ce kowa daga cikin waɗanda suka koma ya samu tallafin naira 50,000 ($32; £24), yayin da NEMA ta taimaka musu wajen ci gaba da tafiya zuwa garuruwansu a sassa daban-daban na Najeriya.
Wannan sabon aikin ya zo ne gabanin ranar ƙarshe ta 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da baƙin haure a Afirka ta Kudu suka sanya, inda suka yi kira ga ’yan ci-ranin da ba su da takardun izinin zama su bar ƙasar.