Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta ƙaryata cewa jiragen Amurka sun ratsa ta mashigar Hormuz

    Iran ta musanta iƙirarin da Amurka ta yi na cewa jiragen sojin ruwanta biyu sun ratsa ta mashigar Hormuz.

    "Mun musanta iƙirarin kwamandan babbar cibiyar ayyukan sojin Amurka (CENTCOM) na cewa jiragen ruwan Amurka sun ratsa ta mashigar Hormuz," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars, na Iran ya ambato mai magana da yawun shalkwatar rundunar tsaron Iran na bayyanawa.

    "Amincewa da ratsawar duk wani jirgin ruwa na hannun dakarun jamhuriyar Musulunci ta Iran," a cewar jami'in.

    Tun farko a ranar Asabar, cibiyar ayyukan sojin Amurka ta wallafa wani saƙo a shafin X cewa dakarun Amurka sun "tsara yadda za a cire nakiyoyi a ƙarƙashin mashigar Hormuz" sannan kuma jiragen ruwa biyu "sun ratsa ta mashigar Hormuz...a matsayin wani mataki na ganin an kawar da nakiyoyi daga babbar hanyar ruwan ta Hormuz".

  2. Iran da Amurka na ci gaba da tattaunawa har tsakar dare

    BBC ta fahimci cewa an ci gaba da tattaunawar neman cimma yarjejeniya da ke gudana a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan har zuwa tsakiyar dare.

    Tuni aka kwashe sa'o'i ana tattaunawar da ta ƙunshi ɓangarori uku: wato Amurka da Iran da kuma Pakistan mai shiga tsakani.

  3. Za mu baiwa sojojinmu wadatattu makamai don yaƙi da 'yan ta'adda -Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta shirya domin ƙarfafa sojojin Najeriya da ke yaƙi da 'yan ta'adda da 'yan bindiga a faɗin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar kwana guda da ya kai jihar Bayelsa a ranar Juma'a, inda ya ƙaddamar da wani aiki da Gwamna Douye Diri ya yi, inda shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa dakarunta atisaye da kayan aiki domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar.

    Ya jaddada cewa sun mayar da hankali wajen neman cin nasara da kawo ƙarshen duk wasu lamuran tsaro.

    Rahotanni sun ambato tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan da mai ɗakinsa Patience na cikin waɗanda suka raka shugaban ƙasar taron.

  4. "Jiragen man Amurka sun wuce ta mashigar Hormuz"

    Rundunar sojan Amurka ta ce wasu jiragen ruwa biyu na sojin Amurka sun bi ta mashigin Hormuz, karon farko bayan fara yaƙi da Iran.Da farko shugaba Trump ya ce Washington ta fara kwashe nakiya daga mashigar ruwa, ikirarin da Tehran ta ƙaryata.Wani jami'in sojan Amurka ya ce an mayar da hankali kan samar da hanya jigilar kayayyakin kasuwanci.

    Sake buɗe mashigar inda kusan kashi biyar na man duniya ke wucewa mataki ne mai muhimmanci Amurka.

  5. An karya yarjejeniyar da muka cimma - Rasha

    Jami'an Rasha sun ba da rahoton karya yarjejeniyar tsagaita wuta a lokacin bikin Easter, sun zargin Ukraine da kai hare-hare da jirage marassa matuka a iyakar da ta hada ƙasashen biyu.

    Rahotonni sun bayyana yadda wasu mutane uku suka jikkata a Kursk ya yin da wasu biyu suka ji raunuka a yankin Belgorod.

    Har yanzu Moscow ba ta ce komai ba.

    Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda ta fara aiki za ta kai ranar Lahadin gobe.

    Tun da farko Ukraine da Rasha sun yi musayar sojojin da suka kama da yawansu ya kai 170 tare da fararen hula bakwai.

  6. An kammala tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran

    Tawagar manyan jamai'an Iran da Amurka sun yi zaman tattaunawar sulhu ta sa'o'i biyu a birnin Islamabad.

    Ba a sanar da matsayar zaman ba, amma wakilin BBC ya ce amincewar bangarorin biyu su yi ganawar kai tsaye alama ce ta nasara.

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ce za a ƙara wata tattaunawar a ƙarshen mako.

    Wakilan Amurka ba su ce komai ba game da zaman tattaunawar sulhun.

    Ɓangarorin biyu na zargin juna da karya yarjejejniyar tsagaita wuta.

    Ya yinda suke neman matsaya game da batutuwa da dama da suka haɗa da wucewa ta mashigin Hormuz da janyewa Iran takunkumai da tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon da kuma makomar shirin nukiliyar Tehran.

  7. Ko Amupitan ya sauka ko mu ɗauki matakin ban mamaki - ADC

    Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya tace ko Shugaban Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta INEC Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa ko kuma sau ɗauki matakin da zai girgiza kasar.

    Jam'iyyar ta bayyana haka ne lokacin da take gabatar da wasu sabbin zarge-zarge kan shugaban hukumar.

    ADC ta soki Amupitan kan tsofaffin bayanansa da ya wallafa a shafinsa na Twitter waɗanda suka riƙa nuna goyon bayansa ga jam'iyyar APC mai mulki.

    Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar INEC ta hannun sakataren watsa labaranta Adedayo Oketola, tace Shugaban ya gargaɗi mutane da amfani da intanet wajen bata suna da kuma aikata laifuka ta internet da kuma amfani da bayanan bogi da yaɗa labaran ƙarya.

    Ya kuma jaddada cewa INEC ƙarƙashin shugabanci Amupitan na fatan gudanar da zaɓe mai sahihanci da babu cutarwa cikinsa, inda ya shawarci mutane su riƙa neman bayanai daga kafar INEC kawai don gujewa bayanan ƙarya.

    Da yake nasa bayanin kakakin ADC Bolaji Abdullahi ya ce, "Bayanan da aka samu na yadda shugaban INEC ke goyon bayan Bola Tinubu ba kawai ta da hanakali suke yi ba kawai, wata fitina ce da ke tunkarar tsarin zaɓen Najeriya.

    "Dole ne Farfesa ya yi murabus, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba. Gaza hakan cin fuska ne ga mutanen Najeriya kuma haɗari ne ga dimokradiyyarta," in ji Bolaji.

  8. Tafiyar Arsenal ta cin Premier na cikin rashin tabbas

    Ƙoƙarin Arsenal na lashe kofin Premier ya haɗu da babban koma baya, bayan kashin da ta sha a hannun Bournemouth har gida a filin wasa na Emirates.

    Wannan na nufin Arsenal ta yi rashin sa'a wajen samun damar ƙara maki uku kan 12 da ta baiwa ta bayanta Manchester City wadda za ta yi wasa da Chelsea a gobe Lahadi.

    Bournemouth ce t fara jefa ƙwallo ta farko ta hannun Kroupi a minti na 17 da fara wasan, yayin da Viktor Gyokeres ya farke wa Gunners a minti na 35, Alex Scott ne ya ƙara kwallo ta biyu a minti na 74.

    Mikel Arteta ya yi kira ga magoya bayan ƙungiyar saboda muhimmancin wasan ga kakar wasa Gunners domin ƙarawa ƙungiyar kwarin gwiwa, wadda fatanta na lashe Carabao da FA Cup ya zo ƙarshe a makonnin baya.

    Wannan ce kaka kusan ta uku da Arsenal ke fadawa matsanancin hali a Premier lokacin da damar lashe kofi ke hannunta, amma daga baya ta kufce, duka ƙarƙashin mai koyarwa Mikel Arteta.

  9. Ba za mu yarda da tashin farashin takin zamani ba - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana ''lura da farashin takin zamani a lokacin abin da ya kira yaƙin neman ƴanci da Iran.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Trump ya ce ''Amurka ba za ta yarda da tashin gwauron zabon farashin takin ba''.

    A baya-bayan nan ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kashi ɗaya bisa uku takin zamanin duniya - irin su uriya da potash da amoniya da kuma phosphates - na bi ta mashigar Hormuz.

    Wasu alƙaluma daga Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya sun nuna cewa tun bayan fara yaƙin aka dakatar da jigilar taki ta mashigin.

  10. Kafofin labarai na son cewa Iran na samun nasara bayan kuma babbar asara take yi - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Iran ta yi ''babbar asara'' a yaƙin da Amurka da Isra'ila suke yi da ƙasar.

    Cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce kafofin yaɗa labarai na ''son cewa Iran na samun nasara, bayan kuma a gaskiya kowa ya san babbar asara take yi''.

    Ya jaddada iƙirarin da gwamnatinsa ta sha yi a lokacin yaƙin cewa ''An gama da rundunar sojin ruwan Iran da rundunar sojin samanta, na'urorin kakkaɓo jiragenta sun daina aiki, sadarwar tsaronta ta Radar ta daina aiki''.

    ''An ruguza masana'antun ƙera makamanta masu linzami da na jirage marasa matuƙa, an kuma lalata makaman linzamin kansu da jiragen marasa matuƙa, wani abu mafi muhimmanci shi ne jagororin ƙasar da suka jima suna jan ragamar ƙasar a yanzu babu su, mun gode wa Allah'', in ji shi.

    Bayan bayyana cewa Iran na dasa nakiyoyi a cikin teku, ya ce Amurka ta fara ''share mashigar Hormuz domin taimaka wa ƙasashen duniya''.

    Saƙon na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da tawagogin ƙasashen Amurka da Iran suka fara tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin a Pakistan.

  11. Labarai da dumi-dumi, An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Pakistan

    Rahotonni daga Islamabad, babban birnin Pakistan na cewa an fara tattaunawar yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

    Ana tattaunawar ne bisa jagorancin Pakistan mai shiga tsakani.

    Ƙasashen biyu sun aike da tawagar wakilai da suka ƙunshi ƙwararren masana diplomasiyya da siyasar duniya.

    Ana sa ran tattauanwar ta haifar da yarjejeniyar dindindin ta kawo ƙarshen yaƙin.

  12. Wane ne Mohammad Bagher Ghalibaf da ke cikin tawagar wakilan Iran?

    Mohammad Bagher Ghalibaf na cikin tawagar wakilan Iran da ke Pakistan domin tattaunawa da Amurka don kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu.

    Ɗan siyasa ne mai tattsauran ra'ayi da ke da ƙwarewar aikin soji, wanda a yanzu ke riƙe da mjuƙamin kakakin majalisar dokokin Iran.

    Tuni dai ya nuna fatan samun amince a tattaunawar.

    Ya yi zargin cewa a tarihance tattaunawa da Amurka ba a fiye samun nasara ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim na ƙasar ya ruwaito.

    An haifi Ghalibaf a shekarar 1961, sannan ya shiga rundunar juyin juya halin ƙasar a shekarar 1980 inda ya zama ɗaya daga cikin kwamandojin rundunar lokacin yaƙin Iran da Iraƙi.

    Ghalibaf - wanda ya zama magajin garin birnin Tehran mafi daɗewa - ya riƙe muƙamin na tsawon shekara 12.

    Sau huɗu yana tsayawa takarar shugaban ƙasar, kodayake ba ya yin nasara, inda a 2013 ya zo na biyu.

    Yana yawan wallafa saƙonni a shafukansa na sada zumunta tun bayan fara yaƙin, duk kuwa da rashin intanet a ƙasar.

  13. Rasha da Ukraine sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'a 32

    Ana sa ran tsagaita wuta za ta fara a Ukraine da yammacin yau Asabar, domin bikin Easter na Orthodox.

    Gwamnatocin Rasha da Ukraine sun amince da dakatar da duk wani faɗa na tsawon sa’o’i 32.

    Shugaba Zelensky ya ce ƴan Ukraine na buƙatar yin bikin Easter ba tare da barazana ba, amma yana son Rasha ta amince da tsagaita wuta mai ɗorewa har sai ɓangarorin biyu sun tattauna yarjejeniyar zaman lafiya.

    Sai dai Kremlin ta yi watsi da hakan, tana mai cewa tsagaita wutar ta wucin-gadi ce kawai.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu, sama da fararen hula 15,500 ne aka kashe a Ukraine tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da mamayarta, fiye da shekaru huɗu da suka wuce.

  14. Abin da ya sa na yi waƙar Samarin Shaho - Fati Halidou

    Fitacciyar mawaƙiyar nan ta Jamhuriyar Nijar, Fati Halidou ta bayyana dalilan da suka ja hankalinta har ta yi waƙar Samarin Shaho

  15. Vance ya gana da firaministan Pakistan

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka, JD Vance ya gana da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif.

    Mistan Vance na tare da jakadan Trump na musamman Steve Witkoff da Jared Kushner, surukin shugaba Trump da ke cikin tawagar Amurkan.

    Ganawar tasu na zuwa ne gabanin tattaunawa da wakilan Iran domin kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran ɗin.

    Mista Sharif ya bayyana fatansa game da tattaunawar, wadda ya ce za ta zama matakin farko na samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Tun da farko firaminstan na Pakistan ya gana da wakilan Iran, ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi.

  16. Su wane ne wakilan Iran da Amurka a tattaunawar da ake yi a Pakistan?

    Yayin da wakilan Amurka da Iran suka isa birnin Islamabad domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka, hankula sun koma kan su wane ne wakilan ɓangarorin biyu?

    A irin wannan tattaunawa dai kowace ƙasa kan aika da ƙwararrun mutane ta fuskar diplomasiyya domin kare muradunsu.

    Iran dai ta gabatar da sharuɗaɗɗa 10 da take son a amince da su domin kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Amurka ta gabatar da 15.

    Suwa ne wakilan ɓangarorin biyu?

    • Tawagar Amurka

    JD Vance: Washinton ta aike da wakilai ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar.

    Ana sa ran Vance zai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar.

    A baya Mista Vance ya sha bayyana adawarsa da yaƙe-yaƙe, ya kuma nuna rashin goyon bayan ƙazancewar yaƙin Iran.

    Steve Witkoff: Sakataren harkokin wajen ƙasar, Steve Witkoff, wanda amini ne ga Shugaba Trump kuma ƙwararren jami'in diplomasiyya.

    Ya taka muhimmiyar rawa a manyan al'amuran duniya ciki har da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza da na Ukraine.

    Jered Kushner: Suruki ne ga shugaba Trump, shi ma ya ƙware a fannin diplomasiyya.

    Ya taka rawar gani a diplomasiyyar yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da yarjejeniyar Abraham Accord.

    Kusher na gudanar da harkokinsa tsakanin kasuwanci da siyasar duniya.

    • Tawagar Iran

    Wakilan Iran na ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, wanda ƙwararren jami'in diplomasiiya ne.

    Yana da gogewar kusan shekara 40 a fannin diplomasiyya, wanda ya sha shiga manyan tattaunawa musamman da Amurka kan shirin nukiliyar Iran.

    Mohammad Bagher Ghalibaf: Kakakin majalisar dokokin Iran, wanda ya jagorancin rundunonin ƙasar da dama a matsayin kwamanda a baya.

    Ya taɓa riƙe muƙamin magajin garin birnin Tehran.

    Ghalibaf ya kasance kan gaba a shafukan sada zumunta wajen mayar wa Amurka martani.

    Waɗannan mutanen biyar za su yi amfani da gogewarsu ta aikin soji da siyasar duniya da kasuwanci da diplomasiyya wajen kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kusan kwana 40 ana gwabzawa.

    Sakamakon tattaunawar da za a yi a Pakistan shi ne zai tantance makomar alaƙar Amurka da Iran.

  17. Su wane ne wakilan Amurka da Iran a tattaunawar Pakistan?

  18. Muna kiran Amurka da Iran su shiga tattaunawar da zuciya ɗaya - MDD

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da tattaunawar zaman lafiya da Amurka da Iran suka amince za su yi, inda ya buƙaci ɓangarorin biyu su shiga tattaunawa da ''zuciya ɗaya''.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai, kakakin Gutteres, Stephane Dujarric ya ce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya yi kira ga duka ɓangarorin biyu su yi amfani da damar tattaunawar wajen kawo ƙarshen rikicin ta hanyar amincewa da cikakkiyar yarjejeniyar.

    "Babban sakataren ya jaddada cewa babu wata hanyar kawo ƙarshen yaƙin cikin zaman lafiya da ta wuce hanyar diplomasiyya,'' in ji Dujarric.

    Jakadan Guterres na musamman ya isa yankin domin tallafa wa yunƙurin diplomasiyyar.

  19. Muna fatan samun tattaunawa mai amfani - Pakistan

    Ministan harkokin wajen Pakistan, Mohammad Ishaq Dar ya yaba wa Amurka kan burinta na samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.

    Mista Dar ya bayyana hakan ne lokacin da yake tarbar tawagar Amurka ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance lokacin da suka isa Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran bisa shiga tsakanin Pakistan domin kawo ƙarshen yaƙin Iran da AMurka da kuam Isra'ila.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta fitar, ta ambato Dar na cewa yana fatan samun tattaunawa mai amfani tsakanin Iran da Amurka.

    Ya kuma jaddada burin Pakistan na ci gaba da shiga tsakanin ɓangarorin biyu har zuwa lokacin da za su cimma yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin.

  20. Ƴan sama-jannatin Amurka da suka je duniyar wata sun sauko

    Ƴan sama-jannatin nan huɗu, na shirin zuwa duniyar wata na Artemis II sun dawo wannan duniya tamu lami lafiya, bayan wata doguwar tafiya zuwa duniyar wata, inda suka zagaye shi kafin dawowa gida.

    A yanzu sun zamo rukunin bil'adama na farko da aka samu harbawa duniyar watan a sama da rabin ƙarni.

    Kumbon da suke ciki ya sauko da taimkon lemmomi a cikin Tekun Pasifik kusa da kudancin California bayan shafe kwanaki 10 a sararin samaniya.

    Daga nan ne aka ɗauke su zuwa wani jirgin ruwan sojin Amurka domin duba lafiyarsu.

    Hukumar kula da sararin samaniyar ƙasar NASA, ta ce suna cikin ƙoshin lafiya, tare da bayyana wannan aiki a matsayin gagarumin ci gaba a binciken sararin samaniya da ɗan'adam ke yi.

    Masana sun bayyana nasarar a matsayin muhimmin mataki a ƙoƙarin ci gaba da tura mutane duniyar watan.