Nijar ta gayyaci kamfanonin sufuri bayan hatsarin bas da ya kashe mutum 22
Gwamnatin Nijar ta gayyaci kamfanonin sufuri biyu domin amsa tambayoyi bayan wani mummunan hatsarin bas da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 22, ciki har da sojoji 17.
Ma'aikatar Sufurin ƙasar ta ce motocin kamfanonin STM da SONITRAV ne suka yi karo da juna gab da ƙauyen Rezi a yankin Madaoua.
Motar kamfanin SONITRAV na ɗauke da sojojin da ke dawowa daga horaswa.
Baya ga mutum 22 da suka rasu, mutum 37 sun kuma jikkata.
Hukumomi sun ce sun fara bincike kan musabbabin hatsarin tare da ɗaukar matakan hana irin haka a gaba.
Hatsarin ya sake tayar da hankali kan matsalar haɗurran motoci a hanya a Nijar, inda ake yawan danganta su da gudun da ya wuce kima, take dokokin hanya da kuma lodin da ya wuce ƙa'id