Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 02/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 02/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Manyan kantuna a ƙasashen Turai sun fuskanci hari ta intanet

    Wasu manyan kantunan sayar da kayayyaki a ƙasashe bakwai na Turai sun fuskanci hari ta intanet, wanda ya sa aka ɗaga yanayin sanyi a firij da na’urorin daskare kayayyaki daga nesa.

    Rahotanni sun ce kusan shaguna 40 ne lamarin ya shafa a ƙasashen Belgium da Luxembourg, inda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ce an zubar da abinci da darajarsa ta kai miliyoyin Yuro saboda lalacewa.

    Richard Nilsson manajan katafaren kantin saida kayayyaki na ICA a Sweden ya ce dole ta sa suka zubar da komai tare da yin asara da darajarsa ka iya kai wa miliyan daya na Euro,.

    ''Ban san ta inda masu kutsen za su amfana da hakan ba, amma wannan ya yi kama da harin ta'addanci,'' in ji Richard.

  2. Wata fashewa ta hallaka mutum hudu a yankin Douala na Kamaru

    Hukumomi a Kamaru sun ce aƙalla mutum huɗu ne suka mutu yayin da wasu 16 suka jikkata sakamakon wata fashewa a wata masana'antar narkar da ƙarafa da ke birnin Douala.

    Wata sanarwa da kamfanin Metafrique wanda ke gudanar da masana'antar ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Litinin, kuma har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin faruwar lamarin.

    Gwamnan yankin Littoral, Samuel Dieudonné Ivaha Diboua, ya shaida wa manema labarai cewa fashewar ta haddasa wata babbar gobara, inda jami'an kashe gobara suka garzaya wurin domin shawo kanta tare da ceto ma'aikatan da suka maƙale a cikin ginin.

    Ya kuma ce likitoci sun ce wadanda suka jikkata sun samu munanan raunuka, abin da ke ƙara tayar da fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa.

    Hukumomi sun ce an taba samun irin wannan gobara a masana'antar a farkon shekarar nan, abin da ya sake jawo ƙarin bincike kan matakan tsaron da kamfanin ke dauka.

    A halin yanzu, ana kula da wadanda suka jikkata a asibiti yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan musabbabin fasewar.

  3. Na yi imanin Allah ya amsa addu'ata - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa ƙasar hidima, inda ya ce yana da yakinin cewa Allah ya amsa addu’arsa ta ci gaba da kasancewa a kan mulki.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake kammala ziyarar da ya kai Saudiyya domin gudanar da Umrah.

    Tinubu ya samu damar shiga cikin Ka'aba tare da tawagar Najeriya, inda suka yi wa kasar addua'a.

    ''Ina matuƙar godiya ga Mai Kula da Masallatan Harami Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da kuma Yarima Mohammed bin Salman kan irin karamci da kyakkyawar tarbar da suka nuna mana,'' in ji Tinubu.

    Ya kuma tuna irin kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Saudiyya, inda ya ce ya yi amfani da damar shiga Ka'aba wajen yi wa Najeriya addu'ar samun zaman lafiya da kuma cigaba.

  4. Hare-haren Rasha sun hallaka mutum 18 a Ukraine

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce akalla mutum 18 ne suka mutu sakamakon hare-hare da dama da Rasha ta kai kan wata makaranta da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Mista Zelensky ya ce ana amfani da ginin makarantar da ke yankin Zaporizhzhia a matsayin cibiyar rarraba kayan agaji ga mazauna yankin.

    Ya ce an kai fiye da hare-hare goma wurin, yana mai ƙara da cewa Moscow tana sane da cewa ana amfani da makarantar wajen raba kayan agaji.

    Jami'an yankin sun ce mutane da dama sun jikkata a harin.

    A halin yanzu ana ci gaba da aikin ceto domin neman waɗanda abin ya shafa.

  5. 'Za mu kammala sa ido kan mutum 62 da suka yi hulɗa da masu Ebola nan da 13 ga Nuwamba'

    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya (NCDC), ta ce ana sa ran kammala sa ido kan mutane 62 da aka gano sun yi hulɗa da wadda aka tabbatar ta shigo da cutar Ebola ƙasar nan da 13 ga Nuwamban 2026.

    Hukumar ta bayyana haka ne a wasu sabbin bayanai da ta fitar dangane da yanayin cutar a kasar, ranar Litinin.

    NCDC ta tabbatar da samun mai dauke da Ebola na farko a kasar ranar 20 ga watan Oktoba, bayan gwaji ya gano cutar a jikin wata mata wadda ta yi balaguro daga Uganda.

    Duk da cewa cewa hukumar ba ta yadda za a sa idon ba, ta ce za a yi hakan a lokuta daban-daban tsakanin 31 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba.

    Ta kuma ce an yi wata ganawa ta masu ruwa da tsaki domin karfafa yaki da cutar.

  6. An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

    Wata Babbar Kotu a jihar Kano ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin kisan kai.

    An kuma yanke wa wanda ake tuhuma na uku hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

    Gwamnatin Jihar Kano ce ta gurfanar da mutanen uku kan zarge-zargen hada baki wajen aikata laifi, kisan kai da kuma ɓoye laifi.

    Da take yanke hukunci, mai shari’a Fatima Adamu ta Kotun lamba ta 18 da ke titin Miller Road, ta ce ɓangaren masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Lauya Salisu Muhammad Tahir ya gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa waɗanda ake zargin.

    Kotun ta samu Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da laifin kashe Alhaji Dahiru, wani mazaunin Yankusa, bayan daba masa wuƙa.

    Har ila yau, kotun ta same su da laifin haɗa baki da Sadik Sanusi, wanda ake zargi ya yi amfani da babur mai ƙafa uku wajen kai su wurin da suka ƙona gawar mamacin.

    Masu gabatar da ƙarar sun ce waɗanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a wani yunƙuri na ƙwace takardun mallakar fili na mamacin.

  7. Mutum hudu sun mutu a wani harin bam a Colombia

    Akalla Mutum huɗu sun mutu sakamakon wani harin bam a Kolombiya, ciki har da jariri mai watanni biyu.

    Hukumomin yankin sun ce an ɗora ababen fashewar ne a kan wata babbar mota, kuma bam ɗin ya tashi ne a kusa da wani sansanin soji da ke garin Planadas a yammacin ƙasar.

    Har yanzu ba a san waɗanda suka kai harin ba, amma wannan fashewa ita ce ta baya-bayan nan cikin jerin hare-haren ta’addanci da suka faru tun bayan hawa mulkin sabon shugaban ƙasar mai ra’ayin mazan jiya, Aberlardo de la Espriella.

    Ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya masu ra’ayin rikau sun bayyana cewa su ne suka kai wasu daga cikin hare-haren da suka gabata, amma ana ɗora alhakin wasu hare-haren kan masu safarar muggan ƙwayoyi.

  8. Falasɗinawa huɗu sun mutu a hare-haren Isra'ila

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce aƙalla Falasɗinawa huɗu ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a wurare daban-daban.

    Ma’aikatan lafiya sun ce mutanen sun mutu ne a Khan Younis, Al-Mussadar, da kuma unguwar Tel Al-Hawa da ke cikin birnin Gaza.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari ne kan mayaƙa a yankin, amma ba su bayar da ƙarin bayani ba.

    A makonnin baya-bayan nan, Isra'ila ta ƙara tsananta hare-harenta duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma fiye da shekara guda da ta gabata, inda take zargin Hamas da sake ɗaukar makamai. Hamas dai ta musanta wannan zargi.

    Jami'ai a Gaza sun ce fiye da Falasɗinawa 1,500 ne Isra'ila ta kashe tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar.

  9. Yadda aka tarbi sojan da ya yi shekaru 28 yana zagaya duniya a ƙafa

    Tsohon sojan Birtaniya ya isa garinsu na Hull da ke arewacin Ingila bayan ya kammala wata tafiya ta shekaru ashirin da takwas yana zagaya duniya a ƙafa, wadda ya fara daga Kudancin Amurka.

    Karl Bushby, mai shekaru 57, ya samu tarba daga ɗumbin jama’a, ya gabatar da jawabi gabannin shiga inda zai kammala tafiyar wato gidan mahaifiyarsa.

    Ya ce shekara 20 ke nan, ga mu a nan, a matakin ƙarshe na kammala tafiyarnan ba na jin akwai wurin da ya fi cancantar na kammala kamar wurin nan.

    Firaministan Birtaniya Andy Burnham ya taya shi murna kan wannan gagarumar nasara.

    A cikin tafiyarsa mai tsawon mil 31,000, ya fuskanci tsaiko na tsawon shekaru goma sha uku.

  10. An samu ƙaruwar cin zarafin ƴan adawa a Zambiya - Human Rights Watch

    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi gargadin cewa an samu ƙaruwa wajen murƙushe masu adawa da gwamnati a ƙasar Zambiya tun bayan zaɓen watan Agusta.

    Wakilin BBC ya ce Human Rights Watch ta ce hukumomi sun zafafa dabarun murkushe 'yan adawa, da tsare su ba bisa ƙa'ida ba, da azabtarwa yawanci ana zarginsu da aikata muggan laifuka, an kuma soke fasfo na masu sukar gwamnati shida yayin da suke ƙasashen waje.

    Human Rights Watch ta yi kira da a gudanar da bincike kan samamen da ‘yan sanda suka kai gidan wani jagoran ‘yan adawa, inda aka harbe wani tsohon minista har ya mutu.

  11. Za mu buɗe Hormuz cikin kwana biyu idan Amurka ta yarda da sharaɗinmu

    Iran ta ce ba za a cimma wata yarjejeniya ba, kuma ba za a sake buɗe mashigar Hormuz ko tabbatar da tsaronta ba, har sai Amurka ta kawo ƙarshen killacewar ruwa da jiragen yaƙinta suka yi, sannan kuma aka aiwatar da halastattun buƙatun Iran."

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Esmail Baghaei ya ce tubalin tattaunawa da Amurka shi ne shirin kare muradun Iran wanda yanzu aka takaita shi kuma "a shirye yake a fara aiwatar da shi cikin kwanaki biyu."

    Da yake magana kan wasiƙar da Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya aika, Mista Baghaei ya faɗa sakataren tsaron Iran Mohsen Rezaei cewa wannan wasiƙa "ba ta ƙunshi wata sabuwar manufa ba, kuma tushen duk wata mu’amala ta kai-tsaye ba tare da ganawa ba ta hanyar masu shiga tsakani shi ne wannan shiri mai maki bakwai na Iran.

    Mista Baghaei ya ci gaba da cewa sakataren majalisar tsaron Iran ne kawai zai mayar da martanin wasiƙar.

  12. Isra'ila ta janye sojojinta daga Hebron

    Sojojin Isra’ila sun ce sun janye dakarunsu daga birnin Hebron bayan kammala wani samamen tsaro na kwanaki goma a Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    An ruwaito cewa fiye da Falasɗinawa dubu uku ne suka rasa matsugunansu sakamakon wannan samame, wanda ya faru sakamakon kashe wasu sojojin Isra’ila biyu a wani hari da ‘yan bindigar Falasɗinu suka kai makonni biyu da suka gabata.

    Sojojin Isra’ila sun kuma kakaba ƙawanya a birnin da yankunan da ke kewaye da shi.

    Rundunar sojin ta ce tana ƙoƙarin gano da kuma cafke mayaƙan da take zargin suna da hannu a harin da aka kai kan sojojinta.

  13. Trump ya sake barazanar kai wa Iran mummunan hari

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazanar far wa Iran da yaƙi.

    Da yake jawabi a wani taron yaƙin neman zaɓen tsakiyar wa'adinsa, shugaban na Amurka ya ce dalilin kawai da ya sa har yanzu ba a kawo ƙarshen yaƙin da Iran ba shi ne saboda yana son kauce wa ƙarin asarar rayuka.

    ''Dalilin kawai da ya sa har yanzu ba mu gama da Iran ba shi ne saboda ina son yin sassauci da su. Idan zai yiwu, ina son ceton mutane daga mutuwa. Amma daga ƙarshe akwai lokacin da ya zama dole mu kai mummunan hari," in ji shi.

    Kalaman na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin sake farfaɗo da tattaunawa tsakanin Tehran da Washington, wadda Qatar ke shiga tsakani a cikinta.

    Wannan na zuwa ne bayan bayan wata wasiƙa da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya aika wa Mohsen Rezaei.

    Yakin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran na daga cikin manyan batutuwan da suka shafi zaɓukan tsakiyar wa'adin mulki na Amurka, waɗanda za su fara cikin ƙasa da sa'o'i 48.

    Sakamakon waɗannan zaɓuka na iya yin tasiri kai tsaye kan manufofi da matakan da gwamnatin Shugaba Trump za ta ɗauka.

  14. Na gode wa hukumomin Saudiyya da suka ba ni damar shiga Ka'aba - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda ba shi damar shiga ɗakin Ka'aba da ya ce sun yi a lokacin ziyarar Ibadar Umara da yake yi a ƙasar.

    Yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala ibadar, Shugaba Tinubu ya ce karramawa ce da bai zai taɓa mantawa da ita ba.

    ''Na goda wa Sarki Saudiyya da Yarima mai jiran gado bida karramar da suka nuna min, wanda har aka ba ni damar shiga cikin ɗakin Ka'aba'', in ji Shugaban na Najeriya.

    Shugaban na Najeriya ya ce gina makomar ƴan Najeriya masu tasowa na daga cikin manyan ƙudurorinsa.

    ''Idan ma bu gina wa yaranmu makomai mai kyau ba, wanda za su amfana nan da shekara 50 , ta yaya za a riƙa tunawa da mu'', in ji shi.

  15. Iran ta yi wa Amurka sabon barazanar yaƙi

    Kakakin rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya ce idan wani sabon yaƙi ya ɓarke, "yankin da za a yi faɗan ba zai takaita ga Yammacin Asiya kaɗai ba."

    Ya ƙara da cewa, "Kayan aiki da cibiyoyi da sojoji da muradun Amurka, a duk inda suke na iya zama wuraren da za a kai wa hari."

    Da yake magana kan ƙarfafa ayyukan soji da sabunta jerin wuraren da ake niyyar kai wa hari, Akraminia ya ce wani sabon yaƙi na iya zama "mai tsawon lokaci fiye da na baya."

    Kakakin sojin ya kuma ce: "An fara tsarin sauya manufofin kare kai na Iran zuwa manufofin kai hari tun da daɗewa, kuma an nuna hakan a fili a lokacin yaƙin da ya gabata."

    Shafin intanet na hukuma na Mojtaba Khamenei ya ruwaito cewa an umarci kwamandojin Iran su da su mayar da martani "nan take kuma ba tare da la’akari da iyakokin ƙasa ba" ga duk wata barazana da abokan gaba za su iya yi.

    An kuma rawaito jagoran Jamhuriyar Musuluncin yana cewa idan aka sake kai wa Iran hari ta fuskar soji ko kuma "ta'addanci", ita ce za ta ƙayyade lokaci da sharuɗan kawo ƙarshen rikicin.

  16. Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum tara a Amurka

    Wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a wata unguwa da ke jihar Florida ta Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum tara da ke cikinsa.

    Jirgin samfurin Learjet 60 na kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Bahamas ne bayan ya tashi daga jihar Texas, a lokacin da ya faɗo a yankin Palm Beach County, kafin ya kama da wuta.

    Sakataren kula da harkokin sufuri na Amurka, ya bayyana lamarin a matsayin wata mummunar masifa, yana mai cewa jami'ai na ci gaba da sanya ido sosai kan abubuwan da suka faru.

    Har yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin hatsarin jirgin ba, kuma ana ci gaba da bincike kan abin da ya haddasa shi.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, mande tushen aiki ko da nasara na tsoronki.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.