Jirgin dakon mai ya taka nakiya a tsibirin Ghanam da ke Iran - IRGC
Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar da cewa ɗaya daga cikin jiragen dakon mai biyu da ke ƙoƙarin wuce mashigar ruwa ta Hormuz a ɓoye, ba tare da izini ba, ya taka nakiya, yayin da ɗayan ya juya baya.
Rundunar sojin ruwan IRGC ta ce jirgin dakon man ya fashe ne bayan ya taka nakiya a arewacin tsibirin Ghanam, yayin da wani jirgin da ke tafiya tare da shi ya tilasta masa komawa baya.
Tsibirin Ghanam yana bakin mashigar ruwa ta Hormuz, kuma yana ƙarƙashin ƙasar Oman.
A safiyar yau, IRGC ta kuma sanar da cewa wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-16 ya ja da baya bayan da tsaron Iran ya yi masa harbin gargaɗi.
Rundunar ta ce jirgin ya matso kusa da yankin Iran da ke kudu maso gabashin tsibirin Hengam ne a lokacin da yake raka jiragen ruwan da take zargi da laifi, tare da ba su kariyar sama.
Sanarwar IRGC ba ta fayyace ko waɗannan al'amura biyu suna da alaƙa da juna ba.