Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutum biyu da aka sace a jihar Taraba
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta ƙarkashin Operation Whirl Stroke sun ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a yankin Lande Jessi da ke karamar hukumar Lau a jihar Taraba.
Sojojin sun bayyana cewa sun ƙaddamar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari ƙauyukan Tashan Musa da Barkindan Fulani, inda suka sace mutane biyu tare da kwashe kayan abinci.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Yulin 2026.
Bayan gudanar da bincike da sintiri a wurare daban-daban, dakarun sun samu nasarar ceto mutanen biyu da aka sace waɗanda aka ce sun shafe kusan mako guda a hannun masu garkuwa da mutanen kafin a kuɓutar da su.
Rundunar ta ce nasarar aikin na nuna ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama'a tare da ci gaba da yaƙi da dukkan nau'ikan laifuffuka a faɗin kasar.