Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya yi farin ciki da umarnin da Babban Sufeton Ƴansandan Najeriya, Olatunji Disu ya bayar na gudanar da bincike kan ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
A ranar Juma’a ne IGP Disu ya ba da umarnin a yi bincike kan zargin da wani mai suna Muhammad Musa Kamarawa, ya yi na cewa wasu jami’ai biyu, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba, suka kashe Dadiyata da wani mutum mai suna Saminu S/Fada Gusau, a Kaduna.
Musa ya yi iƙirarin cewa "a gaban idonsa aka kashe Dadiyata". Tuni batun ya ɗauki hankali a shafukan sada zumunta.
A wani sako da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce yana kwarin gwiwa kan matakin da IGP ya ɗauka na binciken zargin da ake yi cewa ƴansandan biyu na da alaƙa da sace ɗan gwagwarmayar.
“Tun da aka sace shi a shekarar 2019, ni da ƴan'uwa muke ta addu’a tare da kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a bacewarsa a gaban kotu,” in ji Kwankwaso.
Ya bukaci ƴansanda su sa ido kan jami’an da ake zargi don hana yin katsalandan a binciken, inda ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an biya iyalan Dadiyata diyya kan halin da aka jefa su.
Dadiyata fitaccen mai sharhi a shafukan sada zumunta da ya yi ƙaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Kano ta wancan lokacin ƙarƙashin gwamna Abdullahi Ganduje.
A watan Agustan 2019 ne wasu da ba a san ko su waye ba suka sace shi daga gidansa da ke Barnawa, Kaduna, kuma har yanzu ba a san inda yake ba bayan shekaru bakwai.