Cutar Ebola da ke yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta bazu zuwa yankunan kiwon lafiya 47 a faɗin larduna biyar na Adja da ke lardin Ituri.
Alƙaluman da aka fitar ranar 19 ga Yuli sun nuna cewa an tabbatar da mutum 2,423 sun kamu da cutar, yayin da mutum 967 suka mutu, abin da ya sa adadin mace-macen ya kai kashi 39.9 cikin 100.
A cikin sa'o'i 24 da suka gabata kaɗai, an samu sabbin mutum 79 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutum 37, inda mafi yawan su suka fito daga lardin Ituri.
Yankunan Bunia, Nizi, Rwampara da Adja ne suka fi samun sabbin waɗanda suka kamu da cutar.
Hukumomi sun ce ana bin diddigin kashi 81.1 cikin 100 na waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar, sai dai har yanzu akwai giɓi musamman a lardin Haut‑Uélé.
An ayyana ɓullar cutar ne a ranar 15 ga Mayu, kuma ƙwayar cutar da ake kira da Bundibugyo ebolavirus ce ke haddasa ta.
Hukumomin lafiya sun ce matsalar tsaro, yawan zirga-zirgar jama'a da kasuwancin kan iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu na ƙara wahalar daƙile yaɗuwar cutar.
Sun kuma yi gargaɗin cewa wajibi ne a ƙara sa ido da matakan kariya domin daƙile annobar.