Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 02/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 02/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. MURIC na zargin gwamnatin Najeriya da nuna wa Musulmai bambanci

    Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnatin Najeriya da nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci a ƙasar.

    MURIC ta yi wannan kiran ne bayan ta samu rahotannin cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar gina wani katafaren coci da za kashe wa naira biliyan 25 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    A wata sanarwa da MURIC ta aike wa BBC, shugaban ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya kuma nuna takaici kan yadda gwamnatin ta tallafa wa waɗanda rikici ya shafa a jihar Filato da naira biliyan 2, ba tare da ta yi irin hakan a jihohin Sakkwato, Borno, Kebbi da Zamfara ba, da su ma suke fama da matsalolin tsaro.

    "Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da ya sa ake nuna wannan fifiko. Musulmai a Najeriya ba su cancanci haka ba...," in ji sanarwar.

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin Najeriyar ta ware irin waɗannan kuɗaɗe na kimanin naira biliyan 25, da kuma fili ga Musulman ƙasar domin su ma su gina katafaren masallaci a filin jirgin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa: "Wannan haƙƙin mu ne. Kuma ya kamata a ba mu."

  2. Gwamnan Bauchi ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APM

    Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APM.

    Gwamnan ya sanar da matakin ne a fadar gwamnatin jihar a yau asabar, inda shugaban APM ya karɓe shi tare da ba shi katin shiga jam'iyyar.

    Rahotanni sun ce ya fice ne tare da wasu mambobin jam'iyyar PDP masu goyon bayan shugabancin Tanimu Turaki.

    Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki da gwamnan na jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi.

    Dama dai a hirarsa da BBC, gwamnan ya ce, tun bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan rikicin PDP ya ƙuduri aniyar ficewa daga jam’iyyar.

    Kafin sauya sheƙar tasa, shi ne shugaban gwamnonin jam'iyar PDP

  3. Kungiyar Fulani ta ja hankalin jagororin arewa su haɗa kai don magance matsalar tsaron yankin

    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kullen Allah ta yi kira ga jagororin arewacin Najeriya su haɗa kai domin magance matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Khalil Mohammed Bello ya fitar, ya ce matsalolin tsaron da yankin arewa maso yammacin ƙasar da arewa ta tsakiyar Najeriya ke fuskanta na haifar da asarar dukiya mai ɗimbin yawa, lamarin da ya shafi miliyoyin iyalai.

    Haka nan ƙungiyar ta nuna matuƙar da damuwarta kan rohoton ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International da ta ce sojoji sun tsare makiyaya da dama tare da iyalansu a wani sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihar Kwara, lamarin da Amnesty ta ce ya haifar da mutuwar fiye da mutum 150, galibinsu mata da ƙananan yara.

    "Arewacin Najeriya na da ƙarfi da ikon da zai hana faruwar waɗannan matsaloli na tsaro da ke addabar yankin", in ji sanarwar.

    "Yanki ne da ke da tsoffin shugabannin ƙasa da tsoffin manyan sojoji da manyan sarakunan gargajiya da jiga-jigan 'yansiya, waɗanda in dai za su yi aiki tare za a samu maganin wannan matsala", kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Yankin arewacin Najeriya ya jima yana fama da matsalolin tsaro, waɗanda ke haifar ƙaruwar tarin matsalolin rayuwa a yankin.

    Kullen Allah ta ce bai kamata yankin ya tsaya jiran taimakon gwamnatin tarayya wajen tunkarar matsalolin yankin ba.

    Ƙungiyar ta yi kiran amfani da hanyoyin sulhu domin warware matsalolin, inda ta bayar da misali da Birnin Gwari a jihar Kaduna da ta ce sakamakon sulhun aka samu zaman lafiya.

  4. 'Dakarun juyin juya halin Iran 14 sun mutu a ƙoƙarin kwance nakiya'

    Kamfanin dillancin labarai na Fars a Iran ya bayar da rahoton cewa dakarun juyin juha halin ƙasar 14 ne suka mutu a daren da ya gabata sakamakon fashewar wata nakiya da aka dasa lokacin yaƙin ƙasar da Amurka da Isra'ila.

    A cewar Fars, ofishin hulda da jama'a na rundunar IRGC, a lardin Zanjan inda lamarin ya faru, ya ce dakarun rundunar 14 ne suka mutu, yayin da biyu suka jikkata a lokacin ƙoƙarin dakarun rundunar na kwance nakiyar.

    Mataimakin gwamnan Zanjan ya ce za a rufe duka ma'aikatun gwamnati da bankuna a lardin a ranar Lahadi domin jana'izar dakarun.

  5. An kama sojojin Mali da dama da hannu a hare-haren makon da ya gabata

    Kotun sojin Mali ta ce an kama sojojin ƙasar da dama kan zargin hannu a hare-haren ƴanbindiga masu alaƙa da al-Qaeda da ƴantawayne Tuareg a makon da ya gabata a faɗin ƙasar.

    Masu shigar da ƙara sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma tuni binciken ya gano hannun wasu sojojin ƙasar da kuma waɗanda suka yi ritaya wajen kisat hare-haren.

    Cikin wata sanarwa da sojojin mulkin ƙasar suka karanta a gidan talbijin na ƙasar, ba su bayayana adadin sojojin da ke da hannu a hare-haren ba, amma ta tabbatar da ƙarin kame cikin rundunar sojin ƙasar, yayin da ake ci gaba da bincike.

    Haka ma ana zargin 'yansiyasar ƙasar, ciki har da jagoran adawar ƙasar da ke zaman gudun hijira a wajen ƙasar, Oumar Mariko.

    A lokacin hare-haren na makon da ya gabata an kashe ministan tsaron kasar.

    Yanzu haka dai 'yanbindigar sun ce suna shirin yi wa Bamako, babban birnin ƙasar ƙawanya, yayin da rahotonnni suka ce tuni mayaƙan sun fara kafa shingayen bincike a faɗin birnin.

  6. Zan tsaya takarar Sanata a zaɓen 2027 - Gwamnan Bauchi

    Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya ce zai tsaya takarar sanata a zaɓen 2027 da ke tafe.

    Cikin hirarsa da BBC, gwamnan, wanda ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu, ya ce bisa kiraye-kirayen magoya bayansa, zai tsaya takarar sanatan Bauchi ta Kudu a zaɓen mai zuwa.

    ''Zan nemi kujerar ne domin ƙara wa jam'iyyarmu ƙwari a jihar Bauchi, musamman ga ɗan takarar gwamna'', in ji shi.

  7. OPEC ta amince ta ƙara yawan man da take haƙowa

    Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta amince kowace ƙasa ta ƙara yawan man da take haƙowa da ganga 188,000 a kowace rana.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ambato wasu majiyoyi masu kusanci da ƙungiyar na bayyana hakan gabanin taron ƙungiyar da aka shirya yi ranar Lahadi.

    Matakin na zuwa ne bayan ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da ficewa daga ƙungiyar.

    A watan da ya gabata ne ƙungiyar ta amince da ƙara yawan man da ƙasashen ƙungiyar ke haƙowa da ganga 2026,000 a kowace rana.

    Galibi ƙungiyar kan ƙara yawan man da take haƙowa a duk lokacin da aka samu ƙarancin mai a kasuwannin duniya.

    Rufe mashigar Hormuz sakamakon yaƙin Iran na daga cikin abubuwan dake haifar da ƙaranci da tsadar mai a kasuwannin duniya a halin yanzu.

  8. Za mu nemi jam'iyyar da za mu koma don nemar wa kanmu mafita - Gwamnan Bauchi

    Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya ce yana neman jam'iyyar da zai koma tare da magoya bayansa.

    Matakin na zuwa ne bayan da a cikin makon nan Kotun Kolin ƙasar ta haramta shugabancin jam'iyyar tsagin Tanimu Turaki, wanda Bala Muhammad ɗin ke ciki.

    A hirarsa da BBC, Bala Mohammed ya ce a matsayinsu na masu biyayya ga dokokin ƙasa sun amince da hukuncin kotun, don haka za su nemi sabuwar jam'iyyar da za su koma domin mafitarsu.

    ''Kowa ya san yadda muka jajirce kan wannan matsayi, amma kodayake ba mu samu abin da muke so ba, saboda kotu ba ta yarda da taron da muka yi a Ibadan ba, su ma ba su samu abin da suke so ba'', in ji shi.

    Bala Mohammed ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike da zame wa PDP ''dagwalo'', inda kuma ya ce ya yi nasarar yin hakan.

    ''Don haka tun da babu lokaci, dole ne mu yi amfani da hikima, mu samu wata jam'iyyar mai tsafta domin sanya magoya bayanmu a ciki don su tsaya takara a zaɓe mai zuwa'', in ji shi.

    Ya ce tuni ya samo jam'iyyar da magoya bayansa za su koma, domin su samu zarafin tsayawa takara a zaɓukan da ke tafe.

  9. Nato ta tuntuɓi Amurka don jin bahasin janye dakaru 5,000 daga Jamus

    Ƙungiyar tsaro ta Nato ta bayyana cewa ta tuntuɓi Amurka domin samun fahimtar juna kan matakinta na janye dakarunta 5,000 daga Jamus.

    Kakakin ƙungiyar, Alison Hart ta bayyana a shafinta na X cewa ''muna tattaunawa da Amurka don samun fahimtar juna kan matakinta na janye sojojinta daga Jamus''.

    A ranar Juma'a ne ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta bayyana cewa sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya bayar da umarnin janye dakarun ƙasar 5,000 daga Jamus cikin shekara ɗaya.

    Adadin ya kai kashi 15 cikin 100 na sojojin Amurka da ke Jamus, wadda mamba ce a ƙungiyar tsaro ta Nato.

  10. Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum da shida cikin mutanen Ngoshe da aka sace

    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kuɓutar da wasu mata uku da yara uku cikin mutanen Ngoshe da mayaƙan Boko haram suka sace a farkon watan Maris.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operations Hadin Kai mai yaki da Boko Haram, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar ya ce sojojin sun kuɓutar da mutane shida a garin Amuda da ke tsakanin garin Ngoshe da Gava lokacin da suke sintiri.

    Sanarwar ta ƙara da cewa mayaƙan sun buɗe wa sojojin wuta da nufin kwace mutanen, sai dai sojojin mun mayar da martani cikin ƙwarewa lamarin da ya tilasta wa mayaƙan janyewa zuwa tsaunukan Mandara.

    Laftanal Kanal Sani Uba ya ce cikin waɗanda aka kwato har da wata da aka tilasta wa auren ɗaya daga cikin kwamandojin mayaƙan.

    Tuni dai aka sada mutanen da iyalansu bayan yi musu gwajin lafiya a sansanin soji da ke jihar Borno.

    Sojojin sun kuma buƙaci al'umma su rika taimaka musu da bayanan sirri domin daƙile hare-haren mayaƙan na Boko Haram

  11. Buɗe mashigar Hormuz ba zai daidaita al'amura nan take ba - Starmer

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi gargaɗin cewa tattalin arzikin ƙasarsa ba ''zai koma daidai ba'', ko da an sake buɗe mashigar Hormuz.

    Yayin wata hira da BBC, Mista Starmer ya ce halin da ake ciki yanzu na buƙatar sabbin salo, domin tunkarar matsalar tattalin arziki da aka riga aka samu sakamakon yaƙin.

    Da aka tambaye game da yiwuwar samun hauhawar farashi sakamkon tashin farashin man fetur, firaministan ya ce gwamnati ba za ta kya hana aukuwar hakan ba.

    ''Muna fuskantar yaƙi har guda biyu'', kamar yadda ya bayyana.

  12. Hare-haren Iran sun lalata mafi yawan cibiyoyin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya - Rahoto

    Wani sabon rahoto da kafar yaɗa labaran CNN ta Amurka ta fitar, ya ce hare-haren ramuwar gayyar Iran sun lalata 16 cikin cibiyoyin sojin Amurka 19 da ke yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda jaridar Indepenpent ta Birtaniya ta ruwaito.

    Wani mutum da CNN ta zanta da shi ya ce ''bai taɓa ganin abu irin wannan ba a baya''.

    Majiyar ta ƙara da cewa an yi amfani da sabbin fasahohin makaman yaƙi na zamani wajen ƙaddamar da hare-haren

  13. Amurka ta sayar da makaman kusan dala biliyan 9 ga ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da sayar da makaman soji da kuɗinsu ya kai dala biliyan 8.6 ga ƙawayenta ƙasar da ke Gabas Tsakiya, da suka haɗa da Isra'ila da Qatar da Kuwait da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Matakin na zuwa ne yayin da ake cikin mako na uku da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

    Daga cikin waɗannan makaman an sayar wa Qatar na fiye da dala biliyan 4, yayin da aka sayar wa Kuwaita na dala biliyan 2.5, sai kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ta samu na dala miliyan 147.

  14. Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane da take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asiri

    Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu fursunoni biyu kan zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri.

    Ma'aikatar shari'ar ƙasar, wadda ta zartar da hukuncin, ta ce kotun kolin ƙasar ce ta tabbatar da hukuncin.

    Ma'aikatar ta ce ɗaya daga cikin mutunen an same shi da laifin haɗa kai da hukumar leƙen asirin Isra'ila Mossad, inda ya riƙa aika mata da muhimman bayanan tsaron ƙasa a lokacin yaƙin ƙasashen.

    Haka kuma ma'aikatar ta ce ɗayan kuma an same shi da laifin zirga-zirga a wurare masu muhimmanci na tsaron ƙasar.

    Inda ta ce ya riƙa aika wa wani jami'in Mossad muhimman bayanai game da wuraren ciki har da Natanz.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

  15. Trump ya sanar wa Majalisar Amurka kawo ƙarshen hare-hare kan Iran

    Shugaba Trump na Amurka ya rubuta wata wasiƙa ga shugabancin majalisun dokokin Amurka da a ciki yake sake jaddada abin da ya kira ''an kawo ƙarshen hare-hare kan Iran'', wanda hakan ke nufin ba ya buƙatar amincewar majalisar kan yaƙin.

    Dokokin Amurka dai sun yi tanadin cewa dole sai majalisaun dokokin ƙasar sun amince da duk wani matakin soji da ya wuce kwana 60.

    Shugaba Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ciki a yanzu ta kawo ƙarshen hare-hare a watan da ya gabata.

    Duk da wannan yarjejeniya dai ƙasashen biyu na hana jiragen ruwa zirga-zirga a kewayen Tekun Fasha.

    Tun da farko dai Mista Trump ya ce bai ji daɗin buƙatun da Iran ta gabatar wa Pakistan na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ba.

  16. Amurka za ta janye dakarunta 5,000 daga Jamus

    Amurka ta ce za ta janye sojojinta 5,00 daga Jamus sakamakon saɓanin da ke ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu.

    A baya-bayan nan an samu saɓa i tsakanin Shugaba Trump da shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz kan batun yaƙin Iran.

    Ma'aikatar tsaron AMurka ta ce za a kwashe sojojin ne cikin wata shida zuwa 12 masu zuwa.

    Shugaba Trump ya soki Mista Merz da sauran shugaban ƙasashen ƙungiyar Nato kan ƙin tura sojojinsu domin buɗe mashigar Hormuz.

    A ranar Litinin ne shugaban gwamnatin Jmaus ɗin ya ce shugabancin Iran na kunyata Amurka ta hanya sa wakilan Amurak su tashi takanas har Pakistan, domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin amma su koma ba tare da wani sakamako ba.

    A cikin wannan mako ne dai Mista Trump ya sanar da janye wasu sojojin ƙasarsa daga ƙasashen Italiya da Sifaniya saboda yaƙin na Iran

  17. Barkanmu da safiya

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.