Sojojin Najeriya sun ce sun ceto mata da yara 360 da aka sace a Borno
Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Hadin Kai sun ceto kimanin mata da yara 360 da '’yan ta’adda' suka sace daga ƙauyen Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, kakakin rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce aikin ceton ya gudana ne a ranar 6 ga Yuni, tare da haɗin gwiwar sauran runduna ta Musamman a yankunan da ke kusa da Dutsen Mandara.
Ya ce sojojin sun gudanar da aikn ne da dabarun da suka rikita sansanonin ’yan ta’adda, wanda hakan ya ba su damar shiga da kuma kuɓutar da mutanen cikin nasara.
A cewarsa, mutanen da aka ceto an sace su ne a harin da aka kai Ngoshe a ranar 3 ga Maris, 2026.
Sai dai ya ce an samu asarar rayukan jarirai biyu yayin aikin ceto, sakamakon wahalar hanya da yanayin da aka fuskanta yayin fitar da su zuwa wuri mai aminci.
Ya ƙara da cewa dukkan waɗanda aka ceto an yi musu gwaje-gwajen lafiya nan take, inda aka kwantar da wasu a Asibitin Gwamnati da ke Gwoza domin ƙarin kulawa, yayin da aka ba su abinci da ruwa kafin a tura su wurin da ake kula da su na wucin gadi.