An ceto sauran mutanen da aka sace daga gidan marayu a jihar Kogi
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto yara bakwai da manya biyu da aka sace daga wani gidan marayu a jihar Kogi a watan da ya gabata.
Cikin wata sanarwar da ta fitar, runduar sojin ta ce an ceto su ne a wani aiki da jami'an tsaro suka yi.
Satar mutane domin neman kuɗin fansa dai ya zama ruwan dare a Arewa ta Tsakiyar Najeriya, inda ƴan bindiga ke yawaita kai hari kan makarantu da kuma ƙauyuka.