Messi da Ronaldo: Hamayyar da ta kawo sauye-sauye a ƙwallon ƙafa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A shekarar 2007 fitaccen ɗan ƙwallon tawagar Brazil, Kaka ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon kafa na duniya na Fifa, wato FIFA Player of the Year, amma wani abin kunya da ya faru a dandalin bayar da ƙyautar ne ya zama abin da ya bazu sosai, kuma a lokacin aka fara ganin wata gagarumar hamayya tsakanin wasu fitattun ƴan wasan tamaula biyu.

A lokacin, matashi Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun zo na biyu da na uku a jerin masu ƴan takarar ƙyautar. Sai dai fitaccen ɗan wasan Brazil, Pelé, ya yi kuskure lokacin da yake ba da ƙyautar, sai ya miƙa wa Ronaldo ƙyautar a matsayi na biyu maimakon Messi a taron da aka gudanar a Zurich Opera House.

Shugaban FIFA na lokacin, Sepp Blatter, ya shiga tsakani, inda ya roƙi ƴan wasan biyu su yi musanya ƙyautukan, yayin da dukkansu suka nuna rashin jin daɗi a fili.

A cikin shekara 10 da suka biyo baya, Messi ko kuma Ronaldo ne suka mamaye ƙyaututtukan Ballon d'Or da na FIFA. A hakika, tun daga 2007, ƙyaututtuka 20 cikin 29 na gwarzon ɗan wasan Turai sun lashe ne a tsakanin ɗan wasan Argentina da na Portugal.

A tsakaninsu sun kusan cin ƙwallo 2,000 a rayuwarsu ta sana'ar taka leda, kuma idan ka haɗa da kofuna 85 da suka lashe a tsakaninsu a matakin kasa da ƙungiyoyi da lambobin yabo da suka samu da tarihin da suka kafa a ƙwallon kafa, ya zama wajibi a jinjina da ƙwazon da suka yi.

Hamayyar da ke tsakaninsu ta zama alamar ƙwallon ƙafa a cikin shekara kusan 20 da suka gabata, inda ta zarce iyakokin ƙungiya da ƙasa da gasa, ta kuma sauya yadda ake kallon wasannin da tafka muhawa ko tattaunawa da kuma fahimtar yadda suke kalubalantar juna a tsakaninsu.

Burinsu na lashe kofuna da kafa tarihi da kokarin sai na fi abokin hamayyata, shi ne abu mai ƙyau da ya suka dunga tura juna da ta kai suna taka matakan da ba a taɓa gani ba a fannin ƙwallon kafa a tarihi.

Wata hamayya ce da ta zarce muhawarar "waye mafi girma a tarihi a tsakaninsu da suka haddasa, idan ka duba bajintar Messi sai fa ka kalli ƙwazon Ronaldo, hakan ya sa suka buɗe babi na musamman a tarihin ƙwallon ƙwallon kafa da har yanzu ba a kammala shi ba.

Mutane da dama suna kallon Messi da Ronaldo a matsayin ƴan ƙwallo masu halaye da salon wasa da suka sha bamban ƙwarai da gaske.

Ɗaya ƙwararren wajen yanka da zamiya da dabara da hangen nesa, ɗaya kuma ɗan wasa ne mai ƙarfi da hazaka da zuciyar taka leda. Ɗaya ana kallonsa a matsayin haziki mai natsuwa, ɗayan kuma a matsayin mai cike da kwarin gwiwa da nuna kai. Haka kuma hamayyarsu ta haɗa tsakanin Barcelona ta Pep Guardiola da Real Madrid ta José Mourinho a lokacin, har ma tsakanin kamfanonin da suke yiwa talla wato Adidas da Nike.

Sai dai duk da cewa an gina labarin hamayyarsu ne a kan bambance-bambancen da ke tsakaninsu, akwai abubuwa masu yawa da suka yi kama da juna tun lokacin da suke ƴan ƙanana.

Dukkaninsu sun taso ne daga iyalai marasa galihu. Sun bar gidajensu tun suna yara domin neman cika burinsu a fannin ƙwallon ƙafa—Messi ya bar Argentina zuwa Barcelona yana da shekara 13, yayin da Ronaldo ya bar tsibirin Madeira zuwa Lisbon yana da shekara 12. Dukkaninsu kuma sun sha fama da kewar gida bayan rabuwa da iyalansu.

Amma abin da suka yi kama da juna, shi ne ƙwazon da suke da shi na samun nasara da sa ƙwazo a koda yaushe ba tare da nuna gazawa ba. Tun suna matasa suka fara gina sunansu a matsayin fitattu kuma hazikan ƴan ƙwallo masu baiwa ta musamman.

A daidai wannan lokaci kuma a Ingila, matashi Ronaldo ya rattaba hannu a kan yarjejeniya da Manchester United, bayan da ya koma Old Trafford daga Sporting CP.

Daga nan a shekarar 2008, lokacin wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai (Champions League). Manchester United da Barcelona suka haɗu. Ronaldo da Messi shi ne karon farko da suka fara fuskantar juna a wani babbban mataki a duniya, Wannan ne ya zama farkon hamayya da za ta mamaye duniyar ƙwallon ƙafa na tsawon shekaru masu yawa.

Dukkansu sun taka rawar gani a lokacin da ta kai mabiya ƙwallon kafa suka fara muhawara kan wane ne ya fi wani tsakanin Messi da Ronaldo, kuma har yanzu a kan batun ake.

Bayan da Cristiano Ronaldo ya koma Real Madrid a shekarar 2009 kan kuɗi mafi tsada a duniya a lokacin, fam miliyan 80, ya sanya shi da Lionel Messi suka faɗaɗa hamayya a tsakaninsu da ta shafi Barcelona da kuma Real Madrid.

Sai dai a lokacin da Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus a 2018, shi da Messi sun riga sun lashe ƙyautar Ballon d'Or sau biyar-biyar.

A cikin shekara tara da suka yi tare a Sifaniya, Ronaldo ya zura ƙwallaye 450 a wasa 438 da ya buga wa Real Madrid, yayin da Messi ya ci ƙwallaye 471 a wasa 476 da ya yi wa Barcelona.

Wata gagarumar hamayya ce da ta ɗauki hankalin duniya. Barcelona da Messi sun fi samun nasarori a La Liga ta Sifaniya, amma a Gasar Zakarun Turai (Champions League), Real Madrid da Ronaldo ne suka mamaye gasar.

A shekarar 2012, Ronaldo ya jagoranci Real Madrid zuwa lashe La Liga karo na farko cikin shekaru huɗu. Duk da haka, Messi ne ya sake ɗaukar ƙyautar Ballon d'Or karo na huɗu a jere, abin da ya tayar wa Ronaldo hankali sosai.

Daga baya kuma, Messi ya ƙara lashe huɗu daga cikin Ballon d'Or biyar da suka biyo baya, wanda hakan ya ƙara tsananta hamayya tsakanin manyan taurarin biyu da suka mamaye duniyar ƙwallon ƙafa tsawon fiye da shekara goma.

Ko da yake hamayyar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a Sifaniya ta zo ƙarshe lokacin da Ronaldo ya koma Juventus a shekarar 2018, amma ba a daina muhawara a duniya ba, kan wanene ya fi wani a tsakanin Messi da Ronaldo..

Daga baya Ronaldo ya sake koma Manchester United kafin ya koma inda yake taka leda a yanzu haka Al-Nassr ta Saudi Arabia. Messi kuwa ya koma Paris Saint-Germain, sannan daga bisani ya rattaba hannu a Inter Miami da ke gasar Major League Soccer ta Amurka, inda har yanzu yake taka leda.

Bayan tasirin da suka yi a Sifaniya da sauye-sauyen da suka yi zuwa sabbin ƙungiyoyi, ana ganin ba don bunkasa ƙwallon ƙafa kaɗai suka yi ba, har ma saboda dalilan kasuwanci da talla.

A shekarar 2018, lokacin da Ronaldo ya koma Juventus, an sayar da riguna 520,000 mai ɗauke da sunansa cikin sa'o'i 24 kacal. A 2021 kuma, Messi ya koma Paris Saint-Germain, inda aka sayar da riguna 150,000 cikin mintuna bakwai kacal.

Lokacin da Manchester United ta sake ɗaukar Ronaldo a 2021, kuɗin da aka samu daga sayar da rigunarsa ya kai fam miliyan 187, kusan ninki biyu na abin da aka samu daga rigunan Messi a PSG.

A dandalin Instagram, Ronaldo na da kusan mabiya miliyan 700, yayin da Messi ke da sama da miliyan 500. Hoto da ya samu yawan mabiya ko kuma (likes) a tarihin Instagram kuwa shi ne na Messi lokacin da yake ɗaga Kofin Duniya, wanda ya samu sama da miliyan 75 na likes.

Ta fuskar kuɗin shiga ma, Ronaldo ne ke gaba a ƙididdigar hukuma. Mujallar Forbes ta sanya ɗan wasan Portugal a matsayin mafi yawan kuɗin shiga a duniya karo na huɗu a jere, inda ya samu dala miliyan 300 (kimanin fam miliyan 223). Messi kuma yana matsayi na uku da dala miliyan 140 (kimanin fam miliyan 104).

Hamayyar tasu ta ƙara armashi saboda suna wakiltar manyan kamfanonin kayan wasanni biyu masu gogayya da juna. Messi yana tallata Adidas, yayin da Ronaldo ke tare da Nike.

Haka kuma, mutane da dama ba za su manta da shahararren hoton da aka ɗauka kafin gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar ba, inda aka nuna Messi da Ronaldo suna wasan dara a saman akwati na Louis Vuitton domin tallata sabon kamfen ɗin kamfanin.

Sai dai abu mafi muhimmanci shi ne, wannan labari bai ƙare ba tukuna. Idan har Argentina da Portugal suka haɗu a gasar Kofin Duniya a 2026, akwai yiwuwar duniya ta sake shaida babi na ƙarshe na ɗaya daga cikin manyan hamayyar da aka taɓa gani a tarihin ƙwallon ƙafa.

Za a fara gasar cin kofin duniya daga 11 ga watan Yuni a Amurka da Canada da Mexico, Messi da Ronaldo kowannen zai buga babbar gasar tamaula ta duniya karo na shida, watakila ta karshe da kowanne zai halarta.

Sai dai Messi ya lashe kofin duniya a 2022 a Qatar, kofin da Ronaldo ke fatan ɗauka a bana kenan. Shin ko burinsa zai cika kuwa kafin ya yi ritaya?