Inter Milan ta lashe Seerie A karo na 21 a tarihi

Lokacin karatu: Minti 1

Inter Milan ta lashe gasar Serie A karo na 21 a tarihi, bayan doke Parma da ci 2-0.

Inter da ke neman maki domin lashe gasar cikin wasanni uku da suka mata saura, ta samu nasarar jefa ƙwallaye biyun ne ta hannun Marcus Thuram da Henrikh Mkhitaryan wani abu da ya janyo shewa da farin ciki a filin wasa na San Siro.

Inter ta lashe gasar a baya a 2024, inta ta baiwa Napoli da ta lashe gasar a wancan lokacin tazarar maki 12.

Ɗan wasan gaban Faransa Thuram ne ya fara jefa kwallon a minitna 45 na farko bayan ƙara lokacin gabanin tafiya hutun rabin lokaci.

Sai da aka je mintina na 80 kafin Inter ta ƙara kwallo ta biyu inda Lautaro Martinez ya kwasowa Mkhitaryan kwallon shi kuma ya jefa ta raga.

An yi ta kunna wuta a filin wasan bayan kammala mintina 90, lokacin da kocin ƙungiyar Cristian Chivu ya shigo filin wasan domin taya juna murna, wanda ya lashe gasar sau uku lokacin da yake bugawa ƙungiyar.

Inter Milan ta ci kwallo 19 a wasanni shida da ta buga a baya, kuma ita aka fi sa ran za ta lashe gasar ganin ta ci wasa 26 cikin 35 da ta buga.