Me ya sa mata suka fi maza iya juya jari?

    • Marubuci, ویل اسمیل، فیل لیک و جس کار
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی‌بی‌سی
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani sabon bincike ya nuna cewa matan da ke zuba jarinsu a harkokin kasuwanci na samun riba fiye da yadda maza ke samu.

Sai dai wani rahoto ya nuna cewa kusan kashi ɗaya bisa huɗu ne kawai na mata a Birtaniya ke zuba jari, idan aka kwatanta da kusan kashi 40 cikin 100 na maza.

Mun yi nazari kan bayanan da ke dangane da waɗannan al'amura, waɗanda suka bayyana wasu bambance-bambance kan yadda maza da mata ke zuba jari da kuma yadda suke tunkarar harkar.

Tellery Evans ta fara tara kuɗi domin sayen gida ne lokacin da take da shekara 25. Bayan wasu shekaru, ta buɗe asusun ajiyar kuɗi na dogon lokaci da ake samun riba ta hanyar zuba jari.

A lokacin da ta kai shekara 33, ta tara fam 40,000, inda ta samu ƙarin fam 8,000 a matsayin riba daga zuba jarin.

"Na yi tanadin kuɗi sosai, kuma na zauna a gidan mahaifiyata tsawon rabin lokacin," in ji ta.

Evans, wadda ma'aikaciyar gwamnati ce a Cardiff, da abokiyar zamanta sun yi amfani da kuɗin da suka tara wajen biyan kuɗin farko na sayen gida a farkon wannan shekarar.

Wani bincike ya nuna cewa kashi 26 cikin 100 na matan Birtaniya ne kawai ke zuba jari, kuma adadin ya ragu zuwa kashi 23 a tsakanin matan da ba su kai shekara 45 ba.

A gefe guda kuma, kashi 41 na maza ne ke zuba jari, yayin da adadin ya kai kusan kashi 40 a tsakanin mazan da ba su kai shekara 45 ba.

To, me ya sa mata suka fi maza ƙauracewa harkar zuba jari?

A cewar Gillian Fleming, wadda ta kafa kamfanin Mint Ventures mai kula da harkokin zuba jari a Birtaniya kuma shugabar gudanarwarsa, bambancin ya samo asali ne musamman daga wasu ɗabi'u da aka saba da su.

Kamfanin nata na daga cikin kamfanonin zuba jari da mata ke gudanarwa.

Ta ce: "A tarihi, maza ne suka fi ɗaukar nauyin yanke shawarar zuba jari a cikin iyali, yayin da mata suka fi mallakar ƙaramin kaso na dukiyar iyali, amma wannan yanayi na sauyawa."

Ta ƙara da cewa: "Haka kuma, kuɗi da hanyoyin samar da dukiya ba batutuwa ba ne da mata suka saba tattaunawa a kai, kuma muna son sauya wannan yanayi."

Mata masu zuba jari

Tellery ta ce a baya-bayan nan ta fara lura da sauyi a wannan yanayi.

Ta ce: "Lallai zuba jari ya zama ɗaya daga cikin batutuwan da mata suka fi tattaunawa a kai, kuma hakan abin farin ciki ne. Haka abin yake a cikin ƙungiyar abokaina."

Idan mata suka zuba jari a kasuwar hannayen jari da sauran hanyoyin zuba jari, ana ganin sun fi maza samun ɗan ƙarin riba.

Wani bincike da kamfanin Fidelity International ya gudanar ya nuna cewa matan da suka zuba jari a kamfanin sun samu ribar kashi 50 cikin 100 a jimillar shekaru uku, idan aka kwatanta da kashi 47 cikin 100 da maza suka samu.

Binciken bai bayyana dalilin wannan bambanci ba, amma waɗanne abubuwa ne ka iya taimakawa wajen samun wannan ƙarin riba?

Wata alama da za ta iya bayyana dalilin da ya sa mata ke samun ɗan ƙarin riba a dogon lokaci ita ce yawan saye da sayar da jarin da suke yi.

Bayanan bankin Barclays sun nuna cewa mata na saye da sayar da jarinsu kusan rabin yawan lokutan da maza ke yi.

Joanna Floyd, wata masaniyar ilimin halayyar ɗan Adam a fannin kasuwanci a Cibiyar Masana Halayyar Ma'aikata da ke Landan, ta ce hakan na iya kasancewa saboda mata sun fi haƙuri kuma ba sa son shiga haɗarin da ba su da tabbas.

Ta ce: "Bincike ya nuna cewa masu zuba jari maza sun fi mata yawan saye da sayar da hannayen jari, kuma suna neman samun riba mafi yawa, amma a zahiri mata ne ke samun ribar da ta fi yawa."

A cewarta, "takatsantsan da ke hana mata shiga kasuwar zuba jari tun da farko, shi ne ke taimaka musu samun sakamako mai kyau da zarar sun shiga."

Ana kuma ganin irin wannan taka-tsantsan wajen fuskantar haɗarin kuɗi a sauran fannoni, inda mata suka fi zaɓar hanyar da ta fi aminci idan suka fuskanci yiwuwar yin asarar kuɗi.

Gillian Fleming ta ce mata kan yi taka-tsantsan da gangan idan ana batun zuba jari.

Ta ce: "A kan zargi mata da tsoron shiga haɗari, amma mu a wurinmu muna kallon hakan a matsayin fahimtar haɗarin da ke tattare da zuba jari."

"Abubuwan da muka tattauna da maza masu zuba jari sun nuna cewa abin da suka fi mayar da hankali a kai shi ne yawan ribar da za su samu."

Gillian Fleming ta kuma ce ana ganin mata sun fi maza rarraba jarinsu zuwa fannoni daban-daban.

Ta ce: "Maza sun fi karkata wajen zuba jari a kamfanonin fasaha saboda yiwuwar samun riba mai yawa. Amma mata sun fi neman zuba jari a fannoni daban-daban, tun daga kasuwancin sayar da kayayyaki, abinci da abubuwan sha, zuwa kiwon lafiya da ƙawata jiki, fasahohin da suka shafi mata da kuma masana'antun kirkire-kirkire."

Anna McDonald, daraktar dabarun zuba jari a kamfanin Hargreaves Lansdown mai ba da hidimomin hada-hadar kuɗi, ta amince cewa mata sun fi yin taka-tsantsan wajen zaɓen kamfanonin da suke son zuba wa jari.

Ta ce: "Ana ganin mata sun fi maza damuwa kan inda kuɗinsu zai shiga da kuma tasirin da hakan zai iya haifarwa. Haka kuma, suna son tabbatar da cewa jarin da za su zuba ya dace da su."

Gillian Fleming ta ce: "Bincikenmu ya nuna cewa maza sun fi sha'awar samun riba ta kuɗi, kuma galibi hakan ne ke sa su zuba jari domin samun riba mai yawa."

Gemma Slingo, masaniyar harkokin ritaya da zuba jari a kamfanin Fidelity International, ta ce ana ganin mata masu zuba jari sun fi danganta hakan da manufofin da suke son cimmawa a rayuwarsu, tun daga tara kuɗin da za su taimaka musu a lokacin da suka shiga matsin tattalin arziki, zuwa kula da 'ya'yansu.

Yana da muhimmanci a lura cewa, mata a Birtaniya gabaɗaya suna da ƙarancin kuɗin da za su iya zuba wa jari idan aka kwatanta da maza. Hakan ya samo asali ne daga ci gaba da samun bambanci tsakanin albashin maza da mata, inda mata ke samun ƙarancin albashi idan aka kwatanta da maza a matsakaici.

Anna McDonald ta ce masana'antar zuba jari na buƙatar "ƙara ƙoƙari wajen sauƙaƙa wa mutane shiga harkar zuba jari, tare da tabbatar da cewa harkar ta shafe su kuma ta dace da manufofinsu da ƙimomin da suke rayuwa a kai."

Ta ce: "Magance wannan matsala zai taimaka wajen ƙarfafa ƙarfin mata na fuskantar ƙalubalen kuɗi a dogon lokaci, tare da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar."