'Yadda nake rayuwa da al'aura biyu'

    • Marubuci, Asha Juma
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Nairobi
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ya za ka ji a ce kana rayuwa da wata lalurar da ko likitoci sai sun yi ta kame-kame kafin su iya yin bayanin abin da ke damunka - ko kuma rayuwarka ta dogara ne kan ƙoda guda ɗaya?

Wannan ce rayuwar da Abigael Kendi, ƴar shekaru 19 ke ciki a Kenya, inda aka haife ta dubura biyu, farji biyu, mafitsara biyu da kuma ƙoda guda ɗaya.

BBC ta samu damar tattaunawa ita da kuma ƙalubalen da ta ke fuskanta.

Abigael na fuskantar ƙalubale da dama tun daga 202 saboda yanayin al'aurar ta.

Yadda rayuwar Abigael ta kasance

Abigael ta girma kamar sauran yara mata, amma yanayin halittarta ta fara canzawa ne a lokacin da ta fara balaga.

"Na fara jin matsanancin zafi a duk lokacin da na ke jininn al'ada, kuma duk idan na faɗa wa mahaifiyata sai ta ce haka kowa ce mace take. Amma sannu a hankali sai na fara daina yin fitsari da bahaya kamar yadda na saba kuma ina amai. Na faɗa wa mahaifiyata amma ta yi tunanin wasa nake yi," in ji Abigael.

Wannan yanayin ya sa matashiyar ta fara jin ba daɗi, washe gari kuma ta fara jin wani yanayi a jikinta mara daɗi, inda daga nan aka kai ta asibiti.

"An fara da min gwajin juna biyu saboda yadda ciki na ya kumbura inda wasu suka yi tunanin ina da ciki ne," in ji Abigael.

Amma gwajin ya nuna cewa lafiya ƙalau take, inda likitoci suka buƙaci a yi wasu gwaje-gwajen na daban.

Yaushe iyayen Abigael suka gano wannan matsalar?

Abigael ta ce: "A lokacin da aka kwantar da ni a asibiti an ba ni wasu magunguna saboda yadda ciki na kumbura. Na je na yi hoton ciki inda suka gano cewa baya ga ƙoda guda ɗaya da nake da ita, ina da al'aura biyu."

Abigael ta ƙara da cewa ta san cewa rayuwa da ƙoda guda ɗaya ba wata matsala ba ce sboda mutane kan iya tallafa wa wasu da ita.

"Amma tawa kusan ruwa-ruwa take, kuma an faɗa min cewa in riƙa shan magani saboda kaucewa samun matsala. Na ji tsoro sosai saboda yadda rayuwa ta ke cikin haɗari, wasu lokutan ma sai in yi tunanin in haƙura kawai," in ji ta.

Wannan ne karon farko da iyayenta suka san cewa ƴarsu na fama da lalura.

Abigael ta na yawan tuna lokacin da mahaifiyarta ke kuka bayan da aka faɗa mata wannan bayanin.

'Ban taɓa yin jinin al'ada ba'

Abigael ta ce dalilin wannan lalurar ta fuskanci ƙalubale da dama.

"Ina jin zafi amma ba na iya yin jin al'ada kamar sauran mata. Ban taɓa yin jin al'ada ba. Amma a lokacin da aka ɗauki hoton ciki na, na ga wani abu kamar jini har ina cewa wataƙila zan fara al'ada."

"Ina jin tsananin zafi a lokuta da dama, alal misali, a wannan watan tsakanin 10 zuwa 15 ga wata da 20 zuwa 25 ga wata, amma kuma ba na iya ganin jin al'ada. Ban taɓa yin jin ba ko sanya audugar mata da kowace mace ke sanyawa," in ji Abigael

Wannan ya sa Abigael ke tunanin ba lafiya take ba. "Na fara zargin kaina, ina zargin jiki na, har sai da na rubuta littafi, inda nake magana a kan wannan abin."

'Ba na iya yin bahaya cikin sauƙi'

Abigael ta ce a wasu lokutan ta na jin jikinta na wani irin wari da ba ta saba yi ba.

Ta ce a duk lokacin da take jin wannan zafin da ke mata kama da na al'ada, mutane na faɗa mata cewa tana tafiya a kaikaice. Hakan na faruwa ne saboda nauyin da take ji a gefen marar ta.

A irin wannan yanayin ta kan so yin wasu abubuwa amma ba za ta iya ba.

"Ba na iya yin fitsari. A lokuta da dama sai dai in yi amfani da magani. Ko kuma in yi amfani da kororon mafitsara. Na kan sanya shi na tsawon kusan sati biyu. Sai dai bayan da suka ga ina yawan kamuwa da cututtuka, sai suka nuna min yadda zan riƙa saka shi da kaina. A duk lokacin da na ji ina son in yi fitsari, sai in je in yi kuma in jefar da kororon."

Wannan lalurar da Abigael ke fama da ita, ya sa tana shan wahala wajen yin fitsari da bahaya.

Abigael ta ce: "Abin ba sauƙi. Watakila saboda an taɓa min wankin ciki ne. Amma duk da haka ma ba na jin a jiki na ina so in yi bahaya, wani lokacin kawai ina zuwa banɗaki ne saboda na san na ci abinci kuma akwai buƙatar in yi bahaya."

'Wahalar da na sha a makaranta'

Abigael na amfani da wata na'ura da take taimaka mata wajen yin fitsari a lokacin da take makaranta.

A dalilin haka, an ba Abigael izinin amfani da wani banɗaki ita kaɗai, amma kuma ƴan ajinsu sun sa mata ido da son sanin me ya sa aka ba ta wannan damar.

"Ɗalibai da dama na yawan tambayar me ya sa ake ba ni kulawa ta musamman har da baɗaki na daban. Akwai wasu malaman ma da su ke ganin me ya sa ake min wannan kulawa. Wani ma har cewa yake yi ai ba a kaina aka fara yin tiyata ba, amma haka na jure har lokacin da ya bar makarantar," in ji Abigael.

Abin da ba ku sani ba shi ne Abigael na cikin damuwa a rayuwarta.

Ta ƙara da cewa: "Ina yawan fama da ciwon kai. Na yi gwaje-gwaje da dama inda suka ce ina da wani ruwa a cikin kaina. Amma suka ce ba za su iya wani abu ba saboda ina da lalurar a mara ta. Kuma za a ɗauki dogon lokaci kafin ƙoda ta, ta samu lafiya ko da an yi min tiyata," in ji Abigael.

Sau bakwai ana yi wa Abigael tiyata

Abigael ta ce tana ta faɗi tashin ganin ta samu lafiya a rayuwarta. Ta ce sau bawai ana yi mata tiyata domin ganin rayuwarta ta koma kamar sauran mata.

"Sau bakwai ana yi min tiyata domin ganin na yi rayuwa kamar kowace mace, kuma in riƙa ganin jinin al'ada amma har yanzu abin ya ci tura," in ji ta.

Ta ce zuwa yanzu har ta gaji da yin magani.

"An yi min tiyata. Wasu lokutan ina jin kamar ina wahalar da iyaye na saboda suna ta kashe kuɗinsu a kaina, sun sayar da abubuwa da dama saboda ni, kuma ko da sun sayar ɗin, ba wani sabon abu da ake gani. Na gaji. Akwai lokacin da ma na gwammace in mutu"

"Sai dai suna yawan ba ni ƙwarin gwiwa, kuma na ga sun damu da ni suna buƙata ta, shi ya sa nake ganin wataƙila in samu kyakkyawar makoma," in ji Abigael.

'Ba kowa ke fahimta ba'

Ba kowa ne zai fahimci halin da mutum ya ke ciki ba, musamman idan kana fuskantar ƙalubale a rayuwa. Abigael ta ce akwai abin da kowa ke kallon lamarin.

"Ba kowa muke yi wa bayanin cewa ina da al'aura biyu ba. Ba su fahimtar mu, suna ganin kamar ba ni da lafiya ne kawai amma ba su san wahalar da nake sha ba."

"Wasu ma suna ganin asiri ne ko kuma akwai abin da kakata ta ɓoye ba ta faɗa mana ba. Wasu na cewa mu je wajen malamai a mana addu'a, wasu kuma su ce ana sauya min tunani ne," in ji Abigael.

Matashiyar ta ce dole ta sa take yin bayanin halin da take ciki, saboda iyayenta sun yi iya bakin ƙoƙarinsu amma sun kasa samun maganin matsalar.

Abigael ta yi kira ga waɗanda ke fama da wasu lalurori na rashin lafiya a ɓoye da su daina jin tsoro su yi bayani saboda su samu taimako.

Yanzu dai Abigael na samun kulawa a babban asibitin Kenyatta na ƙasar Kenya, kuma hakan na bata ƙwarin gwiwa cewa wata rana mafarkinta zai tabbata.